001-234-567-8910

5th Avenue Madson, NY758, USA

Get Update on our recent Gadgets & Tabs

Add this

Add this

Web Design Agency Nigeria https://www.ads54.com/ad/a/10595_4daf76b52369930

Add this

Website Value Calculator - Domain Worth Estimator - Buy Website For Sales

Add This

KASAN YADDA DUNIYA TAKE CIKI.Yadda Ake Bincike A Google

Assalamu alaikum, yau zamu yi magana akan yadda ake bincike a Google, sai a biyo mu.

Mafi yawan mutane suna amfani da google sai dai zamu iya cewa da yawan masu amfani dashi acikin al'ummar mu basu fahimci google din ba.

Domin yin bincike (searching) a google sai a ziyarci www.google.com

1. Yadda ake samun sahihin bincike daga Google.
Misali: Idan na rubuta Sharfadi nayi searching sai ya bani saka mako guda 50,100 domin zai kawomin duk wani abu dake da alaka da kalmar ko yayi kama da ita wadda ya sani.

Amman ina saka masa alamar magana kamar wannan "sharfadi" to zanga ya takaitamin results din zai bani in gantaccen abinda na nema ba tare da yin kwashe-kwashe ba.

2. Idan ina son na binciki ma'anar wani abun ko wata kalma, misali zamu nemi ma'anar kalmar GIRL.
To yadda yakamata na rubutu shine: Define:Girl to zai kawo min ingantacciyar ma'ana babu kwashe-kwashe.

3. Idan ina son nayi searching wasu kalmomi guda biyu misali zanyi search akan Kwankwaso Da Shekarau ko Kano da Jigawa to yadda zanyi shine:

Zan rubuta Kano-Jigawa zan sanya alamar debewa (minus) a tsakaninsu kuma babu space.
To zai bani amsar duk Inda wadannan kalmomi guda biyu suka zo a Internet ba zai bani kalma daya ita kadai ba.

4. Idan zan binciki wani abu da shekara misali zaben 2015 to kawai zan rubuta.
Nigerian Election -2015

To duk amsar da ya bani zai bani ta wannan shekarar ne.

4. Yadda ake searching din website:
Idan kana son yin searching wani website a Google misali zamuyi search Sharfadi.com yadda za kayi shine:
sai ka rubuta: site:sharfadi.com ko bintubetv.
com.ng
To zai kawo maka dukkan bayanan dake da alaka da wannan website din.

5. Yadda Ake Searching website masu alaka:
Misali BBC.com shafi ne na labarai sai nake son samo wasu shafukan masu kama dashi wadanda suke aiki iri daya, to yadda zanyi shine:
Sai na rubuta: related:bbc.com
To zai kawo maka shafukan da suke kawo labarai masu kamanceceniya da BBC.

6. Yadda ake searching Littafi a google:
Idan kana son yin searching Littafi a google kai tsaye sai kaje https://books.google.com

7. Yadda ake yin searching da hoto a google :
Da yawa mutane basa amfani da wannan bangaren kuma abune mai matukar amfani, yadda yake shine idan kana da hoton wani abu to kana sakawa zai yi maka bayanin hoton, misali ka saka hoton Shugaban kasa kana sakawa zai kawo maka cikakken bayani akan shugaban kasar.
Yadda ake yi shine zaka ziyarci https://images.google.com

8. Yadda ake neman aiki ta Google:-
Zaka shiga google sai ka rubuta "Job near me" to zai kawo maka wuraren da suke neman aiki a yankin ka.

Zamu dakata anan sai a rubutu na gaba.

Domin karanta sauran rubutukan da suka gabata sai a ziyarci www.sharfadi.com

Email: info@sharfadi.com
Call & WhatApp: 09035830253

Basheer Sharfadi
Social Media Strategist.
#BasheerSharfadi #Google #GoogleSearch #GoogleImageSearch #GoogleBookSearch

No comments:
Write comments

Hey, we've just launched a new custom color Blogger template. You'll like it - https://t.co/quGl87I2PZ
Join Our Newsletter