001-234-567-8910

5th Avenue Madson, NY758, USA

Get Update on our recent Gadgets & Tabs

Add this

Add this

Web Design Agency Nigeria https://www.ads54.com/ad/a/10595_4daf76b52369930

Add this

Website Value Calculator - Domain Worth Estimator - Buy Website For Sales

Add This

CIKEKKEN BAYANI YADDA MUTUM ZAIYI KARATUN DEGREE NA 1,2 HAR NA 3... TA INTERNET.Shafin an tsara shi a sigar tambayuyi da amsoshi.

 1 ~TAMBAYA~
Shin yayin da mutum yake daukar Jarrabawa bayan yayi Register da Makaranta shin ya yanayin Jarrabawar zai Kasance? Ma'ana Live za'ayi Masa Jarrabawar Kamar Video Call ko Yaya?
* AMSA
Ya danganta da makarantar, amman mafi yawa ba Live suke Wai ana kallonka ba. Sai dai akwai masu yin Live na lokaci.
       Misali ace zaku fara karfe 8 zuwa 9 to in lokaci yayi ko ka gama ko baka gama ba shikenan, Kamar dai Jamb.

 2 ~TAMBAYA~
 Shin zan iya register a makarantu dayawa?
 * AMSA
Eh zaka iya.

3 ~TAMBAYA~
Shin anan gida Nigeria ana consider din karatun ko yaya, wato accreditation?

* AMSA
Eh ana yi sai dai in makarantar ba ingantacciya bace. Anan sai ku kula ba komai ne za'a turo muku ace Online Learning ko Online Business ka karba ba. Akwai wanda na gan-gan ne.
    Karin cikakken bayani ka nemi shirin mu na *Mukoyo Computer a Sauke* wanda zaku iya samu a Sharfadi.com wanda nayi bayani akan 'Yan Damfara a Internet.
 
   4 ~TAMBAYA~
Ya ingancin makarantun yake a Nigeria?
     * AMSA
Yanzu Haka daliban National Open University (Noun) an amince da su fara zuwa Bautar Kasa. Wannan a matakin Degree Kenan sauran kuma daman karbabbu ne.
  -Makarantar ce ake bukatar ta zama ingantacciya.
 5  ~TAMBAYA~
Shin karatun zai zamo kamar wani karatu da akayi a waje?

* AMSA
Eh yanzu mafi yawan manyan makarantun duniya ma sun samar da tsarin karatun online.
      Misali :
BUK sai ta bude bangaren online mutum yayi register kuma shima dalibinta ne har ya gama karatu.
   Idan kayi karatu a daya daga cikin irin wadannan makarantun kwalinka na kasar waje ne sai dai zasu nuna cewa kayi karatu ne ta Yanar gizo wanda amintacce ne a duniya a hukumance.A nan ma Mutanemmu ne da basu da wayewa akai ba.

6 ~TAMBYA~
Ta yaya za'a gane cewa wannan makarantar ta online ingantacciya ko kuma akasin haka?
  * AMSA
Yauwa wannan kuma gaskiya idan mutum bashi da ilimin yin bincike a internet kada ya shiga har sai ya nemi sanin ingancin ta saboda ba rubutawa ake cewa Wannan makarantar ta Jabu bace.

7 ~TAMBAYA~
Mutum zai iya yin ko wata makarata ne?
  * AMSA
Eh sosai ma kowa, sai dai wasun zakai la'akari da lokacin jarrabawansu.

  8 ~TAMBAYA~
Ya tsarin time table nasu yake, shin acikin sati kullum ne akeyin wannan karatu kokuma?
  * AMSA
Ya danganta da makarantar da mutum ya cike. Wani kuma har iya lokacin da ka gama domin suna baka lokacin a Hannunka duk sanda ka samu time zakayi.


  9 ~TAMBAYA~
Wajen neman aiki a company ko wajen gov't yaya girman kwalin shin zaiyi daidai da karatun Wanda bana internet ba?

* AMSA
Eh.


 10 ~TAMBAYA~
Wai duk makarantun kyuta ne ko ana biyan Kudi?

 * AMSA
A'a akwai na kyauta akwai kuma na Kudi.

Akwai kuma wanda sai ka gama zaka biya kudin certificate.


11 ~TAMBAYA~
Shin akwai makarantun online da suke koyar da mutane amma da harshen Hausa ko babu?

 * AMSA
Akwai International University of Languages (iOUL) a nan Nigeria suna da Study Center a Sokoto.

Sannan, tamu Idan mun kammala ta harshen Hausa ce zalla. Wato makaratar cibiyar, SHARFADI.COM


 12 ~TAMBAYA~
Shin wadannan test din da  kuma exam din da mutun zai  yi  duka suma ta online ne ko suna da centre ne inda mutun zai je yayi?

 * AMSA
Eh online ne ta wayarka ko computer. Amma akwai wadansu makarantun online sun's da center musamman lokacin jarrabawa.


     # Hadawa Muh'd M. Umar.

No comments:
Write comments

Hey, we've just launched a new custom color Blogger template. You'll like it - https://t.co/quGl87I2PZ
Join Our Newsletter