001-234-567-8910

5th Avenue Madson, NY758, USA

Get Update on our recent Gadgets & Tabs

Add this

Add this

Web Design Agency Nigeria https://www.ads54.com/ad/a/10595_4daf76b52369930

Add this

Website Value Calculator - Domain Worth Estimator - Buy Website For Sales

Add This

Amfnin flash memori (Flash Memory)

Duniyar computer (digital era) part 16

Amfnin flash memori (Flash Memory)

Shi flash memori kuma ana amfani da shine a jona a jikin Komfiuta don a tura wasu bayanai daga cikin Komfiuta zuwa cikinsa don a ajiye koda watarana za'a nemi wadannan bayanan ko kuma ana amfani dashi don a kofi wani abu daga cikin wata Komfiuta zuwa wata itama tana da amfani matuka saidai kuma tana iya daukan cutan Komfiuta daga Komfiuta mara lafiya zuwa mai lafiya kuma duk lokacinta kwayar cutan bairos ya shiga cikin flash yana iya bata abubuwanda yake ciki.

Sannan kuma shi Flash Memory yana baciwa idan har ba'a bin ka'idar amfani da ita misali idan aka sakata a jikin Komfiuta aka tura wasu abubuwa ko kuma aka kofa daga cikinta ba'a yarda a cireta daga jikin Komfiutaba har sai Komfiuta ta bada daman cirewa yadda Komfiuta zata bada daman cirewan kuma shine kamar j:-

Zaka je kan Task bar (sandan ayyuka) 

Sannan sai ka dannan wannan alamar 

Sai ya nuna maka haka 

Daga nan sai ka dannan

Ko kuma zai nuna maka sunayen ma'aiyoyi masu yawa sai ka dannan wanda kake so daga ciki sai ya fitar daga jikin komfiutar sannan sai ka zare kayanka.Ko kuma ga hanya ta biyu kamar haka:Shi kuma zaka tafi mai Komfiuta (My Computer) sai kaje kan ma'jiyar da kake so ka zare sai ka danna maballin gefen daman (Rigth Click) a dan bera sai ya nuna maka wani Allon bada zabi sai ka danna fitarwa (Eject) sai ya fitar maka amma shi wannan hotonda kuke gani a sama na Komfuitar Larabcine saidai babu bambanci da na Turanci duka saidai yare kawai sannan kuma na daukone a Windowss Xp.Fadakkarwa

Akwai lokacinda zaki bi wadannan hanyoyin duka amma kuma Komfiuta taki bada dama a cire ma'ajiyar da take jikinta to a wannan yanayin dole a kashe Komfiuta ta hanyar dannan maballin kashewa kai tsaye saboda a cire wannan ma'ajiyar inba haka ba za'a iya samun matsalar lalacewar ma'ajiya matukar Komfiuta bata bada dammar cirewaba abinda yake kawo rashin amincewar Komfiuta a cire ma'ajiya a jikinta kuma shine samuwar bairos a cikin ma'ajiyar ko kuma a jikin Komfiuta kokuma rashin yin saurin Komfiuta ta yadda bazai bada umrani da wuri a cireba.Sannan itama ma'ajiyar Flash Memori tanada girma gorgodon kudinta da tsadanta domin ana samun mai Gig um m----------har zuwa 256 sabanin ma'ajiyar Floppy Disk wanda baya wuce mega byte uku kachal.
A karshe kuma akwai hanyar da mutum zai dauki bayanai a cikin Komfiuta.

ko ya tura zuwa cikin Komfiuta ta hanyar yin amfani da memorin wayar Salula amma ita wannan hi.


#Bintubetv  #Duniyarcomputer #fasaharzamani 

[Computer] Yaya ake amfani da External CD-ROM.

Duniyar computer (digital wold) part.15

Na uku itace ma'ajiyar Blu-Ray:-

Ita wannan ma'jiyar tafi kowace ma'ajiya daga cikin ma'ajiyoyi guda ukunda muka fada a sama daukan kayaki mai yawa da karfi da inganci da kuma sauri da dadewa amma saidai ba akasaifai ake samuntaba saboda itace sabuwar fita wato na zamani don haka ba a ko ina ake samuntaba sannan kuma tana da tsada haka kuma bata kunnuwa a cikin Komfiutocin da sai na yayi kamar yadda ma'ajiyar DVD bata kunnuwa a cikin wasu Komfiutocin don haka mai karatu bazai iya mu'amala da wannan ma'ajiyarba har sai ya shirya amma da za'a samu wannan majiyar da tafi kowane daga cikin ukun da yafi saboda ita wannan ma'jiyar tana iya daukan kayanda nauyinsu yakai gig dari (100) don haka zai taimaka wajen ajiya matuka indai ana da daman samu.

To wadannan sune abinda ake nufi da ma'ajiya Curarriya kamar yadda muka sa mata suna da hausa wanda kuma ake kira da suna CD-ROM da DVD-ROM da Blu-Ray da ire-irensu kamar yadda kuka kalli hotunansu a sama da kuma amfaninsu don haka anan zamu dakata don mu wuce wani bangaren daban.Fadakarwa

Mai karatu ka san cewa idan Komfiuta bata da makunnin DVD to babu yadda za ayi kayi amfani da ma'jiyar DVD haka kuma idan Komfiuta bata da makunnin Blu-Ray ba yadda za'ayi kayi amfani da ma'ajiyar Blu-Ray haka kuma koda Komfiuta tana da ma'jiyar DVD ko Blu-ray to ba yadda za'ayi ka iya kofan bayanai daga cikin Komfiuta ka daura akan ma'ajiyoyinnan guda uku har sai makunnin naka ya kasance yana iya karantawa sannan kuma ya rubuta saboda a ilimin Komfiuta akwai abinda ake cewa karantawa da kuma rubutawa to dole sai Komfiuta ta kasance tana iya yin biyun duka kafin ka ajiye kayanka a wadannan ma'ajiyoyin in kuma Komfiuta bata dashi sai ka samu makunnin waje wato External-Drive kenan a turance wanda aka fi sani da suna External CD/DVD ROM don tayi maka wannan aiki ita kuma ana jonatane a jikin Komfiuta sai a saka ma'ajiyar a ciki ga hotonta kamar haka:-                         External CD-ROM

#Fasaharzamani #Bintubetv #Duniyarcomputer

[Computer] Amfanin ma'ajiya curarriya (CD ROM & DVD ROM).


Duniyar computer (digital wold) part. 15

Amfanin ma'ajiya curarriya

Ita ma'ajiya Curarriya ta kasu kashi uku:-
CD ROM.

DVD ROM. 

Blu-Ray.

Na farko ita ma'ajiyar ajiya ta CD-ROM  ko CD-R itama ta kasu kashi biyu:-

1-Akwai CD-R.

2-Akwai CD-RW.

Bambancinda yake tsakanin wadannan nau'ukan guda biyu kuma shine shi CD-R zaka tsaye shine babu koma a cikinsa sai ka tura dukkan abubuwanda kakeso daga Komfiuta zuwa gareshi don ka ajiye zuwa watarana idan na Komfiutarka ta samu matsala sai ka dauko na CD-R dinka ka saka mata ko kuma zaka kofi wani abu daka Komfiutarka don ka baiwa wani da sauransu amma bayan an saka mata abu ba'a iya gogeta ko a kara da zaran ka gama ka cireta a Komfiuta shikenan ba yadda za'ayi a sake saka mata wani abu ko a goge abinda ke cikinta.

Na biyu wato CD-RW shi ana iya saka mata abu sannan kuma ana iya goge abinda yake cikinta don a saka wani wannan shine bambancinda yake tsakaninsu to amma kudinsu dabanne saboda amfaninsu ya bambanta shi na biyun yafi tsada.

Sannan kuma ita ma'ajiyar CD-ROM ko CD-R iri biyu duka suna iya daukan kaya wanda yawansu zai kai mega byte700 wato kusan Gig daya kenan.

Haka kuma ita ma'ajiyar DVD-ROM itama ta kasu kashi biyar:-

1- DVD-R

 2- DVD+R

3- DVD-WR

4- DVD+WR

5- DVD RAM

Bambancinda ke tsakaninsu kuma sune kamar haka:-

Shi Ma'jiyar DVD-ROM ko DVD-R ana iya sayansa haka babu komai a cikinsa don a zuba masa bayanai daga cikin Komfiuta a ajiye ko a saka a wata Komfiuta amma da zaran an saka mata abu ba'a iya gogeta ko a kara wata ana amfani da itane ta wajen tura abu sau daya kawai.


Itama ma'jiyar DVD+R haka take kamar na farkon amma bambancinsu shine shi wannan ma'ajiyar ta DVD+R tafi ta DVD-R kyau da inganci ta wajen tura abu ko kofan abu.
Sannan kuma ita ma'ajiyar DVD-RW ita tana iya daukan abu ta ajiye haka kuma ana iya goge abinda yake cikinta don a sake saka wani kamar yadda ake wa memori.
Haka itama m'ajiyar DVD+RW itam aikinta daya da na DVD-RW amma saidai wannan tafi ta saman sauri da kuma wasu 'yan bambance-bambance ammadai bambancin bashi da wani muhimmanci mai yawa.


Na akrshe daga cikin nau'ukan ma'jiyar DVD shine DVD-RAM shi kuma yafi kowanne daga cikin ma'ajiyoyin DVD inganci saboda shi yana da sauri sosai sannan kuma aikinsa ya sha bamban da sauran nau'ukan sannan kuma

ana iya saka masa abubuwa sannan a goge har sau 100,000 dubu dari sabanin sauran DVD wanda in aka gegesu sau 1000 dubu ko sama da haka kadan shikenan zasu daina aiki amma kuma shi wannan na karshen yafi kowanne tsada da kuma wahalan samu.To amma mai karatu ya san cewa dukkannin nau'ukan ma'ajiyar DVD guda biyar da muka fada suna da kayu ta wajen ajiye abu saboda suna iya ajiye maka abinda yake cikinsu tsawon shekara talatin 30 ba tareda sun samu matsalaba haka kuma suna iya ajiye maka kaya wajen kusan gig biyar akwaima wanda yake iya daukan gig takos ko tara sannan kuma cutan bairos baya iya yi musu komai balle ya bata maka abinda yake ciki.
Fadakarwa

Saidai kuma su ma'ajiyoyin CD ko DVD basa son a taba fuskarsu da abu mai kaushi ko a ajiyesu a inda ruwa zai taba ko zafi mara misali ko goguwa da juna don haka indai kana so kayanda ka ajiye a ciki ya dade har tsawon wannan shekarun dole sai ka bi wadannan ka'idojin da kamfani ya fada.

#Duniyarcomputer #Fasaharzamani #Bintubetv.

[Computer] Ma'ajiyar Flash حيضييىنا جشكازنا Flash Memory.


Duniyar computer (digital wold) part. 14

Ma'ajiya ta biyu

Ma'ajiya ta biyu kuma sune ma'ajiyoyin Komfiuta wadanda ake iya sakawa a jikin Komfiuta ko kuma a cire sannan ana iya goge abubuwanda yake cikinsu in anga daman hakan su kuma sune kamar haka:-Hausa Larabci Turanci:


Ma'ajiya mai karfi حثهصنا نيزختنا جذحو      Hard Dick


Ma'ajiya mara karfi حنشًنا نيزختنا جذحو    Floppy Disk.


Ma'ajiya Curarriya حديذًنا نيزختنا جذحو       CD ROM.

Ma'ajiyar Flash حيضييىنا جشكازنا      Flash MemoryTo wadannan sune abubuwanda ake kira da suna ma'ajiya ta biyu kamar yadda kuka ga hotunansu a sama yanzu kuma sai muji yadda ake amfani dasu kamar haka:-Amfanin ma'ajiya mai karfi

Ita ma'ajiya mai karfi itace babban abinda Komfiuta take dogaro dashi wajen ajiye dukkan abubuwanda aka saka a cikin Komfiuta gorgodon girmanta gorgodon yadda Komfiuta zata dauki abubuwa masu yawa saidai kuma a sani cewa koda wannan ma'ajiyar tana da girma indai RAM bata da girma to akwai abubuwanda baza a iya sakasu a cikin Komfiutaba kamar wasu daga cikin Softwere amma indai ajiyane kake so kayi a cikin Komfiuta kamar ajiyan karatuttuka da wa'azi da kayan kallo da sauran bayanai masu amfani to dole ka bukaci wannan ma'ajiyar tayi girma.


Haka kuma girman wannan ma'ajiyar tana farawane daga GB (giga byte) 8-

har zuwa GB dubu biyu ana samun Komfiuta mai gig 8,20,40,80,120,160,250,320,500,640,750,1000,2000 wato Terabyte biyu kenan a ma'aunin ma'ajiyar Komfiuta.

Amma a sani cewa duk lokacinda girman wannan ma'ajiyar tayi yawa

dole kudin Komfiutama ta karu amma kuma ana iya cire wannan ma'ajiyar a saka wata wanda ta fita girma in aka bukaci hakan kamar yadda ake yi wa wayar hannu.
Amfanin ma'ajiya mara karfi wato (Floppy Disk)


Ita ma'ajiya mara karfi ana amfani da itane a da lokacinda ba' samu ci gaba kamar na yanzuba kuma ita amfi amfani da itane a Komfiutocin kan tebur da kuma wasu daga cikin Komfiutar tafi da gidanka kiran da amma yanzu an maye gurbinta da CD ko DVD ko Flash Memory ko Blu-ray saboda su wadannan ma'ajiyoyin suna dauka abubuwa masu yawa amma ma'ajiya mara karfi bata wuce wasu mega byte (Mega byte) 'yan kadan.#Fasaharzamani #Bintubetv #Duniyarcomputer.

[Computer] Bambanci tsakanin ma'ajiyar ROM da RAM.


Duniyar computer (digital wold) part. 14

To anan zan dakata game da abinda ya shafi na'urorin fitarwa sai mu wuce gaba domin jin bayani gameda na'urorin ajiya wato (storage devices) kamar haka:-
Na uku na'urorin ajiya

Abinda ake nufi da na'urorin ajiya kuma sune dukkan abubuwanda ake amfani a dasu don a ajiye bayanai ko murya ko kayan kallo da sauransu a cikin Komfiuta wadannan ma'ajiyan kuma akwai wadanda suke zuwa tare da Komfiuta akwai kuma wadanda ake jonawa a jikin Komfiuta daga baya gasu kamar haka:-

Wadannan ma'ajiyan kuma sun kasu kashi biyu:-


Hausa
larabci
Turanci

1.
Akwai ma'ajiyar ainihi.
حيسيئشنا جشكازنا
main memory

2.
Akwai ma'ajiya ta biyu.
حيىناثنا جشكازنا
Secondary memoryMa'ajiya na ainihi sune kamar haka:-

Hausa larabci turanci:


Ma'ajiyar dindindin.   حًئاذنا نيزختنا جذحو Rom


Ma'ajiyar lokaci kadan حيئاىشعنا نيزختنا جذحو Ram
To wadannan sune ake kira da suna ma'ajiyar ainihi abinda yasa ake kiransu da suna ma'ajiyar ainihi kuma shine su wadannan ma'ajiya guda biyu in babu su ba yadda za'ayi Komfiuta tayi aiki ko ta kunnu domin ita ROM a cikintane aka ajiye dukkan abubuwanda suke kunna Komfiuta wanda kuma kamfaninda ta kera Komfiuta ita take sakawa don haka ba yadda za'ayi ka goge wani abu a cikinta ko ka kara sannan kuma ita ba'a canzata.


Amma ita ma'ajiyar RAM ana iya canzata a saka babba ko karami ko a kara wata akan na ciki.

Bambanci tsakanin ma'ajiyar ROM da RAM


Ita ma'ajiyar ROM abubuwanda yake cikinta baya goguwa koda an kashe Komfiuta ko ta dauke sannan kuma tana amfanine da abinda kamfani ya saka mata don ta kunna Komfiuta ta fara aiki amma ita ma'ajiyar RAM abubuwanda suke cikinta suna goguwa da zaran an kashe Komfiuta ko ta dauke don hakanema ake kirantan da suna ma'ajiyar lokaci kadan sannan kuma ita RAM ita take saka Komfiuta yin sauri don haka gorgodon yadda ma'ajiyar RAM take da girma gorgodon yadda Komfiuta zata yi sauri ta wajen kunnuwa ko yin kowane aiki.

Fadakarwa

Saidai kuma akwai abinda ake cewa froseso (Processor) inhar wannan froseso bashi da sauri ko girma to koda ma'ajiyar RAM tana da girma to Komfiuta baza ta dinga yin aiki da sauri kamar yadda ake soba don haka koda ma'ajiyar RAM tayi girma to dole froseso ma yayi girma kafin Komfiuta tayi saurinda ake bukata.


#Bintubetv #Duniyarcomputer #Fasaharzamani

[Computer] Na biyu Na'urorin fitarwa (output devices).

Duniyar computer (digital wold) part. 13

Na biyu Na'urorin fitarwa

Su kuma na'urorin fitarwa kamar yadda muka fada a baya sune abubuwanda ake fitar da bayananda aka saka cikin Komfiuta ta hanyarsu su kuma sune kamar haka:-1. Allon talbijin   حشاشنا Monitor.2. Lasifika   خىصنا خاشثكي   loud-speaker.3. Mabugar takardu حعتاطنا      Printer.To wadannan sune na'urorin fitarwa da hotunansu wadanda ake amfani dasu wajen fitar da bayanai daga cikin Komfiuta yanzu kuma sai mu ji

yadda ake amfani dasu kamar haka:-
Amfanin allon talbijin.

Shi Allon talbijin wato (Monitor) da shine ake amfani don kallon dukkan abubuwanda aka shigar cikin Komfiuta ko kuma ake shigarwa ita amfaninta da tibi kusan dayane saboda ana iya kallon tibi ma da shi akwai maballai na rage murya da karawa a jikinsa da kuma yadda za'a rage launi ko a kara da kara haske ko duhu amma shi wannan Allon talbijindin yana da nau'uka biyu .


1-Akwai Allon talbijin mai suna CRT


2-  Akwai kuma Allon talbijin mai suna LCD
Bambancinda yake tsakanin wadannan nau'ukan kuma shine shi Allon talbijin na na CRT ya zama tsohon yayi saboda shi ana amfani da shine a da sannan kuma shi yana cin waje dayawa ga kuma nauyi ga kuma jan wuta sosai don yana iya cin watt 160 na wuta sannan kuma baya amfani da wutan DC sai AC wato in babu wutan lantarki bazai iya kunnuwaba sannan kuma shi yana daukan zafi kuma sannan bashi da kyan hoto sosai da sauransu.
Amma shi Allon talbijin na LCD yana  da kyan nuna  hoto gashi kuma baya daukan zafi sosai kuma yana iya kunnuwa da DC wato wutan batir sannan kuma baya cin waje sosai haka kuma baya jan wuta sosai domin duk jan wutansa baya wuce watta 40 na wuta sannan kuma yana da amfani dayawa sabanin CRT saidai kuma wannan Allon na LCD yafi na CRT tsada sosai.
Amma ta wajen amfani dukkansu biyu ana iya kallon tibi ko dish dasu sannan kuma ana iya hadasu da Komfiutar tafi da gidanka domin ayi amfani dasu a matsayin Allon Komfiutar tafi da gidanka to wannan shine abinda zan iya fada gameda Allon talbijin na CRT da kuma LCD.
Amfanin lasifika

Lasifika kuma amfaninta a jikin Komfiuta itace fitar da murya saboda yawancin Komfitocin da ake amfani dasu a da babu sifika a jikinsu don haka duk lokacinda mai amfani da Komfiuta yake so ya saurari karatun Alkur'ani ko ya ji wa'azi ko yayi kallo a cikin Komfiuta dole sai ya bukaci Lasifika don yaji murya.

Haka kuma ana amfani da Lasifika wajen kara murya ko ragewa saboda wasu daga cikin Komfitoci basu da murya sosai musammanma kamar Komfiutar tafi da gidanka wanda ake kira da suna NoteBook saboda ita bata da murya sosai domin tana amfanine da batir sannan kuma sifikunsa kananane sosai don haka in mai amfani dashi ya bukaci jin karatu ko kallo to dole zai ya bukaci Lasifika ya jona mata.Amfanin mabugar takardu

Ita kuma mabugar takardu wato (Printer) ana amfani da itane ta wajen fitarda dukkan abubuwanda aka rubuta a cikin Komfiuta ko aka zana ko kuma wani abinda aka samo daga kan yanar gizo-gizo ko kuma wani sakonda aka aikowa mutum a hanyar E-Mail da sauran abubuwanda ake so a fitar dashi a rubuce ko a zane saidai kuma ana saka fallen takarda a cikin mabugar takardu kafin ta cire rubutacciyar takardan sannan kuma wani nau'in mabugar takardun ana zuba mata tawadanta wato Ink na baki-da-fari ko kuma mai launi wani mabugar takardan.

kuma tana amfanine da gari wanda ake saka mata.

Sannan kuma wata tana iya buga takarda ta cire sannan kuma ta iya yin foto-kofi sannan kuma tana iya daukan hoto ko rubutaccen takarda don ta gyara

sannan ta sake cirewa.


Saidai kuma ita mabugar takardu ta kasu kashi biyu:-

Akwai mai baki-da-fari

Akwai mai launi.

Haka kuma suna da farshi daban-daban wanda ya danganci karfinsu da kyansu da kuma saurinda suke dashi da kuma ayyukanda suke yi da sauran bambance-bambancensu.

#Bintubetv #Duniyarcomputer #fasaharzamani

[Computer] Amfanin karan wasa, (pen/finger), modem, camera.
Duniyar computer (digital wold) part. 12

Amfanin karan wasa

Ita karan wasa ana amfani da itane a lokacinda mai amfani da Komfiuta yake so yayi was na shaya rai a cikin Komfiuta sai ya dauko wannan karan wasan ya saka sai yayi amfani dashi ta wajen yin wasa saboda ita Komfiuta tana da wasanni iri
daban-daban a cikinta wanda idan mai amfani da Komfiuta yaso yayi wasa sai ya budesu a cikin Komfiuta haka kuma mutum zai iya kara wasu wasannin daban

wadanda babu a cikin Komfiutarsa in yaga dama.


Amfanin web kemara

Ita kemaran web ana amfani da itane a yayinda mai amfani da Komfiuta yake so yayi hira da wani ta yanar gizo-gizo (internet) ko kuma yake so ya dauki hotonsa ya saka a cikin Komfiuta ko ya daura akan yanar gizo-gizo sai ya kawo kemaran web ya daura a kan Allon Komfiutarsa ko kuma ya ajiye a gefe sai yayi amfani da ita in kuma Komfiutar tafi da gidankane to yana da nasa kemaran a fuskar marfin Komfiutar sannan kuma ana iya makala mata wata daban a jikinta ko a gefe.

Amfranin makirufo

Shi kuma Makirufo ana amfani da shine a yayinda mai amfani da Komfiuta yake so ya dauki muryarsa ya sakata a cikin Komfiuta ko kuma yake so ya yi rekodin din wani abu da sauran abubuwanda ake so a shigar cikin Komfiuta indai

muryace to ana amfanida Makirufo don yinta.


Amfanin modem

Modem ana amfani da shine a yayinda ake so a hada Komfiuta da yanar gizo-gizo wato Internet don a samo bayanai ko kuma a aika bayanai zuwa kan Internet wanda inhar mai Komfiuta bashi da modem bazai iya shiga yanar gizo-gizoba saidai yayi amfanida wasu abubuwanda suke zama a maimakon modem.


Amfanin madaukin hoto

Shima madaukin hoto ana amfani dashine idan ana so a saka wani hoto ko zane ko bugeggen rubutu zuwa cikin Komfiuta saboda ita wannan na'urar tana daukan surar abu yadda take ta saka a cikin Komfiuta sannan kuma in anga dama sai asake gyarar wannan hoton ko rubutun ta yadda za'a canza masa tsari ko a sake cireta kamar yadda aka sakata ta hanyar mabugin takarda wato (Printer).

To wadannan sune na'urorin shigarwa da kuma amfninsu a jikin Komfiuta yanzu kuma sai mu wuce gaba muga bangare na biyu wato na'urorin fitarwa da kuma

yadda ake amfani dasu da kuma amfaninsu a jikin Komfiuta.


#Bintubetv #Duniyarcomputer #Fasaharzamani

[COMPUTER] AMFANIN DAN BERA (MOUSE).


Duniyar computer (digital wold) part. 11

AMFANIN DAN BERA

Shi kuma dan bera ana amfani da shine kamar yadda ake amfani da yatsa ma'ana shi kamar wata yatsace mai aiki da wutan lantarki da shine ake amfani wajen nuna abu acikin Komfiuta ko kuma jan abu ko kuma amincewa da wani abu ko ki a cikin Komfiuta.

Shi kuma dan bera yana da maballai guda biyu daya a hagu daya kuma a dama kuma a yawancin lokaci amfi yin amfani da maballin gefen hagu indai a babban Komfiutace amma indai a karamin Komfiutar tafi da gidan kane amfi yin amfani da maballi gefen dama saboda a Komfiutar tafi da gidanka ana amfani da tsakiyar Touch Pad wato waje mai tsantsinnan na kusada madannani domin ya yi maka aikinda maballin gefen hagu yakeyi amma a babban Komfiuta kuma babu wajen saidai ka dinga jan dan bera akan wani abu ko cinyarka.Don haka duk lokacinda akace ka dannan dan bera a babban Komfiuta to amfi danna na gefen hagu in kuma na gefen dama ake so ka danna sai ace maka ka danna na dama sabanin karamar Komfiuta.Kuma ana amfani da maballin gefen hagu don nuna abu a cikin Allon talbijin na Komfiuta saboda akwai wata kibiya wanda ake kira da suna Kuso (Cursor) wanda da ita ake nuna abu a jikin Allon talbijin din Komfiuta duk lokacinda ka taba dan bera itama zata dinga motsi don haka da ita ake nuna abu haka kuma ana amfanida maballin gefen hagu don jan wani abu kamar hoto ko rubutu sannan kuma da ita ake amfani wajen zaban abu da sauransu amma shi maballin gefen dama ana amfani da shine ta wajen neman karin bayani idan aka tsaya a gaban abinda ake so a nemi Karin bayani a game dashi aka danna ko kuma ana amfani dashine idan ana so a ofantar da wani abu ma'ana rashin amincewa ko yarda da wani abu.
#Bintubetv #fasaharzamani #Duniyarcomputer

[Computer] Amfani madannai (Keyboards).


Duniyarcomputer (digital world) part 10

Amfani madannai (Keyboard)

Madannai yanada amfani sosai a jikin Komfiuta saboda dashine mai amfani da Komfiuta zai shigar da bayanai cikin Komfiuta kamar rubutu saboda madannai yana daukeda haruffa daga A,B,C, har zuwa Z, wanda da sune mai amfani da Komfiuta zai shigar da dukkan abinda yake so ya rubuta a Komfiutarsa sannan kuma madannai yana daukeda lambobi daga 1, har zuwa 9, da 0 wadanda mai rubutu ko lissafi zai yi amfani dasu idan ya bukaci hakan hakannan kuma madannai yana da wasu alamomin tsara rubutu kamar alamar tambaya da alamar motsin-rai da karan dauri da karan-tsaye da aya da waqafi da alamar hadawa da rabawa da ragewa da bugawa da sauransu kamar yadda muke gani a jikin

kakuleto (Calculator).
Haka kuma madannai yana da wasu maballai wadanda ake amfani dasu ta wajen yin aiki na musamman kamar bawa Komfiuta umarni wadannan maballan kuma ana kiransu da suna (Function Keys) su kuma guda goma sha biyune suna farawa da F1-F12.Sannan kuma muna da wasu maballai a jikin madannai kamar maballin Ctrl da Alt da Delete da Back space da Shift da sauransu wanda zamuyi Maganaakansu in muga zo yin bayani akan amfanin madannai a manhajar rubutu wato Microsoft word in sha Allahu.

Wannan atakaice Kenan da yarda Allah zamu zo muko da cikekken bayanai gameda keyboards din nan.


#Bintubetv #Duniyarcomputer #fasaharzamani

Qwaqwalwar Computer. K. حيزكشًنا حدناعًنا جذحو. CPU


Duniyar computer (digital world) part 10

Sanin PC. Computer

Menene PC Computer (Na'ura mai kwakwalwa ta mutum daya)?

Na'ura mai kwakwalwa wato Komfiuta itace: wata na'ura da take amfani da wutan lantarki' wacce take karbar bayanan da aka shigar mata ta hanyar na'uran shigarwa ta ajiye, sannan kuma ta fitar da bayanan a duk lokacinda aka bukata ta hanyar sarrafawar mai amfani da ita da taimakon na'urar fitarwa.

Abinda ake nufi da na'urar shigarwa sune dukkan abubuwanda ake amfani dasu wajen shigar da bayanai cikin Komfiuta su kuma sun kasu kashi hudu kamar haka:-
Hausa
Larabci
Turanci

1- Na'urar shigarwa. لاخدلإا جزهخأ. Input devices.

2- Na'urar fitarwa. جاشخلإا جزهخأ. Output devices.

3- Na'urar ajiya. نيزختنا جزهخأ. Storage devices.

4- Kwakwalwa K. حيزكشًنا حدناعًنا جذحو. CPU.


Na farko na'urar shigarwa

To na'urar shigarwa kuma sune kamar haka:-


Cikin yaren, Hausa, Larabci, Turanci.

1. Madannai
حيتافًنا ححىن
Keyboard

2. Dan bera
جسأفنا
mouse

3. Karan wasa
ةعهنا اصع
Joy stick

4. Kemaran Web
ةيو جساىصّ   Web Cam.

5. Makirufo
خىصنا طللا
Microphone

6. Modem
فشاكنا/ ىيدىي
Modem

7. Madaukin hoto
يئىضنا حساًنا
Scanner
To a takaice wadannan su ake kira da suna na'urorin shigarwa wadanda ake amfani dasu domin shigarda bayanai cikin Komfiuta kamar yadda mai karatu ya kalli hotunansu a sama da kuma sunayensu a harcen Hausa da Larabci da kuma Turanci yanzu kuma sai mu dan yi bayanai akan kowanne daga cikinsu a takaice.

#Bintubetv #Fasaharzamani #Duniyarcomputer.

Yaren Komfiuta. حديشثنا حغن Programming Language.


Duniyar computer (digital world) part. 9

1- Microsoft Office.

2- Corel Draw

3- Anti Virus.


Na farko shi Microsoft Office a cikinsane ake samun Word wanda ake amfani dashi don yin rubutu a cikin Komfiuta domin in babu shi ba yadda za'ayi kayi rubutu mai tsari a cikin Komfiuta har ka buga a takarda.

Na biyu shi Corel Draw kuma da shine ake amfani don ayi dukkan wani zanen abubuwa ko kuma canza musu tsari da sauransu in babu shi a cikin Komfiuta ba yadda za ayi kayi zane mai kyau har ka buga shi a takarda.

Na uku shi kuma Anti Virus da shine ake amfani don a cire dukkan wata cutar da take cikin Komfiuta domin akwai abinda ake ce mata bairos wanda in ta shiga jikin Komfiuta sai ta bata dukkan abinda yake cikin Komfiuta ko kuma ta hana Komfiuta yin aiki yadda ta dace ko kuma ta zama bata da sauri da makamantansu don haka sai a saka mata Anti Virus don ta kama wannan cutan ta cire.

3.Yaren Komfiuta. حديشثنا حغن       Programming Lan.

Na uku wato Programing Language yaren Komfiuta wato ita Komfiuta tana amfani da wani yare na musamman wanda kamfanin kera komfiuta suka hadata ko kumja wasu mutaneda suke kirkiran manhajoji suka hadata ta yadda suke yin amfani da wasu haruffa da lambobi insuka hada suka ajiye a cikin Komfiuta shikenan ita Komfiuta ta san me ake nufi da wannan abin don haka sai tayi aikinda aka sakata babu wanda yake fahimtar wannan yaren a duniya sai Komfiuta ita kadai.


Itama yaren Komfiuta ya kasu kashi dayawa amma ga kadan daga cikinsu kamar haka:-

1- C++

2- Besic

3- Pascal

4- Python

5- Ruby

6- XLm

7- Java

8- PHP

9-  9-XLM

10-HTML.


To atakaice wadanna sune yarenda Komfiuta ko wata manhaja ta musamman suke aiki dasu a yayinda suke yin aiki.Fadakarwa

Abinda ake nufi da Operating System shine wata manhaja wanda kamfanin Komfiuta ta tsara shi don ya baiwa Komfita umarni ta kunnan kanta ko ta kashe ko tayi wani aiki na musamman in har babu wannan manhajar ta OS to ba yadda za ayi Komfiuta ta kunnu kamar yadda muke da manhaja ta Andriod ko Syimbian a wayoyin hannu amma saidai ita wannan manhajar tana da ire-iren masu yawa amma yanzu yawanci amfi amfani da Windows 7 ko kuma Windows Xp da Windows Vista da Windows 8 amma duk Windows 7 yafi rinjayansu saidai kuma wadanda suke da karamin ma'ajiyar Komfiuta sunfi amfani da Windows Xp to a takaicede wannan shine Windows shine mabudin Komfiuta da kuma mai baiwa Komfiuta dukkan umarni sannan ya isar da mai amfani da Komfiuta zuwa ga manufarsa .

Abinda ake nufi da( Anti Virus) wata gagara ganine wato Software wanda take kashewa ko ta kama kwayar cutan Virus(bairos) wanda kamfani yake kirkiranta sai ya watsata a iska ko kuma akan Internet (yanar gizo-gizo) idan mutum ya shiga intanet da Komfiutarsa shikenan sai ya dauki wannan cutan ko kuma in mutum ya saka memerinsa ko Flash Memori a cikin Komfiuta mai cuta shekenan sai ta dauki wannan cutan kamfani suna yin hakanne don su samu hanyar da zasu dinga sayarda Anti Virus wato maganin kashe cutan Komfiuta sannan kuma shi bairos in ya shiga Komfiutarka sai ya bata maka dukkan abinda yake cikin Komfiutar ko wani sashi ko kuma ya hana Komfiuta yin aiki daidai ko kuma ya hana ta yin sauri da sauransu har sai ka saka Anti bairos mai karfi ya kashesu.

#Bintubetv #Duniyarcomputer #Fasaharzamani 

MANHAJOJIN COMPUTER (APPLICATIONS)


Duniyar computer (digital world) part 8

Kafin mu wuce kan maudu'inmu wato PC Computer kenan mu san cewa dukkan tarkacen komfiuta ta kasune kashi biyu kamar haka:-


1.Ganau
داتعنا
Hardware.


Abinda ake nufi da hardware shine dukkan abinda ake iya gani kuma a taba a jikin komfiuta kamar Allon talbijin da madannai da dan bera da sauransu.2.Gagara gani خايحيشثنا Software.

Abinda ake nufi da Software kuma shine dukkan abinda ba'a iya gani kuma ba'a tabawa ajikin Komfiuta suma sun kasu kashi uku kamar haka:-

1.Manhajar kunnawa.     ميغشتنا واظن     OS/Operating System.


Abinda ake nufi da Operating System shine wata manhajar da kamfani ta tsarashi musamman don ya baiwa Komfiuta umrani tayi dukkan abinda aka sakata kamar kunnawa da kashewa da dukkan umarninda mai amfanida Komfiuta yake bata ita wannan manhajar itace take zama dan aike tsakanin Komfiuta da mai amfani da ita in babu wannan manhajar Komfiuta ko kunnuwa baza tayiba balle tayi wani abu.

Itama wannan manhajar ta kasu kashe-kashe masu yawa amma ga wanda aka fi yin amfani dasu yanzu kamar haka:-

1- Windows Xp.

2- Windows Vista.

3- Windows 7.

4- Windows 8.

Amma yawancin masu Komfiuta sun fi yin amfani da Windows 7 wadanda kuma Komfiutarsu bata da majiya mai girma su sunfi yin amfani da Windows Xp sooda ita ata cin waje sosai.
2.Manhajojin aiki. حيميثطتنا حياشثنا   Application S.ware.

Abinda ake nufi da Application Software kuma itace dukkan wata manhajar da kamfanin Komfiuta ko wasu mutane na musamman suka hada don tayi wani aiki na musamman a cikin Komfiuta itama tana da yawa amma ga misalin kadan daga cikinsu:-

1- Microsoft Office.

2- Corel Draw

3- Anti Virus.


Na farko shi Microsoft Office a cikinsane ake samun Word wanda ake amfani dashi don yin rubutu a cikin Komfiuta domin in babu shi ba yadda za'ayi kayi rubutu mai tsari a cikin Komfiuta har ka buga a takarda.

Na biyu shi Corel Draw kuma da shine ake amfani don ayi dukkan wani zanen abubuwa ko kuma canza musu tsari da sauransu in babu shi a cikin Komfiuta ba yadda za ayi kayi zane mai kyau har ka buga shi a takarda.

Na uku shi kuma Anti Virus da shine ake amfani don a cire dukkan wata cutar da take cikin Komfiuta domin akwai abinda ake ce mata bairos wanda in ta shiga jikin Komfiuta sai ta bata dukkan abinda yake cikin Komfiuta ko kuma ta hana Komfiuta yin aiki yadda ta dace ko kuma ta zama bata da sauri da makamantansu don haka sai a saka mata Anti Virus don ta kama wannan cutan ta cire.

#fasaharzamani #Duniyarcomputer #Bintubetv 

NAU'O IN NAU'RAR ZAMANI (MICRO COMPUTER)


Duniyar computer (digital world) part. 6

NAU'O IN NAU'RAR ZAMANI (MICRO COMPUTER)

1. Komfiutar kujera   يثتكًنا بىساحنا  Desktop.


2. Komfiutar T.-da-G.  لىًحًنا بىساحنا   Laptop


3. Komfiutar rubutu   يشتفذنا بىساحنا   Notebook.


4. Komfiutar hannu   يفكنا بىساحناPalmtop.


5. Komfiutar Allo   يحىهنا بىساحنا Tablet.Fadakarwa

Wadannan komfiutocin wadanda suke karkashin maikro komfiuta duk suna yin kusan aiki dayane amma a gaskiya akwai wasu 'yan bambance-bambance a tsakanin wadannan komfitocin ta bangaren yawan aikinda suke yi wanda ya kamata mai karatu ya sani a yayinda yake so ya mallakesu ga bambance-bambancen kuma kamar haka:-

Idan akace Desktop itace wanda ake ajiyeta akan kujera sannan sai a daura mata Allon talbijin dinta (wato monitor) akanta ma'ana CPU yana karkashin Monitor kamar yadda muka nuna hotonsa a sama.

Amma ita Tower itace wanda ake ajiye CPU a gefen Monitor a tsaye ba a konceba kamar yadda muka nuna a sama amma wadannan nau'uka guda biyun duk aikinsu dayane babu bambanci ta wajen aiki saidai wajen saka wasu abubuwa domin shi Tower yana da girma don haka ana iya kara masa wasu tarkace a cikinsa in aka bukaci hakan sabanin Desktop sannan kuma shi Tower shine na zamani haka kuma shi yafi samun cikekken iskarda take shiga cikinta domin ita Komfiuta Tana bukatar iska sosai haka kuma shi tower kana iya ajiye shi ako ina amma shi desktop yana karkashi Monitor sannan kuma shi Tower ya fi Desktopsauri kadan don shi na zamanine amma dai dukkansu sunfi Laptop yawan hanyoyi na shigarwa a jikinsu don haka sunfi Laptop yawan amfani da yin aiki sannan kuma sunfi Laptop juriya da dadewa a duniya haka kuma suna da madannai (keyboard) wanda yafi na Laptop yawan amfani matuka.

Shi kuma Laptop da Notebook dukkansu komfiutocin tafi da gidankane amma kuma bambanci tsakanin notebook da Laptop sune shi Laptop yana da girma sannan kuma yafi Notebook amfani sosai saboda shi laptop yana zuwa da wajen saka faifan CD a jikinsa sannan kuma yana da wasu hanyoyi na shigarda wasu abubuwa a jikinsa wanda Notebook bashi dashi haka kuma yana da babban Allon talbijin (Screen) wanda zai iya nuna maka komai daidai sabanin Notebook don haka shi Laptop yana yin ayyuka masu yawa sama da Notebook.

Amma kuma shima Notebook yana da nasa abinda yafi Laptop misali shi Notebook yana da karamin jiki don haka bashi da nauyi zaka iya tafiya da shi ko ina don hakanema aka kirasa da suna Notebook wato kamar wani dan takardan rubutu sannan kuma yana rike batir sosai fiye da Laptop sannan kuma yana da saukin farashi sama da Laptop.

Haka shima Notebook yafi Palmtop ko PDA yawan ayyukanda yake yi saboda shi Notebook kana iya yin rubutu da shi ko zane sannan ka jona masa Printer (mabugar takardu) ka cire abinda ka rubuta ko ka zana sannan kana iya saka masa abu sannan kuma ka tura a wani ta hanya mafi sauki sannan kuma yana da ma'ajiya mai girma amma kuma shi Palmtop bashi da hanyyoyin shigarwa kamar na Notebook a jikinsa amma kuma shima Palmtop yana da nasa amfanin wanda babu a Notebook ko Laptop misali zaka iya yin amfani da Palmtop a matsayin waya na kiran mutum sannan kuma kana iya yawo da shi a aljihunka sannan kuma shi yana amfani da tsinke ta yadda zaka dinga taba Allonta da shi ko da hannu haka kuma shi yana rike batir fiye da Notebook da sauransu.

Fadakarwa

Palmtop da PDA duk aikinsu dayane kawai dai sunane ya bambanta.


Sannan kuma sai Tablet Computer itama aikinta kusan dayane da Notebook amma kuma saisai Notebook ta fita da yawan aiki na babban komfiuta saboda ita Notebook tana da mashigar wayoyi fiye da na Tablet a jikinta don haka in ka bukaci na'urar Tablet tayi maka wani abu wanda Notebook take yi baza ta iyaba saboda ba tada hanyoyin shigarwa masu yawa a jikinta amma indai karatu da rubutu da kallon wani abu da sauraron abubuwa da shiga intanet da yin rekodinda sauransu kake so to tabbas komfiutar Tablet tana da kyau a wannan bangaren saboda ita tana amfani da hanyar tabawa ta yadda zaka dinga taba Allon talbijin dinta da hannu don tayi maka aiki da wuri.

Sannan kuma wadannan wayoyin hannu masu kwakwalwa wato (Smart phone) suma suna iya shiga karkashin Micro Computer saboda yanzu kusan dukkan abubuwanda Palmtop yakeyi suma sunayi.
To anan zan dakata bayanina gameda ire-iren komfiuta daban-daban da kuma ayyukansu da amfaninsu saboda wadannan bayanan duka mun kawo sune saboda ilimi amma maudu'inmu a wannan littafin zai takaitane kadai akan PC (Personal Computer) wato komfiutar mutum daya shi kuma komfiutar mutum daya ya hada da Desktop da Laptop da Notebook wadannan sune ake nufi da komfiuta a wajen dukkan mai karatun komfiuta da kuma koyanta don haka anan zamu takaita dalilinda yasa muka kawo wadancan abubuwan shine kadai muna sone mai karatu ya fahimci cewa in akace komfiuta wannan kalmar tana da fadi matuka don yana farawane tun daga kan Super Computer har zuwa kan Smart Phone wato wayoyi masu Kwakwalwa don haka kar mai karatu ya daskararda kwakwalwarsa akan komfiutocinda ya saba gani a wajen mutane kadai.

Muhadu a karatu na gaba.

#Duniyarcomputerdawaya #fasaharzamani #bintubetv 

NA'URAN DA TAKE SARRAFA JIRIGIN SAMA.
Duniyar computer (digital world)

Sannan kuma komfiuta ta bangaren girmanta tana da kashe-

kashe masu yawa amma ga mafi muhimmancinsu kamar haka:-

1. Komfiuta gagara badau   قلاًعنا بىساحنا   Super Computer.


Abinda ake nufi da Super Computer:- itace komfiutar da tafi kowane


komfiuta girma da kuma aiki a duniya wannan komfiutar kuma akace a duniyama su biyarne kachal hudu suna Amurka (America) daya kuma tana kasar Jafan (Japan) kuma ba'a sayar da ita soboda akwai yarjejeniya tsakanin jafan da Amurka na yin amfani da ita amma saidai daga baya sunci gaba da kera wasu ire-iren wannan Komfiutar saidai amma kwannan kasar Chana (China) tayi ikirarin cewa ta kera wata Komfiuta mai suna Sanwe Taihunlait (Sunway Taihun-Light) itama kuma Super Computer ce wanda zata iya fin kowane Komfiuta sauri da yin aiki a duniya kamar yadda suka fada.


Wato Sunway Taihulight din kenan.2. Komfiuta mai girma يزكشيلا بىساحنا  Main F.

Abinda ake nufi da Main Frame Computer:- itace dukkan komfiutar da take da girma sosai ammadai girmanta bata kai Super Computer ba galibi ana amfani da itane a manyan bankuna da kuma kamfanoni masu karfi inda ake bukatar aiki masu yawa sannan kuma tana iya duba kan kananan komfiutoci masu yawa ita kadai.3. Komfiutar kulawa   ىكحتنا بىساحنا  Ctl C.

Abinda ake  nufi  da  Control  Computer:-  itace  dukkan

Komfiutar da ake amfani da ita wajen kulawa da wani abu misali komfitar da ake amfani da ita wajen kulawa da tashin Jirgin sama da saukansa saboda shi jirgin sama ba kamar mota bane ana kulawa dashine ta hanyar Komfiutar da take cikinta wanda kuma tana da alaka da komfiutar kulawa a kasa haka kuma da Komfiutocinda ake amfani dasu a Asibiti a lokacinda ake kulawa da jikin dan adam wanda yake cikin wani yanayi na musamman ko kuma wanda ake amfani da ita ta wajen aika makami mai linzami (misile) a lokacin yaki ko kuma irinwanda Jirage marasa matuka na Amurka suke amfani dasu ta yadda za'a tayara da jirgi daga matashinsa yaje duk inda ake so yayi luguda wuta ya kashe mutane kuma ya komo ya sauka a tashansa ba tareda matuki ya shiga cikiba wannan duka ana yine da Control Computer haka kuma kamar motarda aka kera Kwanannan a kasar Amurka wanda take tafiya tana daukan fasinja taje ta saukar ba tareda dreba ya tukataba itama tana aikine da Control Computer da sauransu misalan suna dayawa akan haka.


4. Komfiutar tska-tsaki طسىتًنا بىساحنا    Mini Computer .

Wannan nau'in bata da wani hoto na musamman.Abinda ake nufi da mini Computer:- itace dukkan Komfiutarda ake amfani da ita a wasu kamfanoni da Jami'oi da sauransu ita tafi kananan komfiutoci amma kuma bata kai manyan komfiutociba wato Main Frame kuma tana iya yin aiki mai yawa a lokaci daya.


Wannan nau'inkuma ya rabu gida


dayawa amma ga

5. Karamar komfiutaكيلذنا بىساحنا   Micro Computer.
muhimmansu


kamar haka:-Abida ake nufi da Micro Computer:- ita bata da wata fassara na musamman saboda ita Micro Computer sune dukkan kannanan komfiutocinda muke amfani dasu wanda sun hada da Desktop da nau'insa guda biyu wato Tower da Desktop da kuma komfiutar Laptop da Notebook da Palmtop da na'uinsa guda biyu wato PDA da shi Palmtop da Tablet da Smart Phone wato waya mai kwakwalwa wanda take aiki da manhajar Android da sauransu.

To a takaice wadannan sune ire-iren Komfiuta tawa bangaren aikinsu da manufarda aka yi su don shi da kuma girmansu sannan kuma anji aikin kowannen daga cikinsu kuma anga hotunansu sai kuma abinda ya shafi maikro komfiuta

suma ga su kamar haka:-

Sai mun hadu a karatu na gaba.


#Fasaharzamani #duniyarComputer #bintubetv 

DUNIYAR COMPUTER, AMFANIN KOMFIUTA DA INDA YAKE AIKI.
Duniyar computer (digital world) part. 4

Komfiuta ta bangaren aikinta ta kasu kashi uku

kamar haka:-


Hausa larabci turanci1.Komfiutar lissafi.    يًلشنا بىساح     Digital Computer


Abinda ake nufi da Digital Computer:- itace dukkan Komfiutarda take karban bayanada ake saka mata ta mayar dashi rubutu sannan tayi abinda ake bukata. Kuma ita tana da sauri da kyan aiki don haka ake amfani da ita ta hanyoyi masu yawa kuma itace irin Komfiutocinda muke amfani dasu a yanzu .


2.Komfiutar gwaje-gwaje  يسايمنا بىساح Analog C.

Abinda ake nufi da Analog Computer:- itace dukkan komfiutarda

ake amfani da ita don yin gwaje-gwaje kamar goda kafrin iska ko yanayin duniya da karfin wutan lantarki ko yanayin aikin jikin mutum da sauransu wannan nau'inkuma shine ake amfani da shi a asibiti da cibiyoyin auna yanayin duniya da sauransu.

3. Komfiutar hadaka. نيدهنا بىساح     Hibrid Computer

Abinda ake nufi da Hybrid Computer:- itace komfiutar da aka hada aikin Digital da Analoge a jikinta saboda ana bukatar dukkan ayyukanda komfiutoci biyun suke yi don saukakawa ma'aikaci.
Sannan kuma komfiuta ta bangaren manufarda akayita

itama ta kasu kashi biyu kamar haka:-
1. Komfiutar K. da ruwanka   واعنا ضشغناور بىساح   G. purpose C.

Abinda ake nufi da General Purpose Computer:- itace dukkan komfiutarda aka yi ta don tayi ayyuka masu yawa ta kowane bangare kawaidai abinda ake bukata shine a jona mata wasu abubuwa a jikinta don tayi aikinda ake bukata.
2. Komfiuta M. manufa daya   صاخنا ضشغنا ور بىساح  S.purpose C.

Abinda ake nufi da Special Purpose Computer:- itace dukkan komfiutarda aka kerata don tayi wani aiki na musamman kamar komfiutar da ake amfani da ita a lokacin siyasa don ta tantance wadanda za suyi kuri'a ko kuma komfiutarda ake kerata don a ayi wasan gem (Game) na yara ko kuma komfiutar da take gidajen Rediyo ko TV da sauransu wanda in aka kaita wani waje to babu wani aikinda zatayi don ba'a yita don tayi wani aikiba.
Sannan kuma komfiuta ta bangaren girmanta tana da kashe-

kashe masu yawa amma ga mafi muhimmancinsu kamar haka:-

[DUNIYAR COMPUTER] SAMUWAR KOMFIUTA DA CI GABANTA.


Duniyar computer (digital world) part. 3

Samuwar komfiuta da ci gabanta

Tabbas kamar yadda malan bahaushe ke fadane cewa "da anki da anso dole ace da mijin iya baba" don haka dole mu jinjinawa malan bature nasara asaran duniya dukda cewa shi Nasara ya zama Fitila ya amfani mutane ya kona kansa ammadai dole mu fadi falalarsa saboda yadda shine ya kirkiro mana Na'urar Komfiuta cikin taimakon Allah domin sun taimaka wajen ci gaban duniya duk da cewa sudai sunyitane da wasu manufofi da kuma yin alfaharin kirkiro wasu abubuwa a duniya amma ba don mu mu amfanaba musammanma kuma ta bangaren amfanar musulunci amma dai Allah ya kaddara cewa su zai fifita da wannan aikin na kirkirar komfiuta sannan kuma mu muzo mu amfana da abinda suka kirkira don mu gabatarda addininmu da tunaninmu zuwa gaba don haka alal hakika komfiuta babu wani abinda dan adam yayi a duniyar ilimi wanda yake da ban mamaki da kuma taimakawa dan adam kamar komfiuta don haka ya zama wajibi ga dukkam mai neman ci gaba a duniyar ilimi da kuma taimakon addininsa a wannan zamani ya koyi komfiuta gorgodon iko saboda ita Komfiuta kogine wanda bashi da karshe saidai kawai ka koyi abinda zaka koya daga gareta amma babu mai kureta yakai bango.

Domin suma turawanda suka kirkiri Komfiuta haka suka yi ta fama da ita shekaru aro-aro har zuwa yanzu kullum kuma kara ci gaba take yi sannan kuma ana kara mata wasu abubuwa daban-daban kuma ana rage girmanta sannan ana inganta kyunta har zuwa yanzu domin malamai sukace an fara tunanin kirkiran Komfiutane tun a shekara ta 1833 wato kimanin shekara dari biyu da goma sha kenan amma bai gama cimma burinsaba har ya mutu sannan wasu turawa suka daura a inda ya tsaya sanna kuma a shekara ta 1934 aka samu wasu kamfanoni na Amurka (America) suka hadu a karkashi wata kamfani mai suna IBM suka fara ciyar da Komfiuta zuwa gaba da kadan-kadan dukda cewa su suna kirkiran Komfiutace a wannan lokacin da wasu manufofinsu na yaki da mallakar duniya da sauransu sannan kuma su Komfiutrda suka kirkira a wancan lokacin tana da girma sosai wanda akace girman komfita daya ta kai girman babbab gida ko beni sannan kuma nauyinta yakai kilo (Kg) dubu talatin (30,000) sannan kuma yana jan wuta kimani kilo wat (Kw) dari biyu (200) wanda karfin wutanda ita kadai take ja zai iya kunna Komfitoci sama da guda dari shida (600) a yanzu don hakanema akace idan aka kunna wannan Komfiutar sai kaga dukkan wutan lantarki na birnin ya yi kasa amma kuma har abin yazo ya bunkasa cikin wadannan shekarun.A sanadiyar samun wata ci gaba da suka yi na samun wani kayan wuta da ake kira Transisto (Transistor) wanda shi karamin abune amma kuma yana dauke da tarkece masu yawa a cikinsa sai suka yi amfani dashi suka bunkasa Komfiyuta daga baya kuma aka sake samun wata ci gaba na abinda ake kira da suna Froseso (Processor) mai karamin jiki wanda shima wani dan karamin abune amma kuma yana daukeda dubbunnan na'urori a cikinsa wanda kuma shine asalin kwakwalwar Komfiuta hakadai aka yi ta ci gaba yau har Komfiuta ta shigo Nijeriya harma ta shiga hannuna da hannunka bayan an dauki wasu shekaru masu yawa ana fama da ita a kasashen Turawa.

To amma kar mai karatu ya fahimci cewa ita Komfiuta itace kadai wadanda ake amfani dasu a yanzu wajen rubuce-rubuce da aika sakonni da ture-ture da sauransi A'a ita Komfiuta ta kasu kashi daban –daban gorgodon ayyukanda suke yi da girmansu da kuma manufofinda akayisu don ita ga kuma ire-iren nasu kamar haka:-


Anan zamu dakata a fitowa na gaba muna dauke da bayanan bangarorin computer da yadda ake amfani da su.

  #Fasahar zamani.

[DUNIYAR COMPUTER] REBE REBEN COMPUTER A MATAKIN FARKO.


Shawakat Computer institute بوساحلل تكوش دهعم

Duniyar computer (digital world) part. 2

dalubai da kuma sauran masu karatu saboda ina son in koyarda abubuwanda na rubuta cikin tsari da bin lokaci.
Haka kuma zanfi baiwa bangaren koyan sunayen tarukucen Komfiuta (Computer) da kuma raben-raben Komfiuta (Computer) da ayyukansu muhimmanci sannan kuma sai bangaren manhajin rubutu a Komfiuta (Computer) wato (Microsoft word) sannan kuma sai manhajin zane-zane wato (Corel draw) saboda wadannan abubuwanda na fada sunfi muhimmanci ga wanda yake so ya koyi Komfiuta (Computer) a karo na farko da kuma wanda yake son yin karatu da Komfiuta (Computer).

To kamar yadda sanin kowane mai harka da Komfiutane (Computer) ne ko kuma wanda yayi karatun Komfiuta (Computer) cewa muna da manhajarda ake ce mata Microsoft office wanda yake dauke da bangarori daban-daban na amfani a cikinta wanda yawansu yakai guda tara kamar haka:-

1. Microsoft Word

2. Microsoft Publusher.

3. Microsoft power point.

4. Microsoft Excel.

5. Microsoft outlook.

6. Microsoft One note.

7. Microsoft Info path.

8. Microsoft Groove.

9. Microsoft Access.

To wadannan sune abubuwanda suke cikin Microsoft Office amma ganin cewa wasu abubuwan aikinsu baya zuwa da wuri ko kuma mu bama amfani dasu a yawancin lokaci shi yasa ko makarantar koyan Komfiuta (Computer) kaje sai kaga ba'ayinsu don haka muma zamu takaita akan abubuwa guda uku kamar Word da publisher da Excel kadai amma hakan bazai hana mu taba sauran abubuwan a takaiceba sannan sai mu wuce kan Corel draw in Allah ya bamu ikon yin hakan to a karshe ina mai sake rokon Allah da ya bani ikon kammalawa kuma ya agazamin wajen fadan daidai kuma ya sannan karbuwa cikin abinda zan rubuta kuma Allah ya sa ya amfani wadanda zan yi dansu amin sannan kuma zan yi wa wannan littafin nawa taken Duniyar Komfiuta.

Muhadu a zongon na gaba.

#Fasahar zamani.

YADDA AKE TSARA RUBUTUN HAUSA


Ka koyi harcen Hausa a rubuce.

1. Mama ta na dafa nama, ta duba ko ya dahu.
2. Baba ya ga zabuwa, ya  fake ta ya kama.
3. Da ana sabo da kuka, da Jaki ya saba da kukawa.
4. Ana hira ana raha, yara Sun kyalkyale da dariya.
5. Soja ya ja damara, ya yi shirin yaki.
6. Yaro ya gudo daga makaranta,  ya sami loko yabuya.
7. Bera barawo ne, ya sace kudin mama.
8. Ali ya ci abinci, ya sha ruwa Ya yi gyatsa.
9. Ana taso 'yan makaranta, sun tsaya a hanya.
10. Damuna ta fadi, kowa ya tafi gona.
11.Malam ya shigo aji, dalibai sun Nutsu.
12. Lokacin jarrabawa ya zo, 'yan makaranta sun himmatu.
13A kwai kasuwa a grain mu, ta na ci kowane mako.

Domin samu rubutu masu alaka da wannan lasa link din dake kasa.
https://www.bintubetv.com.ng/2018/12/mai-bazazzgiyya-tareda-kaidojin-harcen.html

14. Gishiri in ba kai ba miya,
ilimi mai gyaran zamani.
15. Hutun makaranta ya Kare, dalibai sun koma makaranta.
16. Amina ta je makaranta, malam ya ba ta littafi.
17. Akwai kasuwa a garinmu,  ta na ci kowace rana.
18. Ga umman mu, umma ta iya girki.
19. Karya ba ta da kyau, ta na rage darajan mutum.
20. Ilimi dadi gare shi, ya na daukaka mutum.
21. Biri yana cin ayaba, ayaba abincin biri ce.
22. Yau mun je makaranta, malam ya shigo ajin mu.
23. Kwadayi mabudin wahala, duk mai leads to zai wahala.
24. Damuna ta sauka, manoma suna Myrna.
25. Baba ya sayo min Keke, kowa ya na murna.
26. Ana biki a gidan mu, baba ya yanka rago.
27. Karnuka su na yin gadi, karnuka ba sa bacci.
28. Lema ta na amfani, ta na kare ruwa da rana.

#Fasahar zamani
www.bintubetv.com.ng

DUNIYAR SOLA (SOLAR SYSTEM) IRIN KAYAKEN SOLA TAKE AMINCEWA DA WURI TV, FANKA & FIRIJI ETC.

Cigaba da darasin littafin Duniyar sola part 14.

In akwai frigi a gida sai a yi kokari a nemi frigin sola kamar haka:-


In akwai fanka ko dutsen guga na wuta ko hita (heater) na dafa ruwa a gida to
duk a mayar dasu na DC kamar haka:-


Hatta cajin yawa ana so mai amfani da sola yayi amfani da caja mara tranfoma
ma’ana yayi amfani da caja wanda baya jan wuta ya rike irin na da ana so ayi
amfani da caja mara jan wuta kamar haka:-

To wannan shine abinda zan iya fada a gurguje saboda dama wannan littafin
nayisane sabodsa dalubai na a makarantar islamiyya amma kuma hakan bazai
hana wani ya karu dashiba saboda ilimi bataccen kayan muminine duk inda ya
sameshi sai ya dauki kayansa duba ga shekarun wadanda zan koyar dasu da
kuma yanayin iliminsu sai in katse anan in Allah ya kai mu littafi na biyu a karo
na gaba sai mu fara akan abu mai muhimmanci a cikin ilimin sola wato shine
yaya za’a yi ka gane yawan allon solanda kake bukata a gidanka ko shagonka
ko ofis da kuma yawan baturanda kake bukata da kuma yadda ya kamata a hada
sola ba tareda an samu matsalan gazawan wutaba domin a gaskiya yawancin
masu hada sola indai ba mutum ya koyesa bane ta hanyan ilimi yadda bature ya
tsara kayansaba to anan sai kaga ana kiran mutum da suna injiniya amma kuma
in ya hada maka sola sai kaga ana samun matsalan karancin wuta ko kuma
rashin kai lokacinda ake bukata da sauransu to wannan duka yana faruwane a
sanadiyyar rashin sanin yadda za’a lissafa kayan wuta na gida da kuma karfinsu
da kuma wutanda suke bukata da sauransu to sai ince da mai karatu sai mun
hadu a karo na gaba kafin zuwa wancan lokacin kuma duk wanda ya karanta
wannan littafin nawa yaji dadinsa ko ya karu ina neman addu’a na alkhairi daga
wajensa da fatan Allah ya karamin ilimi wanda zan amfani al’ummar Annabi
s.a.w. da shi kuma ya tsawaita rayuwarmu don mu dade munayi kuma ya biya
mana bukatunmu na alkhairi na kusa da na nesa amin.

A karshe sai ince duk wanda ya kalli kuskurena sai yayi kokari ya sanar dani
don ingara a karo na gaba domin masu Magana sunce mai tsoron kuskure baya
zama goni sai ku tuntubeni a kanwadannan adreshim kamar haka:-

G.S.M.: 08027789545/what’s app/pace book by idris abubakar muhammad
G.S.M.: 07066627321
Sibawai2@gmail.com
Nobody is perfect but practice make perfect

الكمالة هلل والعصمة لألنبٌاء
Wassalamu alaikum.

Alhadu lillah Allah yasakawa Mal. alheri da irin wannan namijin kokartawa Kai ba nan kadai yatsaya ba. Mal ysnada littatafai da dama na Duniyar fasaha.

Sannan Ni da na harhada  na tsara yakai ga mai Karatun neke cewa ku kasance tare damu a wannan site mai suna ⤵️

Fasahar zamani

  1. www.bintubetv.com.ng

DUNIYAR SOLA (SOLAR SYSTEM) YADDA AKE HADA CIKEKKEN SOLA A GIDA, OFFIS KO SHAGO.


Cigaba da darasin littafin Duniyar sola part 13.

Flexible wire hard wire


Wannan kuskurenda mai karatu yake gani a sama kuma shine wasu suna hada
sola da wayan wuta na gida ko kuma waya mai tauri to a wannan yanayin ba
yadda za’ayi sola tayi aiki mai kyau sai a kiyaye.


Wannan kuskurenda mai karatu yake gani a sama kuma shine rashin wanke
allon sola ko gegewa daga lokaci zuwa lokaci domin ita allon sola yadda bature
yayita shine bazata baka wutanda aka rubuta ajikintaba yadda ya kamata har sai
kabi ka’idojinta don haka in mutum ya bar allon solansa da kura ko kasa ko
datti ko kashin tsuntsaye da sauransu a kai ko kuma wajen akwai inuwa na
bishiya ko kuma ganyen bishiya yana faduwa akanta to ba yadda za’ayi mutum
yaji dadin amfani da solansa don haka ya kamata a dinga wanke allon sola ko a
gogeta daga lokaci zuwa lokaci kamar bayan sati biyu zuwa wata daya don kar
wutan ya samu matsala in kuma allon solanda ake amfani dashi mara dayodne
to in kura ko inuwa ya rufe wani bangaren to zai iya cutarda allon solamma gaba
daya.

To a takaice wadannan sune wasu daga cikin kura-kuranda masu hada sola suke
fadawa a karshe kuma kafin in rufe wannan littafin naga ya kamata na kawo
wasu daga cikin dabarunda ake yi a rage kudin hada sola domin ita sola a
gaskiya ba abin talaka bane indai akace za’a hadashi a irin hadinda
ma’aikatansa suke yi saboda akwai kashe kudi matuka domin ko daki daya kake
so ka hada masa sola alhali kana da TV da fanka da dish da golobdinka da
wayan to sai ka kashe kamar dubu dari duk wayonka amma saidai akwai wasu
dabarunda ake yi a hada sola da farashi mai araha indai har mutum yana da
masaniya a ilimin kayan wuta to zai hada sola ba tare da kashe kudi mai yawaba
ga kuma wasu daga cikin dabarunda ake yi kamar haka:-


a. Na farko dukkan kayan wutan gida wadanda suke amfani da AC ayi
kokari a mayar dasu DC sannan kuma DC dinma ya zama yana da
karancin watt to sai a hada sola mai sauki misali dukkan kwan wuta da
ake amfani dasu a gida wadanda suke cin watt dari ko sama da haka ko
kasa da haka na wuta sai a mayar dasu na led masu cin watta 5 ko 6
kamar haka:-


Sannan kuma dukkan TV irin na da ko kuma LCD masu cin wuta kamar watt
200 ko sama da haka sai a mayar dasu na LED TV mai cin watt 100 ko kasa da
haka kamar 50 ko 40 kamar haka:-


Anan zamu dakata sai a rubutu nagaba zamu dora wanda yake da matukar muhimmaci kuma da shi zamu rife darasin insha-Allah.

Fasahar zamani
www.bintubetv.com.ng

DUNIYAR SOLA (SOLAR SYSTEM) NA'URAN DA TAKE SARRAFA SAKANIN NEPA & SOLAR.Cigaba da darasin littafin Duniya sola part 11.

Fadakarwa

Mai karatu ya sani cewa wadannan nau’ukan inbatanda muka fada guda
ukunnan dukkansu suna da girma-girma gwargodon bukatan kayan gida domin
akwai inbata mai watt 60 har zuwa 500 ko 1000 ko 1500 ko 2000 har zuwa
5000 abinda yayi sama gorgodon yawan watt dinsa gorgodon tsadansa.Sannan
akwai inbata mai aiki da batir mai voltage 12 akwai kuma mai 24 zuwa sama.
Ga kuma yadda ake bambancesu kamar haka:- Pure sine wave inverter square wave inverter
انفرتر موجة شبه جيبية
Modified sine wave inverter

Sannan kuma ga wasu tambarinda kamfani suke sakawa a jikin inbata
don ka gane a wane nau’I yake kamar haka:-


Tamabarin fiwa sain web tambarin modifaid tambarin skwaya web
To atakaice wadannan sune rukunnan hada sola ta yadda indai ana so a hada
sola da sunan sola dole sai an bukacesu yanzu kuma sai mu wuce gaba don
muga yadda kuma ake hada wadanan rukunnan a waje daya don suyi aiki kamar
haka:-

To a takaice wannan shine yadda ake hada wadannan rukunnan guda biyar don
su bada wuta a gida har a amfana a wani lokacin kuma mutum zai bukaci ya
kara yawan allon sola domin ya samu wuta mai yawa to a wannan lokacin
akwai abinda ake ce masa series connection ko kuma parallel connection ta
yadda zaka hada allunan sola koda guda darine a waje daya yadda ake yi kuma
shine in mutum yana so ya kara karfin wutane wato voltage sai yayi series
connection wato zai hada waya mai tambarin kari (+) na allo daya da kuma
waya mai tambari ragi(-) na allo daya sai ya hadasu tare sannan sai ya dauko
wayoyi biyunda suka rage sai ya daura akan batir ga yadda yake kamar haka:-


In kuma kana so ka kara wutan caji wato amp sai ka hada waya mai tambarin
kari (+) na allo biyu duka waje daya sannan kuma sai ka hada waya mai
tambarin ragi biyu suma waje daya sannan sai ka daurasu akan batir ga yadda
ake kamar haka:-

Ya mai karatu sai munhadu a wata matashiya.

Fasahar zamani.
www.bintubetv.com.ng
Hey, we've just launched a new custom color Blogger template. You'll like it - https://t.co/quGl87I2PZ
Join Our Newsletter