001-234-567-8910

5th Avenue Madson, NY758, USA

Get Update on our recent Gadgets & Tabs

Add this

Add this

Web Design Agency Nigeria https://www.ads54.com/ad/a/10595_4daf76b52369930

Add this

Website Value Calculator - Domain Worth Estimator - Buy Website For Sales

Add This

DUNIYAR SOLA (SOLAR SYSTEM) NA'URAN DA TAKE HADA SAKANIN SOLA & NEPA.Cigaba da darasin littafin Duniyar sola part 10.

                         Menene inbata?

Inbata itace wata na’ura wanda ake amfani da ita a sola domin ta juya wutan
batir mai voltage 12 ko 24 zuwa ga wutan nefa mai karfin voltage 220
Shi inbata kuma aikinsa shine juya wutan DC (wutan Batir) zuwa wutan AC
(wutan nefa) domin muna da kayan wuta iri biyu akwai kayan wuta na DC
wadanda suna iya amfani da batir kai tsaye akwai kuma kayan wuta na AC
wadanda basa iya amfani da batir kai tsaye don haka sai ayi amfani da inbata
domin ta juya wutan batir zuwa wutan nefa sannan kuma inbata ta wajen aikinta
ta kasu kashi biyu akwai inbata wanda tana iya yin cajin batir sannan kuma ta
juya wutan batir ta koma nefa sannan kuma akwai inbata wanda bata caji ita
kadai juya wutane aikinta.
 Haka kuma inbata ta wajen karfin aikinta sun kasu kashi uku kamar haka:-


Ire-iren inverter=العواكس أوواع

1. Pure sine wave inverter=الجيبية موجة عاكس
2. Modified sine wave inverter=جيبية شبه موجة عاكس
3. Square wave inverter=مربعية موجة عاكس

To wadannan sune nau’I guda uku na inbata bari muji bambancinda yake
tsakaninsu kamar haka:-

Na farko fiwa sain web inbata yana iya daukan dukkan nau’ukan kayan wuta
wanda ake jonasu a jikin wutan nefa har dasu frigi da AC da hita da gugan wuta
da sauransu.

Na biyu modifaid sain web shi kuma yana iya daukan yawancin kayan wuta
amma kuma yana haddasa wasu matsaloli ko kuma kaji yana yin kara da
sauransu.

Na uku skwaya web shi kuma baya iya daukan wasu kayan wuta saidai
kananan kayan wuta.

Sannan kuma akwaima wasu inbatan daban wadanda ana iya hadasu da
wutan nefa domin kamfanin wutan nefa ta amfana da wutan solan da aka hada
indai yayiwa gidan yawa.


Muhadu a rubutu na gaba.

Fasahar zamani 
www.bintubetv.com.ng

DUNIYAR SOLA (SOLAR SYSTEM) WAYOYIN SOLA DABAN TAKE.
Cigaba da darasin littafin Duniyar sola part 9.

4. Flexible wire=المرن السلك

Na hudu daga cikin rukunnan sola shine waya mai taushi ko laushi domin shi
wutan sola ba ‘a hada shi da wayan wutan nefa ko waya mai tauri don haka dole
a samo waya irin nasa sannan kuma wayan ya zama yana da karfi gorgodon
karfin wutanda ake bukata da kuma nisan inda ake so aja wutan da sauransu
wannan kuma ba abune da za’a koya wa mutum a lokaci kadanba sannan kuma
ansan cewa ita waya aikinta kawai shine dauko wutan kawai daga allon sola
zuwa batir amma dai ga irin wayanda ake bukata kamar haka:-


Sai munhadu a wata rubutun

Fasahar zamani 
www.bintubetv.com.ng

DUNIYAR SOLA (SOLAR SYSTEM) YADDA SOLA TAKE SARRAFA KANTA.

Cigaba da darasin littafin Duniyar sola part 8.

3. Charge controller=الشحه مىظم
mppt pwm

To wannan shine na uku daga cikin rukunnan sola ga hoton nau’insa guda biyu
duka wato mppt da pwm zamu zo muji aikin kowanne daga cikinsu in sha
Allahu.


 To shi kuma wannan na’uran aikinsa a jikin sola shine kamar haka:-

1. Yana tsayar da wutanda yake zuwa a jikin allon sola in batiri ya cika ta
yadda batirin bazai baciba indai lead acind ne sannan kuma bazai fashe ya
haddasa gobaraba indai lithium-ion ne.
2. Sannan kuma yana nuna wa mutum yanayin votage din batir wanda ya rage
indai caj-kontrolan yanada allon nunawa wato (Digital) kenan.
3. Sannan kuma yana kunna wutanda aka hada na sola da kansa in dare yayi
sannan kuma ya kashe in gari ya waye ba tare da an tabashiba.
4. Sannan kuma yana rage wutanda yake sauka daga allon sola sai ya daidaitata
kafin ya shigar da shi cikin batir don kar batir din ya baci ko ya kumbura.

To a takaice wadannan sune aikin caj-kontrola.

Sai kuma bambancinda yake tsakanin mppt da pwm kamar haka:-


Shi caj-kontrola mai tsarin pwm aikinsa shine ya karbi wuta daga wajen allon
sola sai ya rage karfin voltage da kuma amp sai ya yi cajin batir cikin aminci in
ya cika shikenan sai ya katse misali allon sola wanda yake cajin batir mai
voltage 12 yana zuwane da karfin voltage 18 ko 19 to in an daura wannan allon
kan batir sai ya kashe batir din da wuri saboda yafi karfin batir din don haka sai
a saka caj-kontrola sai ya rage voltage guda 7 daga cikin 19 sai ya baiwa batir
din 12 wanda yake bukata sai ya watsar da sauran.

 Haka kuma a ka’ida na cajin batir kowane iri batrure yafi so ayi cajin batir da
daya daga cikin goma na amp din batir 1% saboda batir din ya dade a duniya
domin in ya wuce haka batir yana mutuwa da wuri don haka in ka daurawa batir
mai amp 10 allon sola mai amp 15 misali to caj-controla sai ya rage amp goma
sha hudu ya watsar dasu sai ya dinga saka maka amp 1 kawai haka kuma in ka
daura masa allo mai amp dayama shikenan sai yayi amfani da shi a takaice
wannan shine aikin caj-kontrola mai tsarin pwm.

Amma shi caj-kontrola mai tsarin mppt shima yana yin dukkan ayytukanda
muka fada akan na sama amma saidai shi yana da wani aiki dauriya akan na
bayan wato shi baya watsar da komai cikin wutanda yake zuwa daga jikin allon
sola zai rikesune sai ya juya voltage din ya zama amp sai ya dinga sakawa a
jikin batir da hankali sannan kuma shi yana iya daukan allon sola mai voltage
hansin ko dari ko sama da haka sabanin pwm wanda baya wuce allo mai voltage
12 ko 24 zuwa 48.

Amma saidai shi wannan na biyun yana da tsaya fiye da
kima sannan kuma bashi da yawa a kasuwa sosai.

Digital Mppt
Ga yadda aikin kowane yake kamar haka:-


Fadakarwa

Mai karatu ya mayar da hankali domin yan China suna damfaran sabon shiga
fagen sola ta yadda zasu rubuta akan caj-kontrola cewa wannan mppt ne amma
kuma alhali pwm ne don haka sai a mayar da hankali don kar a cuceka kai bama
wannan kadaiba dukkan kayan wuta yan Chaina suna damfaran mutane dashi ta
yadda zasu rubuta abinda ba shine hakikanin yadda abin yakeba sai su sayar
maka shi araha kana jin dadi alhali sun cuceka.

Ana iya gane mppt da kuma pwm ta wajen nauyinsu da kuma kiran jikinsu da
tarukucenda yake cikinsu kamar haka:-

Anan zamu gemtse sai mun muhadu a wata gaba.

Fasahar zamani 
www.bintubetv.com.ng

DUNIYAR SOLA (SOLAR SYSTEM) YADDA ZAKA KARE ALLON SOLANKA.
 Cigaba da darasin littafin Duniyar part 6.

Fadakarwa

Mai karatu kar ya zafafa wajen binciken ingancin allon sola domin dukkan nu’I
guda biyunda muka fada na sola suna da kyau ga mai amfani dashi a gida ko
ofis saboda duk ingancin allon sola akace bazai baka dari bisa darin wutanda
aka rubuta a jikin allon cewa yana fitarwaba saidai ya baka saba’in da biyar
cikin dari 75% na abinda aka rubuta a jikin saboda wasu dalilai kamar:-

* Allon sola yana bukatan hasken rana wanda bata gazaba kuma bata
wuceba ashirinda biyar na ma’aunin karfin rana kafin ta bayar da
wutanda aka rubuta a jikinta in kuma karfin rana ya gaza haka to bazai
bayar da abinda ake bukataba.
* Sannan kuma kura da datti suma suna rage wutanda allon sola take
bayarwa don haka matukar akwai kura ko datti ko wani inuwa koda
kadanne akan allon sola to baza ta bayar da wutanda aka rubuta a
jikintaba.
* Sannan kuma in rana ta karkata ga barin tsakiyan allon sola shima yana
hana allon bayar da wutanda aka rubuta a jikinta.
* Sannan kuma rashin yin amfani da waya mai kyau mai karfi shima yana
saka allon ya ki bayar da wutanda aka rubuta a jikinsa.
* Haka kuma caj-kontrola mai nau’in PWM shima yana rage wutanda yake
sauka a jikin allon sola don ya daidaitashi.

Don haka duk yadda aka fadawa mai karatu cewa allon sola iri kaza shi yafi to
bazai biya masa bukataba indai shi ba masanin sola bane don haka dukkan allon
sola in zaka yi amfani dashi to dole ka zubarda 25 cikin dari na wutanda yake
cirewa inba kahaba baza ka iya hada sola mai kyauba.

Muhadu a zongo na biyu.

Fasahar zamani 
www.bintubetv.com.ng

DUNIYAR SOLA (SOLAR SYSTEM) INGATATTAUN BATURAN SOLA.
Cigaba da darasin littafin Duniyar Sola part 7.

2. Battery=البطارية

Menene batir

Batir shine wani curarren sinadari a cikin akwatin roba wanda yake tara
wutanda yake sauka daga jikin allon sola sai ya tara a cikin don ayi amfani da
shi bayan faduwan rana ko kuma lokacinda rana bata fitaba.
Wato abu na biyu daga cikin rukunnan hada sola kuma shine batiri saidai kuma
batirin sola daban yake da wasu batira kamar batirin mota ko waninsa don haka
ya kamata mu fadi irin batir dinda ake amfani dashi a wutan sola.

 Kafin haka dole musan menene amfanin batiri a cikin sola to shidai batir
amfaninsa kawai shine ya ajiye maka wutanda allon sola ya tattaro daga hasken
rana zuwa lokacinda babu rana domin kayi amfani dashi wannan kadai shine
amfanin batir a jikin sola domin zaka iya amfani da sola koda babu batir indai
da ranane saidai da zaran rana ta fadi shikenan wutanka yak are.

Ire-iren batura

Muna da batura nau’I uku wanda muke amfani dasu a sola kamar haka:-

1. Lead Acid Battery
2. Lithium-ion Battery (Li-ion) Battery
3. LifePo 4 Battery

Sannan kuma kowanne daga cikin baturannan guda uku suna da iri dabandaban
amma mu zamu dauki wanda ya shafemu shine lead acid battery saboda shi
yana da rabe-rabe kamar haka:-

 Akwai wet cell.
 Akwai AGM ko dry cell.
 Akwai GEL.

To wannan na karshen wato gel yafi kowanne karfi da dadewa da kuma rike
wuta da sauransu amma kuma yafi dukkansu tsada.
Sannan kuma ana iya amfanida batir na biyu wato lithium-ion saidai shi yana da
hadari sosai domin yana fashewa indai mai cell ne in wuta yayi masa yawa ta
yadda zai haddasa gobara Allah ya kiyaye amin.

Bayan wadannan batura guda biyun duk batir dinda zaka yi amfani dashi a sola
saidai kawai ka bata kudinka domin bazai iya yi maka aiki mai yawaba wani
batirinma bazai wuce wata da ko sati dayaba zai mutu sai kayi asaran kudinka
amma batir din GEL ko LITHIUM-ION sai kayi shekara biyar kana amfani
dasu basu mutuba.

 Sannan kuma shi batir yana da girma daban-daban wato karfin daukan abu
voltage kenan da kuma karfin dadewa gorgodon dadewan batir da karfinsa
gorgodon kudinsa amma a yawancin lokaci amfi yin amfani da batir mai karfin
voltage 12 ko 24 a gida sannan kuma karfin dadewa kuma 100 ko 200 amma dai
ba dole bane hakan zaka iya sayan sama da haka ko kasa da haka gorgodon
kudinka da bukatanka ga kuma wasu daga cikin hotunan batiran sola don
kusanto da nesa kamar haka:-12
Fadakarwa
Ana iya amfani da batirin mota ko na keke nafe a allon sola ammafa a sani cewa 
bazai dadeba koda kuma sabo aka saya a cikin kwalinsa nanda wasu watanni zai 
mutu saidai kawai ayi amfani dashi ta wajen kunna hasken wuta ko kuma ayi 
amfani da shi da rana inba hakaba bazai iya ajiye wuta domin ayi amfani dashi 
dadaddareba ko a saka inbataba.
3. Charge controller=الشحه مىظم
mppt pwm

Anan zamu dakata muhadu a rubutb na gaba.

Fasahar zamani 
www.bintubetv.com.ngDINIYAR SOLA (SOLAR SYSTEM ) CIGABA ANA AMFANI DA SOLAR A MOTA KO BA PETUR (MAI).

Cigaba da darasin littafin Duniyar sola part 4.

Wurarenda ake amfani da sola

Ana amfani da sola a wurare masu yawa kamar tauraron dan adam wanda ake
harbawa sama taje ta zauna a sama tsawon shekaru hamsin ko sama da haka
inda kuma babu wutan lantarki to ana hada mata wutan solane sannan kuma ana

amfani da sola a dukkannin na’urorinda ake harbawa sama ko kuma ake ajiyewa
a daji inda babu wuta sannan kuma yanzu cigaba yakai ga ana amfani da sola a
jikin manyan jiragen ruwa da jiragen sama da motoci da kananan abin hawa
masu yawa wanda ba sai anzubawa jirgi maiba sai ta tashi sama taje duk inda
zataje haka ma motan sola sannan kuma ana amfani da sola a manyan
kamfanoni da asibitoci da sauran ma’aikatu inda ba’a yarda a dauke wuta
daidaida minti dayaba sannan kuma ana amfani da sola a gidaje inda ba’a samun
cikekken wuta ko kuma ida ba’a samun maida sauransu ga wasu daga cikin
kayakinda suke amfani da sola a cikin ababen hawa:-

Anan zan dakata muhadu a matashiyar mu mai ta
Falalan sola akan wutan nefa ko generator.


fasahar zamani. 
www.bintubetv.com.ng

DUNIYAR SOLA (SOLAR SYSTEM) IRE IREN ALLON SOLA.
Cigaba da darasin littafin Dumiyar sola part 6.

اللوحة الشمسٌة=1.  Solar panel

Mun riga mun yi Magana akan allon sola da farko da kuma nau’insa guda biyu
don haka ba sai mun sake maganaba shi wannan allon kuma aikinsa kawai shine
ya tattaro hasken rana sai ya mayar da shi wuta amma kuma wutan DC daban
yake da wutan AC wato wutan nefa da zaran ya baka wannan wutan to aikin
allon sola yak are.saidai kuma ga abu mai muhimmanci wanda mukayi
alkawarin fadansa a baya wato shine ta yaya zaka gane allon sola mai karfi da
inganci.

 Dukkannin allon sola na poly da mono duka suna da karfinda kamfani tana
bayar da garantin shekara 25 amma kuma akwai wanda tana da ingancindama
yafi haka yadda ake ganeshi da ido kuma shine kamar haka:-
1. Allaon sola mai BB4 domin muna da BB3 da BB4 da BB5 amma gaskiya
ba’a cika sam
un BB5 ba sannan kuma BB3 da BB4 yafi yawa a kasuwa don
haka BB4 shine na tsakiya ta wajen inganci ga hotonsu kamar haka
                BB3                  BB5

2. Na biyu kuma ana gane ingancin allon sola da glashinda aka saka mata
domin ba a so a saka glashi mai yalki sosai a jikin allon sola saboda yana
rage ingancinta don haka mai sayan sola kar ya sayi irin wannan:-

3. Na uku ana gane ingancin allon sola da dayod (diode) wanda yake bayan
allon domin ana samun allon sola wanda babu dayod a jikinsa to wannan
yana da karancin inganci.

Muhadu a gaba tagaba.

Fasahar zamani
www.bintubetv.com.ng

DINIYAR SOLA (SOLAR SYSTEM) FIFIKON SOLAR AKAN NEFA KO GENERATORCibaga da darasin littafin Duniyar sola, part 5.

Falalar solar akan nefa da generator.  

Tabbas sola tafi wutan nefa da generator duka amfani saidai ita sola tana da
tsada a lokacin hadawa amma da za’a daure a hada to yafi kowane irin wuta
dalili kuwa shine shi wutan sola bashi da hadari na kashe mutum ko gobara
kamar na nefa amma indai an hadata mai kyau sannan kuma ita sola babu
wanda zai zo yace maka kawo kudin wuta ko ya yanke maka wuta ko ace duk
Nigeria wuta ta lalalce da sauransu sannan kuma ita sola bata gurbata muhalli
kamar yadda generator yake yi sannan kuma sola baya bukatan sabis ko canza
wani abu indai batir dinta yana da karfi haka kuma sola bata bukatan zuba mai
sannan kuma duk lokacinda kaga dama sai ka kunna kayi amfani da ita
matukardai rana tana fita ta fada to wannan shine wasu daga cikin fifikon wutan
sola akan nefa ko generator.

Rukunnan hada wutan sola

Duk wanda zai hada sola to dole yana bukatan abubuwa guda biyar ko hudu
kamar haka:-

1. Solar panel=الشمسية اللوحة
2. Battery=البطارية
3. Charge controller=الشحه مىظم
4. Flexible wire=المرن السلك
5. Inverter=العاكس

To wadannan abubuwan inhar zaka yi amfani da sola to dole kana bukatansu
dukda cewa akwai abinda shi ba rukuni bane amma kuma yana da muhimmanci
sosai kamar inbata da kuma caj-kontrola to yanzu kuma bari mu daukesu daya
ban daya domin mu bayyanasu gorgodon iliminmu.

Zamu dakata anan muhadu a rubutu nagaba.

Fasahar zamanI. 
www.bintubetv.com.ng

DUNIYAR SOLA (SOLAR SYSTEM) MA'ANAR SOLARCigaba da darasin littafin Duniyar sola part 3.

Ma’anar solar


Kalmar sola kalmace ta Turanci wanda yake nufin kollon Rana ko kuma dukkan
abinda yake aukuwa a sanadiyyar rana ko kuma yake da alaka da Rana don haka
ake cewa Solar Energy wato wutan karfin Rana. Sannan ana ce masaP.V.
(Photovoltaic cell) dukde ana nufin allon sola amma saidai ita sola tana da ire￾ire masu yawa amma mafi muhimmi wanda ake amfani dasu sune guda uku
kamar haka:-

1-Poly
2-Mono
3-Thin film

Amma saidai a yawancin lokaci anfi amfani da poly ko mono saboda
ingancinsu da kuma dadewansu a duniya da kuma yawaitansu a kasuwa ga
hotonsa kamar haka:-


 Mono crystalline Poly crystalline

Banbanci tskanin Poly da Mono

A gaskiya akwai tsabani a wajen fadan bambancinda yake tsakanin Poly da
Mono ammadai tabbas akwai bambanci saidai wannan bambanci bashi da wani
tasiri mai karfi ga mai amfani irina da irinka don haka kar mai amfani da solar
ya damu da wannan bambancin domin dukka nau’ukan biyu suna da kayau da5
inganci da dadewa a duniya har tsawon shekara ashirin da biyar da kuma fitar
da wuta iri daya indai girmansu dayane amma akwai yadda ake gane allon sola
mai karfi sosai da mara karfi wanda shi ya kamata mu fada a gaba insha Allahu.

Anan zamu dakata sai a rubutu na gaba

Fasahar zamani
www.bintubetv.com.ng

DUNIYAR SOLA (SOLAR SYSTEM ) SOLA MAI AIKI DA FARIN WATA.Cigabada da darasin littafin Duniyar sola part 2

Asalin solar
Sola ta samo asali tun shekaru aro-aro da suka gabata alummu na duniya suna
amfani da hasken rana ta wajen dafa abinci ko dumama ruwa da sauransu amma
an fara amfani da hasken rana a matsayinta na solar ne a shekara ta 1839 yau
kamar shekara dari da saba'in da tara kenan wanda kuma wani baturen
Faransane mai suna Edmond Becquered (بيكريل إدمون( ya fara kirkira amma bai
cimma burinsaba har ya mutu daga baya kuma sai wani baturen Amurka mai
suna (أوهل روسل( a shekara ta 1941 yau kamar shekara tamanin kenan ya daura a
inda aka tsaya har ya kirkiri solar ta farkoa aduniya wanda akayita da sinadarin
silicon kamar wanda muke amfani da ita a yanzu.

Sannan kuma sai kamfanoni suka fara gatsa wajen sake inganta allon sola har
zuwa yanzu ta yadda kullum kara mata karfi da girma da inganci suke yi wanda
yanzu har ankai ga cewa ana tunanin nanda shekara ta dubu biyu da hamsin
2050 za’a kirkiri sola mai akida hasken wata sabanin wanda yanzu yake amfani
da hasken rana domin kamar yadda Alkur’ani mai girma ya tabbatar da cewa ita rana ita take dauke da wuta a jikinta.

amma ita wata babu wuta a jikinta saidai kuma ita wata tanananne kamar batiri wanda take yin caji ta dauki wutanda yake jikin
rana ta rike sai ta dinga baiwa duniya haske da daddare don haka turawa da suka
bincika hakan suka gane sai sukace to ya kamata a saukar da wannan wutanda
wata take Tarawa a cikinta take rikewa zuwa duniya don kowa ya amfana
domin sukace wutanda wata take Tarawa a jikinta in aka saukar kasa zata ishe
dukkan mutanen duniya hart a rage saboda yawanta domin Allah kadai yasan
cajinda take yi a jikin rana saboda tana kusa da rana domin sukace dalilinda
yasa zasu saukar da wannan wutan kuma shine nanda 2050 za’a samu mutae
kamar billion goma a doran kasa sannan kayan wuta zai yi yawa don haka ana
bukata a samu wani wuta mai karfi mara karewa ko yankewa sai suka ga cewa
ba inda za’ samu wannan wutan sai a jikin wata.

To na san wasu daga cikin masu karatu zasu iya karyata wannan yunkurin na
turawa amma abin ba abin mamaki bane saboda ilimine su kuma kullum bincike
sukeyi don haka inkai malamain islamiyyane mai daskararren kokolwa ko kuma  dan bana bakwai mai yini akan benci to sai kaje kayi karatu domin abin ilimine.

Sai mun hadu a rubutu na gaba.

Fasahar zamani
www.bintubetv.com.ng

[FASAHAR ZAMANI] CIKEKKEN BAYANI A KAN DUNIYAR SOLA (SOLAR SYSTEM ).Gabatarwa cikin littafin Duniyar sola part 1. (b)

                           بسم الرحمن الر حيم

Dukkan yabo da godiy sun tabbata ga Allah wanda yace shine Allah wanda ya
halitta muku abinda yake bayan kasa gaba daya (don amfaninku).

Tsira da amincin Allah su kara tabtta ga manzon Tsira Annabi S.A.W. wanda
yace mumini mai kwazo yafi mumini mara kwazo amma dukkansu akwai
Alkhairi a tare dasu.

Bayan haka duba da wannan ayar da hadisinda muka kawo a sama nake so in
dan yunkura in sanar da dalubanmu na wannan makaranta ta A’isha ta haddar
Alkur’ani da darussan musulunci abinda Allah ya sanar dani game da wani
ilimi mai muhimmanci a wannan zamanin wato ilimin sola domin ya amfani
dalubai musammanma kuma wadanda suke dafda kammala makaranta kamar
yadda a baya mun yi wata kwaryakwaryar littafi akan ilimim komfiuta a
wannan makarantar tamu a bangaren shawakat Computer Institute yau kuma
zan rubuta wannan kwarya-kwaryar littafin akan ilimin sola a bangaren
shawakat solar and inverter institute.

Bakakin kalmomi
A cikin wannan littafin zamuyi amfani da wasu kalmomi wadanda basu da
fassara a hausa saidai mu kotanta saboda asalin sunayene na girkawa ko
faransawa wanda kuma yana da muhimmanci mai karatu ya sansu in kuma
dama mai karatu yana da ilimin kayan wuta to shekenan daga an fada zai
fahimcesu ga kuma kalmomin kamar haka da kuma:-

1. Voltage جهد karfin aiki
2. Amp ارٌت karfin jurewa
3. Watt واط karfin wuta
4. Positive موجب mai wuta
5. Negative سالب mara wuta
6. Parallel التوازي على tsarin sahu
7. Series ًالتوال على tsarin jere
8. Solar cell ةٌشمس ةٌخل kwayan sola
9. Solar module ةٌالشمس اللوحة وحدة allon sola
10. Solar system المركبة اللوحات hadadden sola
11. ac متردد ارٌت wutan nefa
12. dc مستمر ارٌت wutan batir

Amma mai karatu ya sani cewa zan rubuta wannan abinne ba don na iyaba sai
don son amfanarda dalubai da sauran mabukata abinda Allah ya sanar da ni don
haka kar mai karatu ya dogara kawai akan wannan littafin shima ya kamata ya
hada da nasa binciken da kuma kokar don ya cimma burinsa.


Anan  zamu dakata sai a rubutu na gaba.


Fasahar zamani
www.bintubetv.com.ng

GA YADDA ZAKA SETA DOMAIN DINKA AKA BLOGAssalamu alaikum Warahmatullah

Dafatan muna cikin koshin lafiya!¡

Kamar yadda na ambata abaya yau zamuyi batu akan blogger. Da farko bayan mutum ya mallaki domain yaje wurin setting/basic sai ya daura. Zanyi amfani da screenshots kawai.


Cikin screenshot da naturo sama, mutum zai seta *Yes* a duka wuri biyu (2).

Sannan ina kira ga dukkan sabbin bloggers da kar su dami kansu da cike Adsense har sai yagama sanin ka'idojinsu da tsare tsaren su.

Lura da akasarin sabbin budewa sun sani. To hakan a wurin AdSense da wuya su karbi mutum su fara bashi talla alhali baida traffic mai kyau.

 yanzu me ya kama ta blogger yayi to. Sai ya tsaya ya maida hankali wurin cike ciken sharruda, Kama daga na blog har zuwa AdSense.

Amma da yawa basu ma gama settings din cikin blog din daidai ba amma yana harin na AdSense. Sai Ku maida hankali wurin settings da na turo screenshots.

Tin daga :
Page
Settings-Basic
Settings-Post comments and sharing
Settings-search preference.

Wadan nan da yawa bamu mai da hankula kan su. Wadannan sharruda duk bloggers yakamata ya samu ya cike su, domin sun ke banta ne ga blog kawai.

Sannan zamu fadi sharrudan AdSense ma, amma kafun nan sai ta yadda ake creating pages tukunna sai mun had.

#Hadawa Muh'd M. Umar.

AMFANIN BLOG PAGES & YADDA ZAKA MALLAKE TA.Assalamu alaikum warahmatullah.

Yau nazo muku da  bayanin yadda zaku kirkiri pages a shafin Ku na blogspot, kuma in bakkada shafi baza ka karbu ba
Abun da ake nufi da pages a nan su ne.

kamar haka:
Contact us
About us
Privacy policy
Disclaimer.
Ku biyomu wannan a takaice kenan.

Farko kayi sing in a blogger.com
Sai ka shiga page kamar yadda yake a wannan hoto dake kasa.


N

Bayan nan sai ka shiga new page kamar yadda kake gani a wannan hoto.


Wajen title ka rubuta sunan page kamar yadda yake a wannan hoto.
Kasa kuma sai kasanya bayanai na cikin page din
Haka zaka yi tayi kana Publish.

Bude shafi a  blog

Yadda abun yake shine
asan cewa kamar yadda munyi batun game da yadda ake kirkirar pages
A blogger.
A baya munyi bayani yadda ake create din pages din, yanzu kuma zamuyi bayanin yadda zaka fito dasu.

Farko kayi sing in a blogger.com
Sai ka shiga layout kamar yadda yake a Horton nanBayan ya gama loading sai kazabi wajen da kake so pages din su fito a shafin ka misali duba hoton nan

Sai ka zabi pages kamar yadda yake a wannan photo
Zai kai ka zuwa yadda yake a hoton nan na  kasa ¤
To abun da zakayi anan shine duk sai kayi Mack din su.

To anan dakata sai mun hadu a wata gaba Kuma.

#Hadawa Muh'd M. Umar.

YADDA AKE CREATING DIN SITE EMAILS


Yau zamuyi batun yadda creating email din site a blog.

1. Misali idan shafinka bintubetv.com.ng  sai kake so kayi *info@bintubetv.com.ng ko support@bintubetv.com.ng* to sai ka rubuta *info/support* a wuri na farko.

A gaban zaka ga domain dinka kamar yadda kuke gani a wannan hoton ¤

2. Wuri na biyu sai ka saka password din da kake so mai tsauri ko kuma kawai ka danna *Generate* yayi maka password sai kayi copy ka saka shi akasa, Sai ka danna *create..*Shi kenan ka bude email na web dinka kuma kana da damar bude guda 2.

Sai ka dawo farkon cpanel dinka Ka shiga *Forwarders*
1. Idan misali *info* ka nude sai ka saka *info* a wajen zaka ga domain dinka a kasa.
2. Wuri na biyu da na kewaye kuma sai ka saka email dinka da kake amfani dashi gmail ko wanin sa, daga nan sai ka danna *add forwarder* Shikenan.

*Note*
Abinda kayi a nan shine Duk sanda wani ya tura maka sako ta email dinka info@...  To kai tsaye zai shigo *Email* dinka Kai kuma kayi masa  *reply*.

Idan kuma zaka shiga email na site dinka kai tsaye zaka iya zuwa ta hayar rubuta sunan shafinka misali www.bintubetv.com.ng sai ka kara /webmail.

Misali: www.bintubetv.com.ng/webmail

Sai dai ba lallai yayi maka yadda kake so a waya ba, Kuma waccan hanyar ta farko itace mafi sauki.

Allah yesa mudace.

*#Hadawa Muh'd. M. Umar*.

[FACEBOOK PROMOTION] YADDA TSARA TALLA A KAN FACEBOOK
Assalamu alaikum

Kamar yadda mukace xamuyi bayani akan Yadda ake sanya talla a facebook,

A shawarce
Kada ka shiga link da zan kawo a bayanan ka bari idan an kammala sai kabi step din da zan kawo.

 *Facebook Promotion*

Tsarin facebook promotion tsari ne da zai baiwa mutum damar tallata haja, ta kaya, sanarwa, campaign  da sauransu, idan ya zama kana yin posting a page dinka kana samun mutum 10 suna gani. To shi tsari ne da zai baiwa mutane sama da wannan adadin su kalla, abaya nace dole ka mallaki page domin yin wannan tsarin. Ba'a yin promotion na facebook a account, dole sai ta page.

Misali: akwai wani dan siyasa a Kano *Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa* ni ba'a mazabarsa nake ba amman dole in na hau facebook sai naga tallansa. Sabida a profile dina na cike cewa ni dan Kano ne. Shi kuma ya biya Facebook su tallatawa duk 'yan Kano.


*facebook business account*

Shi facebook business account dole sai mutum yana dashi. Ana bude shi ne a www.business.facebook.com

Zakayi sign up ne da account dinka sannan ka zabi page. Bayanin yadda ake budewa zai zo a kasa. Ina zuwa ina son hada bayanan ne da hoto yadda in mutum ya shiga zaiga yadda zaiyi. Bayan kayi sign up da account dinka. A nan ne zaka tsara tsarin yadda zaka biya facebook kudi.

*Add Payment*

Shine zaka zabi salon biyan su kudin.

*Edit Payments Methods*

 Shine zaka canja ko ka gyara tsarin idan ka zabi biya ta card Katin ya kasance master card, idan katinka (master card) ne kuma baya yi sai kaje bankinka kayi musu bayani.

#Hadawa Muh'd M. Umar

[FACEBOOK PROMOTION] YADDA AKE SAMUN KUDI TA FACEBOOK.

1. Menene Facebook?
Facebook yana daga cikin dandalin tsada zumuntar yanar gizo, wadanda suke bada daman isarda rubutaccen sako ko audio damn video. Sannan ana iya yin kira ta facebook kamar ways kiran kuma ta video ko audio. A burnin facebook yanada mutane biliyan 2 da sama. An kirkiro facebook a shekara ta 2004.

2. Ta Yaya Facebook ke samun kudin shiga?
Facebook tana samun ta hanyayu da dama, daga ciki akoi tallata kayaken daidaikon mutane da kamfananuwa da sauransu.

3. Kasuwancin Facebook.
To shima facebook kamar sauran shafukan internet ne ana kasuwanci da tallace tallace ta neman kudi.
Don haka yakamata mufahimci Abu daya ana wurin gabaki Dayan kasuwanci ko neman kudi a yanar gizo Abu guda ne wato tallane.

4. Shin kaima zaka iya samun kudi da facebook?
Ba wai iya su Mr. Mark ne kadai zasu iya samun kudi da facebook ba.

Misali: Kunga wasu ne sukayi Computer
Wasu ne sukayi Mota, waya
Amman yau mutum nawa ne suke neman kudi dasu?

5. Akan me kake son neman kudi da Facebook?
Abinda yakamata shine mutum ya fara yin nazari

Shin akan me zai nemi kudi ta facebook din?

Yadda MTN ba biyan facebook kudi yake don ka shiga da Data dinsu facebook ba, Haka facebook bazasu taba daukan kudi su baka don kana amfani dasu ba.

Misali:

 Ina sayar da kayan yara Ko ina siyar da man shafawa, Kullum ina samun mutum 5 suna siyan kayana To sai nazo na tallata kayan a facebook zan samu karin mutane, Idan kuma na biya facebook su tallatamin to zan kuma samun karin yawan costumers.

6. Ka samar da shagonka na Facebook. Bayan ka zabi abinda kake son yi akai, To akwai bukatar ka samar da shagonka na kasuwanci.

*Facebook Page* (shafin facebook kenan).
Shima profile akwai yadda ake tsara shi ba wai yadda yake gama gari kowa yake cikewa ba. Amman wannan shima wani karatune mai zaman kansa don haka bashi zamuyi ba yanzo.

Sannan duk mai son neman kudi a facebook akwai yadda ake bukata profile dinsa ya kasance ba irin na gama gari ba.

Page a facebook
Anyi shine domin bada damar tara mutane/mabiya babu adadi. Profile kuma a dokar facebook mutum ne kadai ya halatta ya bude. Kuskure ne kaga mutum ya bude account a facebook da sunan kungiya ko sunan kamfani. A'a page ake budewa domin wannan. Kamar kaine kake da gida, Sai ka fitar da shago ta waje domin ka dinga neman kudi acikinsa, shine misalin page.

To kana bukatar ka samar da page na sana'arka, wanda bashi da page zai iya dubawa sharfad.com akwai bayanin yadda ake budewa.

7. Ka gina mabiyanka

 Idan ina siyar da Kayan maza na matasa, To sai nayi kokarin fans dina duk su zama mazan. Ba ina siyar da takalman maza kuma naje nayi adding din mata ba.

Ka dinga kula duk wanda baya motsi ka cire shi daga fans dinka. Facebook ba yawan friend ake so ba, musamman a account na neman kudi. Shi fans masu rai/amfani ake bukata.

8. Rubutun Talla.
Ana son ka tsara rubutu mai kyau na tallan kayanka kuma a takaice ba'a son yayi tsayi, Kayi amfani da salo na jan hankalin jama'a.

9. Hotunan Talla.
Yana da kyau ka samu hotuna masu kyau yayin sanya tallanka, idan kana saida takalma to kayi musu hoto mai kyau Su fito.

Zamu dakata a nan sai mun hado a rubutu na gaba.

#Hadawa Muh'd M. Umar. 
Fasahar Zamani.

[Wata sabowa] Kunji kalamin Dr. Gumi Kuwa!!!

o


Kâji Yadda Ake Tofa Albarkacin Baka. Fadin Malam Ba Haushe Rikicin Duniya Da Mai Ake Yi.

Daga: Dr.Mansur Sokoto
Assalamu Alaikum
Yan uwa ina yi mana fatar alheri.
Na samu wani audio na kanenmu dan uwa Dr. Rabi'u Umar Rijiyar Lemu inda ya yi nasiha kyakkyawa ga Dr. Ahmad Gummi bisa zarmiya da ya yi da rashin ladabi ga Manzonmu Annabi Muhammad sallallahu alaihi wasallam.
Nasihar ta yi kyau matuka kuma a cikin mutuntawar da ta dace. Ina son yan uwa su saurari wannan audio kuma su karanta abinda Sheikh Muhd. Awwal Nuhu ya rubuta domin kauce ma fadawa cikin irin wancan hali da Dr Gummi ya shiga. Kuma duk da yake Dr Gummi ya saba sakin maganganu na rashin ladabi ga mutane masu daraja da yi masu izgili a wannan karon WALLAHI ina fatar ya ja da baya, ya yi istigfari domin Allah mai gafara ne, kuma maganar ta yi girma sosai.
Ga dai rubutun Sheikh Awwal nan kamar yadda na kwafo daga shafinsa tare dan karamin gyara na kurakuran rubutu 👇

*HADISIN RUBUTUN MANZON ALLAH S.A.W YAYIN RASHIN LAFIYARSA:*
✍ Muhd. Awwal Nuhu

NEMAN UZURI: 
1- Ina neman afuwar `yan uwa na ce zan yi rubutu a kan wannan hadisi tun shekaranjiya Asabar amma ban samu dama ba sai yau.
2- Ina neman afuwa game da tsawaita rubutun, ban cika son yin rubutu mai tsawo ba, sai dai wannan ya zama dole, saboda da shi ne za a fahimci yadda lamarin yake. Da fatar za a yi hakurin karantawa gaba daya.

________
Kamar yadda muka sani a `yan kwanakin nan an samu ce-ce-ku-ce sakamakon wata magana da Dr Ahmad Gumi ya yi game da hadisin Abdullahi dan Abbass da yake cikin Bukhari da Muslim cewa Manzon Allah s.a.w ya nemi a kawo takarda ya yi rubutu, amma su Umar r.a suka ga cewa ba sai an yi rubutun ba kuma hakan ya tabbata ba a yi rubutun ba.

Dr Gumi ya fassara wannan hadisin da fassarar da ta sabawa fahimtar daukacin Ahlus sunnah na da da na yanzu. A cewarsa, Manzon Allah s.a.w ya yi umarnin abin da ya sabawa shari`a sai sahabbai suka ce ba za a yi ba (wal iyazu billah).
A gefe daya kuma `yan Shi`a sun samu abin da suke bukata cewa su Umar r.a sun hana a rubuta wasiyya ga Aliyu r.a, sai suka dauki wannan magana suka yi ta yayata ta tare da sakin gurbatattun harsunansu a kan Khalifa Umar r.a da sauran sahabbai.

Don haka dole ne a yi bayani da zai warkar in sha`allahu ya kuma warware shubhohin duka bangarorin biyu da suka kaucewa daidai game da wannan abin da ya faru.

- Yana daga cikin ka`idojin fahimtar fikhun da ke cikin hadisi, ka hada hanyoyin hadisi waje daya (ma`ana ka tattara riwayoyinsa waje daya don da haka ne abin da bai bayyana a wata riwaya ba zai bayyana a wata).

- Kamar yadda sai ka tattara hadisai da suke da alaka da juna game da wani hukunci ko wani lamari sannan za ka fahimci inda wannan hukunci ko al`amari ya dosa.
Wannan ita ce ka`idar da za mu yi anfani da ita wajen fahimtar hadisin Ibnu Abbas wanda ya ce: Manzon Allah s.a.w ya nemi a kawo abin rubutu ya yi rubutu yayin da yake kwance ba shi da lafiya, amma su Umar r.a. suka ga cewa ba sai an yi wannan rubutu ba.
___________

YANA DA KYAU MU SAN WASU UBUBUWA GUDA HUDU KAFIN MU FARA MAGANA A KAN HADISIN.

1- Annabi s.a.w ya yi tsawon kwana goma sha biyu 12 ( a wata riwayar sha hudu 14) yana rashin lafiya kafin Allah ya karbi rayuwarsa.

2- lamarin da ya faru a hadisin Ibnu Abbas na neman yin rubutu ya faru ne a ranar Alhamis a yini na takwas da fara jinyar Manzon Allah s.a.w

3- wannan lamari ba shi ne na farko ba, tun ranar da Manzon Allah s.a.w ya fara rashin lafiya ya so ya yi rubutu, amma sai wani dalili ya hana shi.

4- Manzon Allah s.a.w ya rayu bayan wannan lamarin na neman a rubuta takardar tsawon kwana hudu a duniya (daga ranar Alhamis zuwa ranar litinin, sannan Allah ya karbi rayuwarsa a hantsin ranar litinin).
________

BAYANIN YADDA LAMARIN YAKE:

1- Kamar yadda ya gabata Manzon Allah s.a.w ya fara rashin lafiya ne a ranar Alhamis kwana 12 kafin cikawarsa. Kamar yadda ya tabbata a Hadisi ingatacce wanda Bukhari da Muslim suka ruwaito, daga Ummul Mu`uminina A`isha r.a:
عن عائشة، قالت: دخل علي رسول الله صلى الله عليه وسلم في اليوم الذي بدئ فيه، فقلت: وارأساه فقال: «وددت أن ذلك كان وأنا حي فهيأتك ودفنتك» . قلت غيرى: كأني بك في ذلك اليوم عروسا فيه ببعض نسائك، فقال: " بل أنا وارأساه , ادعي لي أباك وأخاك حتى أكتب لأبي بكر كتابا، فإني أخاف أن يقول قائل ويتمنى ويقول: أنا أولى، ويأبى الله والمؤمنون إلا أبا بكر ". رواه مسلم في الصحيح , عن عبيد الله بن سعيد , عن يزيد بن هارون، وقال في الحديث: " فإني أخاف أن يتمنى متمن ويقول قائل: أنا أولى ويأبى الله والمؤمنون إلا أبا بكر
وفي رواية البخاري: لقد هممت، أو أردت أن أرسل إلى أبي بكر وابنه فأعهد أن يقول القائلون أو يتمنى المتمنون» فقلت: يأبى الله ويدفع المؤمنون أو يدفع الله ويأبى المؤمنون
A`isha r.a ta ce: Manzon Allah s.a.w ya shigo wajena ranar da ya fara rashin lafiya, (ya same ni ni ma kaina yana ciwo) sai na ce: "wayyo kaina" sai ya ce: "Ni ne dai zan ce wayyo kaina" …. Ya ce: na yi niyyar in sa a kirawo min Abubakar (Assidik) da dansa (Abdurrahman) don in rubuta wa Abubakar takarda (da za ta tabbatar masa da khalifanci a bayana) don kada wani ya sa ran shi zai shugabanci al`umma, ko wani daga baya ya zo ya ce ya fi shi cancanta, sai kuma na ce: (Ai ba sai an rubuta ba) Allah s.w.t da Muminai ba za su yarda da kowa ba sai Abubakar.

Haka dai ya ci gaba da rashin lafiya, har zuwa lokacin da ya fara ishara ga sahabbai cewa ajalinsa ya zo, ya kuma fara nuna musu cewa Abubakar shine khalifarsa bayansa, inda ya yi khuduba yana mai cewa:
«إن عبدا خيره ربه بين الدنيا والآخرة فاختار ما عند ربه»، ففطن أبو بكر أنه يريد نفسه فبكى، فقال له النبي صلى الله عليه وسلم: «على رسلك»، ثم قال: «سدوا هذه الأبواب الشوارع في المسجد إلا باب أبي بكر رحمه الله، فإني لا أعلم رجلا أحسن يدا عندي من الصحابة من أبي بكر»
Ya ce: "Akwai wani bawa da Allah ya ba shi za6i tsakanin Duniya da Lahira, sai ya za6i abin da ke wajen Ubangijinsa".
Sai Abubakar (shi kadai) ya gane abin da Manzon Allah s.a.w yake nufi (na gabatowar ajalinsa) sai ya fashe da kuka.
Sai Manzon Allah s.a.w ya rarrashe shi ya ce masa "bi sannu". Sannan sai Manzon Allah s.a.w ya ce: ku toshe wadannan kofofin da suke zuwa ga masallaci, sai kofar Abubakar kadai za a bari (yana nufin kofofin da suka bubbude na gidajensu masu kallon masallaci, don su samu saukin shigowa masallaci)….

Haka aka ci gaba har aka kai ga wata rana ciwo ya tsananta ga Manzon Allah s.a.w ta yadda ba zai iya fita sallah masallaci ba sai ya ba da umarni a sanya wani ya jagoranci sallah.
عن عبد الله بن زمعة، قال: لما استعز برسول الله صلى الله عليه وسلم وأنا عنده في نفر من المسلمين دعاه بلال إلى الصلاة فقال: «مروا من يصلي للناس» فخرج عبد الله بن زمعة فإذا عمر في الناس، وكان أبو بكر غائبا، فقلت: يا عمر قم فصل بالناس، فتقدم فكبر، فلما سمع رسول الله صلى الله عليه وسلم صوته وكان عمر رجلا مجهرا، قال: «فأين أبو بكر؟ يأبى الله ذلك والمسلمون، يأبى الله ذلك والمسلمون» فبعث إلى أبي بكر فجاء بعد أن صلى عمر تلك الصلاة فصلى بالناس
Abdullahi bnu Zam`ah ya ce: yayin da jikin Manzon Allah s.a.w ya yi tsanani ina wajansa, sai ga Bilal ya zo ya kira shi zuwa ga sallah. Sai Manzon Allah s.a.w ya ce: "ku Umarci wani ya ja mutane sallah" sai Abdullahi bnu Zam`ah ya fita, sai ya ga Umar cikin mutane a lokacin Abubakar ba ya nan, sai na ce (inji ibnu zam`ah) ya Umar tashi ka ja mutane sallah. Sai Umar ya shiga gaba ya yi kabbara.

Yayin da Manzon Allah s.a.w ya jiyo muryar Umar sai ya ce: "Ina Abubakar ya ke? Allah da musulmai sun ki (wani ya yi shugabanci a wannan lokaci) sai Abubakar", daga nan sai Abubakar ya zo ya ci gaba da jan mutane sallah.

Haka abu ya ci gaba har zuwa wata Alhamis ta zagayo yini na takwas Manzon Allah s.a.w jiki ya ki dadi kuma wannan magana dai ta rubutu game da kalifancin Abubakar na ransa don gudun kada rai ya yi halinsa wasu su zo suna jayayya da Abubakar.
Dan haka sai Manzon Allah s.a.w ya sake tayar da waccan magana da ya yi tun farkon rashin lafiyarsa, ya sake cewa 
ائتوني بكتاب أكتب لكم كتابا لا تضلوا بعده
"Ku kawo abin rubutu in rubuta muku wani rubutu da ba za ku bata ba bayansa"
Ya yi wannan magana a gaban sahabbai da dama da suka zo duba shi, har da Umar a cikinsu, kuma yanayin jikinsa da Umar ya gani da yadda yake fama da rashin lafiya ya sa Umar din ya tausaya masa yake ganin bai kamata a dora masa nauyin shiftar rubutun ba. A maimakon haka a bar shi ya huta ya samu saukin tsananin rashin lafiyar da yake fama da shi, don haka sai ya ce:
إن النبي صلى الله عليه وسلم غلبه الوجع وعندنا كتاب الله حسبنا
"Lallai ciwo ya tsananta ga Annabi s,a,w (don haka a bar shi ya huta) tun da ga littafin Allah a tare da mu ya ishemu"

Sai dai wasu daga cikin mahalarta wajen ba su da ra`ayi irin na Umar suna ganin a kawo takardar Manzon Allah s.a.w ya rubuta don gudun kar a samu sabani daga baya.
Sai suka fara jayayya wasu na cewa a kawo abin rubutu wasu na cewa a`a.

Da manzon Allah s.a.w ya ga sun fara sabani sai ya yanke hukunci ya ce su tashi su tafi.

Daga nan Manzon Allah s.a.w bai sake tayar da maganar ba saboda natsuwar da yake da ita cewa Allah ba zai ba wa wani damar kwace wa Abubakar wannan matsayi ba, kuma musulmai ma ba za su yarda da wani ba matukar Abubakar na cikinsu, (kamar dai yadda ya yi ta maimaitawa a baya).
Haka Manzon Allah s.a.w ya ci gaba da jinya tsawon kwana hudu bayan wannan abin da ya faru.

Bai sake tayar da maganar ba, musamman saboda karin nutsuwar da ya samu ganin cewa Abubakar shi ya ci gaba da jagorantar mutane sallah a sauran kwanakin da yake kwance, abin da ke nuna alamar ba wani mai jayayya da shugabancinsa, har Allah ya karbi rayuwar Manzon Allah s.a.w a ranar litinin bayan kwana hudu da faruwar wannan lamari. Sallallahu Alaihi Wasallam.

ABABEN LURA:
_____________
1- Abin da Manzon Allah s.a.w ya so a rubuta shi kuma Umar r.a ya nemi a saukaka masa ba sai an rubuta ba, abu ne a fili kowa ya san shi, don haka yin rubutun ba wajibi ba ne, kawai dai zai kara karfafa wa ne don kar a samu sabani daga baya, shi ya sa ma da Manzon Allah s.a.w ya ga sun fara sabani wasu su ce a rubuta wasu su ce a`a sai ya zabi a bari ba sai an rubuta ba ya ce: su tashi su tafi.

2- Abin da ya so a rubuta ya tabbata an aiwatar da shi a aikace wato Abubakar Assiddik shi ne ya zama khalifa bayansa, da wannan za mu fahimci ashe BA WANI ABU MANZON ALLAH YA CE A RUBUTA WANDA YA SABAWA SHARI`A KAMAR YADDA DR GUMI YA RIYA BA.

3- babu wata madogara ga `yan shi`a da za su soki Umar r.a cikin wannan hadisin domin abin da Manzon Allah ya so a rubuta a fili yake kuma an aiwatar da shi ko ba a rubuta ba.

ALLAH KA GANAR DA MU GASKIYA KA BA MU IKON BIN TA KA KUMA GANAR DA MU KARYA KA BAMU IKON GUJE MATA.

Yadda Ake Wasa Links Mai Photo A WhatsappBa Sai Kanadashi BaWato ko bakada whatsapp a theme dinka zaka iya sharing links a whatsapp.

Tayaya?

Hmm smile, Mal. abun dabara ne kawai wlh links din zaka kwasu su zuwa whatsapp.

In ka dauko ka ajiyeshi a gefe sannan Kai forwarding dinshi inda kake so, ko Kuma kana pasting dinshi kabarshi yayi loading din hoton sannan Kai posting.
Wannan kenan a takaice.

Yadda Abun Yake Shine :

Idan kashiga shafin da kakeso kayi share
Ka copy address din shafin
Sai kayi pasting a group
Example

1.  Shiga browser ka kabude shafin dakakeso kayi share a WhatsApp
2. Danna kan address din  browser sannan kayi copy
3.  Jeka cikin WhatsApp dinka.  Inda kakeso katura link din.  Sai kadanne hannunka awajan, zakaga *paste* yafito
4. Kadanna paste din address din xefito.
Amma zakaga Bai kawo hotoba.  Kadan bada space ko kadan jira yayi din hoton da kanshi. 

To da alamun zamu kwana anan sai jiko nagaba Insha-Allah.

Fasahar Zamani.

WATA SABOWA KUNGA YADDA AKAYI KACAKACA DA AL-ADUN ALME A JIHAR KANO.
DOKOKIN AURE A DANBATTA, JIHAR KANO

A Karamar Hukumar Danbatta Dake Jihar Kano,
Sarkin Ban Kano Hakimin Danbatta Alhaji Dr.

Muktar Adnan Ya Kaddamar Da Dokokin Aure A
Fadar Shi Dake Garin Na Danbatta A Aranar
2/1/2017 Wanda Mataimakin Shugaban
Kwamitin Alh Ado Muhammed Ya Karanta
Kamar Haka:
Mutanen Danbatta A bisa Jagorancin Sarkin Ban
Kano Hakimin Danbatta Alhaji Dr. Muktar
Adnan, Shugaban Karamar Hukumar Danbatta,
Magadai, Masu Unguwanni, Dattawa Da Sauran
Matasa Maza Da Mata Sun yarda Sun Amince
Da Kudin Dokokin Aure Kamar Haka Don Rage
Yawan Al'adun Wajen Yin Aure.

KASHI NA 1 KUNDIN AURE /BAIKO.
1. Daga Dubu Goma Zuwa Ashirin.
2. Mutum Biyu Za a Aiko Yayin Sa Baiko.
3. Bayan An biya Kuma Iyayen Budurwa Sun
Amince, Ba a yarda A Kara Dora Wata Hidima
Akan Angina.
4. Ba Yarda Wani Ya Nemi Budurwar Da Akaiwa
Baiko Ba.
5. Idan Aka Kama Wani Ya Karya Wannan Doka
Za Hukunta Shi Ta Hanyar Zama Gidan Maza Ko
Biyan Tarar Kudi Adadin Kudin Baiko A gaban
Kuliya.
Allah Yasa Muma

SHARFADI YAYI FINTINKAU GA SAURAN MATASA A DUNIYAR SOCIAL MEDIA.

Basheer Journalist Sharfadi

Matashine wanda ya bada Rayuwarsa a Bangaren Taimakawa Matasa yadda Akeyin Amfani da kafofin sadarwa na Yanar Gizo, Tare da wayar dakan matasa akan Dogaro dakai,
   Yana samar da wani tsari inda yayi masa suna Online Make Money Ma'ana Hanyoyin Samu kudi ta Yanar Guzo.
   Ya Taba hada gidan radio a lokacin yana Makaranta Secondary Tare da wasu abubuwan na Kimiyya da Fasaha Daga Cikin harda Saitin Majigi.
   Wani matashi da muka tattauna da shi ya bayyana mana cewa sunyi makaranta kuma Aji daya Tare da Basheer Journalist Sharfadi inda yace shine ya Rike mukamin monitor a Ajinsu, Matashin ya Wata katafariyar Makaranta wadda babu irinta a Fadin Diniya wacce zata Dinga Bada Darusa cikin Harshen Hausa.
  A kullum kokari yake wajen baje Kolin Basirarsa da Allah ya Bashi domin Sauran Al-umma su Amfana.
   Yayi Aiki da wani Hadisi wanda Annabi (s.a.w) yace Duk wanda Allah ya Bashi wani ilmi bai sanar dashiba To Allah zai masa Linzami dashi Ranar Al-kiyama.
  Basheer yana kokari wajen Sauke wannan Nauyi da Allah ya bashi,  A yanzu dai shine Matashi na Farko a Arewacin Nigeria da Tauraruwarsa take Haskawa a Fannin yanar Gizo.

   Dafatan Sauran Matasa zasuyi koyi da kokari irin na wannan matsahi Basheer Journalist Sharfadi.

Umar Abdullahi Zango 📝

SIFFAR SALLAR ANNABIR RAHMAH
      _*LITTAFIN BAYANIN SALLAH*_
     ➖➖➖➖➖➖➖➖

_Da Sunan *Allah* Mai *Rahma* Mai *Jinqai*_

          ```BABIN SIFFAR SALLAH```
            ➖➖➖➖➖➖➖

_285. An Kar6o Daga *Abi-Humaid As-Sa'adi (ra)* Yace: “Naga *Manzon Allah (ﷺ)* Idan Zaiyi Kabbar Yana Sanya Hannunsa Daidai da Kafadarsa, Idan Zaiyi Ruku'u Sai Ya Sanya Hannunsa Akan Gwiwarsa, Sannan Ya Miqar da Bayansa, Idan Ya Dago daga Ruku'u Kuma Yana Daidaita Har Kowace Ga6a ta Koma Wurinta. Idan Yayi Sujjada Yana Aje Hannunsa Ba Tare da Shimfidasu ba Kuma Bai Dunkulesu ba, Ya Fuskantar da Manyan Yatsun Kafarsa Su Kalli Alqibla. Idan Ya Zauna a Cikin Raka'a Biyu, Yana Zama a  Kafarsa ta Hagu Sai Ya Kafe ta Damar; Idan Kuma Ya Zauna a Raka'ar Karshe (Zaman Tahiyar Karshe), Yana Gabatar da Kafarsa ta Hagu Sai Ya Kafe Dayar Kafar, Sannan Ya Zauna a Mazauninsa”. *(Bukhari)*._

_286. An Kar6o Daga *Aliyu bn Abi-Dalib (ra)*, Daga *Manzon Allah (ﷺ)*, Lallai Ya Kasance Idan Yazo Yin Sallah Yana Cewa: *“Wajjahtu Wajhi Lillazi Fadaras Samãwati Wal Ardi”*. Har Zuwa Fadinsa: *“Minal Muslimin, Allãhumma Antal Maliku Lã'ilaha Illã Anta, Anta Rabbi Wa Ana Abduka”.* Har Zuwa Karshensa. (Muslim Ya Ruwaitoshi). A Cikin Wata Ruwayar Tace: “Yana Karanta Addu'ar ne a Cikin Sallar Dare”._

_287. An Kar6o Daga *Abi-Hurairah (ra)* Yace: *Manzon Allah (ﷺ)* Ya Kasance Idan Yayi Kabbarar Harama Yanayin Shiru Kadan Kafin Ya Fara Karatu, Sai Na Tambayeshi (Abinda Yake Fadi Idan Yayi Shirun), Sai Yace Ina Cewa Ne: *“Allãhumma Bã'id Baini Wa Baina Khadãyãya Kamã Bã'adta Bainal Mashriqi Wal Magribi, Allãhumma Naqqini Min Khadãyãya Kama Yunaqqath Thaubul Abyadu Minad Danas, Allãhummag Silni Min Khadãyãya Bil Mã'i Wath Thalju Wal Baradi”*. (Bukhari da Muslim)._

_288. An Kar6o Daga *Umar (ra)* Lallai Ya Kasance Yana Cewa: *“Subhãnakallahumma Wabi Hamdika, Wa Tabãrakas Muka, Wa Ta'ala Jadduka, Wa Lã'ilãha Ghairuka”*. (Muslim Ya Ruwaitoshi da Sanadi Yankakke "Sanadin Bekai ga Umar din ba")._

_289. An Ruwaito Kwatankwacinsa Daga *Abi-Sa'eedi Khudry (ra)* Marfu'an (da Sanadi Zuwa ga *Manzon Allah (ﷺ)*) Ya Kasance Yana Fadi Bayan Yayi Kabbarar Harama: *“A'uzu Billahi Sami'il Aleem Mminash Shaidanir Rajeem, Min Hamzihi Wa Nafkhihi Wa Nafthihi”*._

_Anan Zan Dakata Sai Mun Hadu a Darasi Na Gaba_

_*✍🏽Sulyman Yahya*_


DALILAN SHAYAR DA JARIRI A QUR'ANANCE
*DAKE AKE GLOBAL*🌹


SHAYARWA
 Al-Kur’ani mai girma ya nuna mana cewa, “Iyaye mata zasu shayar da jariransu shekara biyu cikakku ga wanda ke son cikakkiyar shayarwa (Bakara: 233).

Ke, me zai sa ki bar ‘ya’yanki a hannun mai raino tana basu madara kullum, ki sha magani ruwan nononki ya kafe?!

Ai shayarwa ita ce cikar mace uwa, ita ce tushen kauna da bege tsakanin yaro da mahaifiyarsa. Bayan haka kuma, nonon uwa shi ke dauke da magungunan jarirai wadanda babu irinsu a kowanne asibiti.
❤❤💋❤💋❤💋❤❤


IDAN MUN GINTSE KARATUN YAU ANAN, ABINDA YA FI SHI NAGARTA DA AMFANARWA YANA NAN TAFE A MAKO MAI KAMAWA IN SHA ALLAH.

YAU MUNA TAFE DA YADDA MULUNCI YAYI BAKON HAMZA BAFFAN MONXO (R. A)*_Assalamu Alaikum_*
*
*_22/04/1440,_* _Lahadi._
*_30/12/2018,_* _Lahadi._
*
*ALKÃKI DA RUWAN ZUMA*
_Ingantaccen Tarihin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi wa Sallama Daga Haifuwa Zuwa Jana’iza._
-
*Wallafar:*
_Muhammad Mansur Ibrahim Cibiyar Nazarin Addinin Musulunci Ta Jami'ar Usmanu Ɗan Fodiyo, Sakkwato_
-
*DARASI NA [111]*
*_____________*
-
*_•┈┈┈┈•﷽•┈┈┈┈•_*
-
*3.17  Yanayi ya  Canja  a Makka, 'Ƴan  Gudun Hijira Sun Dawo:*
-
_Bayan  tafiyar  wannan  ayari  na  farko  da  muke  magana  a  kansa, kwatsam  sai  aka  samu  sassafcin  yanayi  a  birnin  Makka._
-
_Domin  kuwa jarumawa  biyu  daga  cikin  waɗanda  ake  tsoro  Allah  ya  karkato  da  zuƙatansu sun  karɓi  Musulunci._
-
_Sune;  Sayyidi  Hamza  -  baffan  Manzon  Allah  -  da Sayyidi  Umar  dan  khaɗɗabi._
-
_Don  haka  ala-tilas  aka  fara  sakar  ma  musulmi mara,  har  ma  ya  kasance  a  yanzu  suna  sallah  a  fili  a  cikin  masallaci._
-
_Jin wannan  sauyi  da  aka  samu  sai  ayarin  Usmanu  ɗan  Affana bayan  watanni  uku da suka share a  can  suka juyo  suka  dawo gida, amma  kuma  tsugunnen dai  ba ta  ƙare  ba._
-
_Zamu  yi  magana  a  kan  musuluntar  waɗannan  jarumawa  da  muka faɗa,  sannan  mu  koma  kan  abin  da  ya  sake  tilasta  yin  hijira  ta  biyu  zuwa Habasha._
-
*3.18  Musulunci  ya Samu Garkuwa*
-
_Bayan  tafiyar  Muhajirai  na  farko  su  goma  sha  huɗu  babu  abinda mushrikai  suka  ƙara  a  kan  musulmi  sai  ta'addanci  da  ƙetare  iyaka._
-
_A  cikin haka  ne  Wata  rana  Abu  Jahali  ya  tafka  irin  ta'asar  tasa;  ya  kalli  ƙwayar  idon Manzon  Allah  Sallallahu  Alaihi  wa  Sallama ya  zage  shi,  kuma  yayi  masa izgili,  yayi  ƙoƙarin  muzanta  shi._
-
_Fiyayyen  halitta  wanda  yafi  kowa  hakuri  ya shuɗe  abin  sa  bai  ce  masa  uffan  ba._
-
_Ashe  duk  abin  nan  da  ke  faruwa  a  bisa kunnen wata kuyanga 'ƴar  gidan  Abdullahi  ɗan  Jud'an, (290) sai wannan kuyanga ta  kwashe  labarin  duk  abinda  ya faru  ta  faɗa  ma  Hamza,  wanda  yake  baffan Manzon  Allah  ne  kuma  abokin  rainonsa,  tun  da  yake  nonon  da  Hamza  ya  saki shi  Manzon  Allah  ya  kama._
-
_Hamza  yace  mata,  tsakaninki  da  Allah  a  gabanki aka  yi  haka?  Ta  ce,  ƙwarai  kuwa._
-
_Nan  take  jinin  Hashimawa  ya  motsa  a  cikin jikinsa,  kasa  ta  kasa  ɗaukar  qafafunsa, bai  zarce  ko  ina  ba  sai  majalisin  kafirai in  da  Abu  Jahali  yake  baje  kolinsa._
-
_Da  isar  Hamza,  ga  shi  saurayi  mai  ƙarfi, kuma  mafi  kwarjinin  samarin  Makka, bai  tsaya  wani  dogon  bahasi  ba  sai  ya cira  bakarsa  ya  watsa  ta  a  kan  Abu  Jahali  sai  da  ya  yi  ma  sa  mummunan  rauni, sannan ya ce, ya  za ka  zage  Muhammadu  ina  a  kan addininsa?! Allahu  Akbar._
-
_A  lokacin  da  Hamza  ya  furta  wannan  kalami  bai  ƙudure a  zuci  abin  da  ya  faɗi  da  baki  ba, amma  kuma  ko  da  ya  dawo  hayyacinsa bayan  fushi  ya  sake  shi,  sai  ya  sake  nazarin  abin  da  ya  faɗa._
-
_To,  mene  ne  illa idan  na  bi  addinin  Muhammadu  amintacce  wanda  na  tabbata  Allah  ya  aiko  shi, ba  ƙarya  yake  yi  ba?  Wannan  duka  mai  zafi  da  Abu  Jahali  ya  sha  wata-ƙila  shi ne  karo  na  farko  da  ya  fara  samun  irin  sa._
-
_Abin  da  ya  sa  da  rikici  ya  ɓarke  a tsakanin  danginsu  biyu,  yace  ku  dakata, Wallahi  nine  na  jawo  jidali,  don  na ci mutuncin  ɗan yayansa. (291)_
-
_Labarin  dukan  da  Abu  Jahali  ya  sha  a  hannun  Hamza  ya  rinƙa  yaɗuwa a  cikin  jama'a,  yana  tafiya  kafaɗa  da  kafaɗa  da  labarin  musuluntar  sa, wannan shine ya  kashe  jikin  Quraishawa  matuƙa._
-
_Kwana  uku  bayan  haka,  sai  kuma  suka  ji Umar ɗan Khaɗɗabii shi  ma ya musulunta._
-
*===============*
_Muhammad bn Umar_
*
DAGA
Zauren *Islamic Ummah*
*

ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ،ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ ﺃﺳﻨﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ
Hey, we've just launched a new custom color Blogger template. You'll like it - https://t.co/quGl87I2PZ
Join Our Newsletter