001-234-567-8910

5th Avenue Madson, NY758, USA

Get Update on our recent Gadgets & Tabs

Add this

Add this

Web Design Agency Nigeria https://www.ads54.com/ad/a/10595_4daf76b52369930

Add this

Website Value Calculator - Domain Worth Estimator - Buy Website For Sales

Add This

[FARKON DAREN QABARI]
➖NA KASASHI GIDA 7⃣

1⃣➖MUQADDIMA‼
   Yaku bayin ALLAH! Mutuwa hakikace da kowa zai kwankwadeta, Rayuwa kuma kasuwace ta sayan guzuri na alhairi ko sharri, Mai hankali shine wanda yayi aiki mai kyau don lahirarsa, yarabu da duniya da karancin nauyin zunubi,

2⃣➖TATTALI‼
   Yaku bayin ALLAH! Lalle ambaton mutuwa da QABARI da firgicenta yasa Malamai da masu taqawa kuka musammanma yayinda suka tunada DARENSU NA FARKO cikin QABARI da kadaici da canjin halayya kuma da kaucewa mummunar makoma, shiyasa suka gaggauta ayyuka nakwarai don samun kyakkyawar makoma,

3⃣➖FARKON DARENKA DA ALLAH‼
   Farkon DARENKA da ALLAH shine a QABARI, dare biyune ke zama a tunanin mutum= ¹ darenda kake gidanka tareda iyalanka da yaranka da dangi kuna kallo da ciye ciye cikin ni'imar rayuwa da dariya da walwala, ² darenda yabiyo wannan daren kwatsam mutuwa ya daukaka an bizneka a QABARI, Farkon lokaci Farkon darenka aciki๐Ÿ˜ข, YACE๐Ÿ‘‰
 HMMMMMMMM! nabar wuri zuwa wani wuri❗natafi daga wurin kwanciyana adakina zuwa wani daki daban❗barci ya kauracewa idona, ALLAHU AKBAR❗ya DAREN FARKO zai kasance mana a QABARI⁉yayinda za'a sanya mutum daga shi ba komai sai aikinsa, ba mata❗ba yaro❗ba abokin sana'a ko na hira,
๐Ÿ’กALLAH SW yace <<sa'annan za'a mayar dasu ga ALLAH majibincinsu na gaskiya >> {SRT AN'AM=62}

4⃣➖FARKON DARE A QABARI‼
   FARKON DARE A QABARI- yasa mutane dayawa kuka- malamai da mahukunta, mawaka dayawa sun wake alhininta, an wallafa dimbin littafai akansa,
ALLAHU AKBAR❗shine ranarda katifa da filonka kasake! Slin shine itatuwa ko tukwane! Rufi shine kasa! Mayafi shine likkafani! Zai tattauna da muhawara Munkarun da Nakirun,

5⃣➖MAMACI BAZAI DAWOBA DUK NACI‼
 ◼Anzo da wani bawan ALLAH salihi wanda yake cikin magagin mutuwa sakamakon cizonda maciji yayi masa lokacinda yafita bulaguro kuma ya manta baiyi sallama da iyayensaba- numfashinsa sama sama yana cewa= yaya zan rabu da 'ya'yana akaramin lokaci haka batareda na gansuba⁉banfa yi sallama da iyayenaba⁉haka rayuwa zata mini tasa sabani tsakaninmu⁉haka zan rabu da dukkan dukiyata akaramin lokaci⁉ZUWA QABARI gidan kadaici⁉
YA kai miskini irina➖shin ka taba tunanin haka ga rayuwarka⁉
 ◼ALHASAN IBN HASAN yayi mutuwar bazata sai matarsa tafita da 'ya'yanta ta buga bukka agefen QABARINSA, don bakin cikin mutuwar tayi rantsuwar ita da 'ya'yanta zasuyi kuka har tsawon shekara anan, da shekarar tacika cikin dare ta tattare bukkar zata tafi tareda 'ya'yanta sai wani tambayar wani batareda tana ganinsuba=
Shin sun sami abinda suka rasa⁉
Sai aka amsa masa= a'a sun yanke tsammani sun koma batareda sun sami abinda suka rasaba, batareda an mayar musu ajiyarsuba‼
‼ALLAHU AKBAR‼nacinsu baisa gawar yayi musu maganaba, bai taba fitowa wurinsa yayi hira dasu koda na dare dayaba, bai sumbaci yaransaba, baiga santaleliyar matarsaba, kunji farkon dare a QABARI‼
   Saidai akwai ranaku alahira, in ya kyautata aiki suma sun kyautata to zasuyi madawwamiyar rayuwa tare a ALJANNA,
๐Ÿ’กALLAH SW yace <<kuma wadanda sukayi Imani kuma zurriyyarsu suka bisu da imani zamu hadasu dasu (cikin ALJANNA) bazamu rage musu komai daga aikinsuba>> {SRT TDUR=21}

6⃣➖UMAR BN ABDIL-AZIZ YANA TUNA FARKON DARENSA A QABARI‼
 ◼Babban Malami IBN ZIYAD yacewa UMAR IBN ABDUL'AZIZ= ya AMEERAL MUMININA- Kafin kahau mulki a MAKKA kana cikin ni'ima da lafiya da walwala, yanzu kuma bayan hawanka mulki me yacanzaka haka ka rame ka kode⁉
 Sai UMAR yace dashi= hmmmmmmmm! Ina tuna farkon shigana QABARINE, yaya zaka ganni aranarda za'a kwabe mini tufafina๐Ÿ˜ข akaini QABARI inyi filo da kasa๐Ÿ˜ข na rabu da masoya๐Ÿ˜ข na bar abokai๐Ÿ˜ข bayan kwanaki 3 in ka ganni cikin QABARIN sai ka firgita๐Ÿ˜ข‼
 ➖Ana Sakai QABARI dan'uwa daga ranar gawarka ta fara kumbura๐Ÿ˜ข kwana kadan idanunka sun zazzaro๐Ÿ˜ข tumbinka ya fashe๐Ÿ˜ข doyi da wari yacika QABARIN๐Ÿ˜ข tsutsa sun lullubeka๐Ÿ˜ข ba kyan gani๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ

7⃣➖RUFEWA‼
   Yaku bayin ALLAH! Munzo karshen hudubar mai taken DARENKA NA FARKO CIKIN QABARI, ina neman kowannenmu yatanadi haskensa don haskaka FARKON DAREN QABARINSA, WALLAHI ba abinda zai haskaka QABARI sai imani da kyawawan ayyuka, mu gabatarwa kanmu abinda zai tayamu hira a QABARI, ranarda za'a rabamu da iyalai da dukiya da 'ya'ya da abokai da motoci da waya da talabijin da kudi da man komai‼
๐Ÿ‘๐Ÿ˜ขYA RABBANA KAHASKAKA MANA QABARINMU! KAWADATAMU ACIKINTA DA ABOKIN HIRA NAGARI ACIKINTA! KABAMU BARCI ACIKINTA, DA ALJANNA IN MUN TASHI DAGA GRETA,
AMEEN.

via๐Ÿ‘‰ Abubakar BN Mustafa Biu✍

TARIHIN MARGAYI ALH. SHEHU SHAGARI A TAKAICE.*LABARAI A TAKAICE*

*Mun samu labarin rasuwar tsohon shugaban Najeriya na farar hula Alhaji Shehu Shagari bayan jinya da ya sha fama da ita. Marigayin wanda shine Turakin Sokoto kuma daya daga manyan jigogin gwamnatin Firimiyan arewa Ahmadu Bello, ya hau mulkin Najeriya bayan dawo da mulki hannun farar hula a 1979 daga gwamnatin mulkin soja ta Olusegun Obasanjo.*

*Jim kadan bayan samun nasarar lashe zabe a 1983, sojoji sun kifar da gwamnatin sa inda Manjo Janar Muhammadu Buhari ya hau mulki kafin sake juyin mulki a 1985 da tsohon shugaba Janar Ibrahim Babangida ya hau mulki.*

*Marigayin dai da ya tsaya takara karkashin jam’iyyar NPN mai alamar masara, ya samu mataimaki daga yankin kabilar Igbo marigayi Alex Ekwueme. Bayanai na nuna za a yi jana’izar marigayin wanda ya rasu ya na shekaru 93 a garin Shagari da ke jihar Sokoto helkwatar Daular Usamniyya ta Dan Fodio a asabar din nan.*

*Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sauka a Uyo jihar Akwa Ibom inda ya kaddamar da kamfen din neman tazarce a matakin jihohin kudu maso kudu. Jihohin da kamfen din ya shafa sun hada da Akwa Ibom, Bayelsa, Rivers, Cross Rivers, Delta da Edo.*

*An ga dafifin ‘yan jam’iyyar APC na yankin na sowar mara baya ga shugaban wanda ya iso filin taron bayan isar sauran manyan ‘yan jam’iyyar irin Bola Tinubu, Adams Odshimohle, Rotimi Amaechi, Godswill Akpabio da sauran su. Masu jawaban musamman Sanata Akpabio sun yi hasashen APC za ta kwace gwamnatin jihar ta Akwa Ibom da ke karakashin babbar jam’iyyar adawa ta PDP.*

*Gwamnan jihar Emmanuel Udom na neman tazarce kuma ya nuna sauya shekar Akpabio ba za ta shafi tasirin sa a siyasa ba.*

*Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tura jami’an ta gidan Sanata Dino Melaye a anguwar Maitama don neman awun gaba da shi da tuhumar yunkurin kashe jami’in ‘yan sanda. Rundunar ta zargi Melaye tare da ‘yan bangar sa na siyasa da yunkurin kashe jami’in ‘yan sanda Danjuma Salihu a Kogi yayin da ‘yan sanda su ka nemi dakatar da tawagar Sanatan don bincike.*

*Dino Melaye dai dama ya yi zargin babban sufeton ‘yan sanda Ibrahim Idris na shirin kama shi da yi ma sa allurar gubar mutuwa. Tuni ‘yan sanda su ka yi watsi da zargin da nuna Melaye ya amsa laifukan sa maimakon neman kawo ‘yan dabaru.*

*Sabon ministan harkokin wajen Saudiyya Ibrahim Al-Assaf ya `ce kasar ta Larabawa ba ta cikin wani rudani kan batun mutuwar Jamal Kashoggi duk da kasar ta kadu ainun da nuna juyayin kashe marigayin. Al-Assaf na magana ne kwana daya bayan nada shi ministan waje inda a ka rage mukamin tsohon ministan Adel Alubeir zuwa karamin ministan ma’aikatar.*

*Al-Assaf ya ce ba batun Kashoggi ba ne ya sanya rage mukamin Aljubeir, amma hakan garambawul ne da kasar ke yi na sabunta lamura da Yarima Muhammad Bin Salman ke jagoranta.*

*Ibrahim Baba Suleiman*
*Jibwis New Media*                                                                         *21-Rabi-ul-Thani-1440*
*29-December-2018*

CIKIKKEN SUNAYEN EN AL-JANNA DA IYALEN MONXON ALLAH (SAW).๐ŸŒณ SUNAN MATAYEN MANZON ALLAH ( S.A.W )๐ŸŒณ

๐Ÿ‘‰ 1. Khadijatu 'yar Khuwailid
๐Ÿ‘‰ 2. Saudatu 'yar Zam'atu
๐Ÿ‘‰ 3. Hafsah 'yar Umar
๐Ÿ‘‰ 4. Aisha 'yar Abubakar
๐Ÿ‘‰ 5. Zainab 'yar Khuzaimah
๐Ÿ‘‰ 6. Zainab 'yar Jahshin
๐Ÿ‘‰ 7. Juwairiyya 'yar Haris
๐Ÿ‘‰ 8. Ummu Salama (HINDU)'yar Abu Umayyah
๐Ÿ‘‰ 9. Safiyya 'yar Huyayyu
10. Ummu habibah (Ramlatu) 'yar Abu Sufyan
๐Ÿ‘‰ 11. Maimunah 'yar Haris

๐ŸŒณ SUNAN YA'YAYEN ANNABI ( S.A.W )๐ŸŒณ

๐Ÿ‘‰ 1. Ibrahim
๐Ÿ‘‰ 2. Alkasim
๐Ÿ‘‰ 3. Abdullahi
๐Ÿ‘‰ 4. Zainab
๐Ÿ‘‰ 5. Rukayyah
๐Ÿ‘‰ 6. Ummu kulsum
๐Ÿ‘‰ 7. Fadimatu

๐ŸŒณ SAHABBAI GOMA DA AKA YIWA BUSHARA DA ALJANNAH ๐ŸŒณ

๐Ÿ‘‰ 1. Abubakar Assiddik.
๐Ÿ‘‰ 2. Umar Dan Khaddab.
๐Ÿ‘‰ 3. Usman Dan Affan.
๐Ÿ‘‰ 4. Aliyu Dan Abi Dalib.
๐Ÿ‘‰ 5. Dalha Dan Abaidullahi.
๐Ÿ‘‰ 6. Zubairu Dan Awwam.
๐Ÿ‘‰ 7. Abu Ubaida Dan Jarrah.
๐Ÿ‘‰ 8. Abdurrahman Dan Aufu.
๐Ÿ‘‰ 9. Sa'adu Dan Abi Wakkas.
๐Ÿ‘‰ 10. Sa'idu Dan Zaid.

๐ŸŒณ SHIKA SHIKAN MUSULUNCI GUDA BIYAR๐ŸŒณ

๐Ÿ‘‰ 1. Tauhidi.
๐Ÿ‘‰ 2. Sallah.
๐Ÿ‘‰ 3. Azumi.
๐Ÿ‘‰ 4. Zakkah.
๐Ÿ‘‰ 5. Hajji.

๐ŸŒณ SUNAYEN WATANNIN MUSULUNCI : ๐ŸŒณ

๐Ÿ‘‰ 1. Almuharram.
๐Ÿ‘‰ 2. Safar.
๐Ÿ‘‰ 3. Rabi'ul Awwal.
๐Ÿ‘‰ 4. Rabi'ul Sani.
๐Ÿ‘‰ 5. Jumadal Ula.
๐Ÿ‘‰ 6. Jumadal Akhirah.
๐Ÿ‘‰ 7. Rajab.
๐Ÿ‘‰ 8. Sha'aban.
๐Ÿ‘‰ 9. Ramadhan.
๐Ÿ‘‰ 10. Shawwal.
๐Ÿ‘‰ 11. Zulkidah.
๐Ÿ‘‰ 12. Zulhijji.
 
๐ŸŒณ NAFILOLIN DA MANZON ALLAH YAYI KUMA YACE AYI. ๐ŸŒณ๐Ÿ‘‰ 1) Raka'a 2 kafin sallar asuba
๐Ÿ‘‰ 2) Raka'a 4 kafin sallar azahar
๐Ÿ‘‰ 3) Raka'a 2 bayan sallar azahar
๐Ÿ‘‰ 4)Raka'a 2 bayan magariba
๐Ÿ‘‰ 5) Raka'a 2 bayan sallar insha,

  * DAN-UWANKU A MUSLIMCI.

HAKKOKIN MA'AURATABismillahi Rahmanir Rahim

 2- CIYARWA: ciyarwa na daga cikin hakkin mace a kan mijinta. Akwai hakkin ciyarwa daidai gwargwadon ikonsa,kamar yadda Allah SWT yake fada a cikin littafinsa mai tsarki... “sai  mawadaci ya ciyar daga abin da aka bashi kuma wanda aka kuntata masa
arzikinsa toh sai ya ciyar daga abinda Allah ya bashi “

Allah ta’ala yace:”kuma ciyar dasu da tufatar dasu yana kan wanda aka haifawa da alkhair”. Suratul bakara:223.

“Mazaje sune masu tsayuwa akan mata saboda abin da Allah ya fifita sashinsu akan sashi da abinda suke ciyarwa na dukiyoyinsu” suratul Nisa:34

Yazo a cikin wani hadisi na hakam dan mu’awiya Alkushairi wanda ya karbo daga baban sa R/A yace: “Ya Rasulilla, menene hakkin mace? Sai manzon Allah S.A.W yace: “ka ciyar da ita idan kayi tufafi” Abu dawud ne ya rawaito.
Da hadisin da jabir ya rawaito Allah ya yarda dashi a cikin khudba “mata suna da hakkin ciyarwa da tufatarwa da kyautatawa” DAKE AKE GLOBAL CONSULTACY

[SHAYARWA] YAKAMATA A SHAYAR DA JARIRI NONO SAU '8 ZUWA 12' CIKIN DARE DA YINI.Alamun hadi mai kyau  sune,

1_bakin jaririn/jaririyar a hangame yake,

2_za,aga ba-bakin dasashin bakin jariri/jaririya na sama,fiyeda nakasa.

3_leben jariri/jaririyar na kasa ya dago sama.

4_leben jariri/jaririyar tana taba nono,

*Lalle jariri/jaririyar ku sudinga jan nono a hankali yadda ruwan zai zubo dayawa,suna dan saurarawa,

KAMAR SAUNAWA YAKAMATA IN SHAYAR DA  NONO ARANA?

*Ku shayar da jariranku lokacin da suke bukata,dare da rana,akalla sau takwas 8 zuwa sha Biyu 12 a kullum,

*cin abinci akai-akai zaitemakawa jikinku,yasamar da Ruwan Nono,

*kucigaba da shayar da jariranku har sai su dakansu sun koshi sunsaki nonon,sai kusake dungura musu dayan nonon,idan sunkoshi bazasu kamaba,

*- zaku iyaganewa da kanku idan jariranku suna shan I isashshen Nono,alamun kuwa sune,zakuga jaririn/jaririyar suna fitsari Wanda kalarsa,batacizaba,kuma akallah sau shida arana,kuma Akallah sau shida arana kuma suna kara nauyi,
*
Kubi ahankali,kuzauna ko Ku kishingida domin shayarwa,kudinga zama kusa da jariranku dare da rana,

Zandakata anan sai nangaba zanci gaba insha Allah


Abinda mukafada daidai wannan Daga Allah ne akasin haka kuma Daga garenine da fatan zaku yafemun๐Ÿคฒ๐Ÿผ


YADAWA:Daga cibiyar bincike da wayar da kan mata da yada alkhairai ta
DAKE AKE GLOBAL
CONSULTANCY.

FARKON MA HADDATAN QUR-ANI A DUNIYA.T~~~ 956
Su wanene daga cikin sahabban manzon Allah SAW suka haddace Al'qurni lokacin yana Raye?

AMSA
1. Abubakar Assidiq
2. Umar bn kaษ—dab
3. Usman bn affan
4. Aliyu bn Abu ฦŠalib
5. Abdurrahman bn Auf
6. Azzubai bn Auwam
7. Mu'az bn jabal
8. Ubay bn Ka'ab
9. Zaid bn Thabit
10. Abu zaid
11. Abdullahi bn Amru
12. ฦŠalha bn Ubaidullah
13. Abdullahi bn mas'ud
14. Huzaif alyamani
15. Salim
16. Abu huraira
17. Abdullahi bn Umar
18. Abdullahi bn Abbas
19. Amru bn Aas
20. Abdullahi bn Amru
21. Mu'awiyya
22. Abdullahi bn zubair
23. Abdullahi bn Sa'ib
24. Aisha
25. Ummu salma
26. Anas bn malik
27. Abu zaid.

Duk akwai maganar malamai cewa wasu bayan rasuwar annabi saka haษ—a haddarsu.
Wallahu aalam

Amsawa: Mal Adam Daiyib

AL-QUR'ANI YA AMBACI GIZO GIZO DA SORA MAI ZAMAN KANSA KUN SAN MEYE HIKIMAR!!? * ME KA SANI DANGANE DA ALQUR'ANI MAI GIRMA

.
Qur'ani na da harrufa 323,015
.
Qur'ani na da Juzi'i 30
.
Qur'ani na da Hizbi 60
.
Qur'ani na da rubu'i 240
.
Qur'ani na da ushuri 480
.
Qur'ani na da aya 6666
.
Surorin Makkah 85
.
Surorin Madinah 29
.
Surarin da suka fara da 'Alhamdu' guda 5
.
Surorin da suka fara da Tasbihi guda 6
.
Surorin da suka fara da harrufa guda 19
.
Guraren Sujjada a Qur'ani guda 15
.
Farkon wanda ya fara bayyana karatun Qur'ani cikin
Sahabbai a Makkah shi ne Abdullahi bn Mas'ud
.
Kalma mafi tsayi a cikin Qur'ani ita ce 'Fa'asqainaakum
uhu' ta na da harrufa 11 a rubutun ta na larabci.
.
Qira'ar da tafi shahara wajen karatun Qur'ani ita ce
ruwayar Hafs daga Aasim. Hafs ya bar duniya a shekara ta
180 H, Asim kuma 127H
.
Tsuntsaye da aka ambaci sunayen su a Qur'ani;
*Alba'ubh
*As Salwa
*Al Guraab
*Al Jarad
*An Nahl
*Al Hudhuda
*Az Zubab
.
Sahabin da aka ambaci sunan sa a Qur'ani Zaidu bn
Thabit a cikin Suratu Ahzab
.
Rabe-raben Qur'ani ; akwai Surori masu suna;
*As Saba'ud Diwaal- sune Bakara, Aali Imran, Nisa'i,
Ma'ida, A'araf, An'am, Yunus. Su 7 ne, su suka fi tsayi.
*Akwai Almi'aini; daga bayan Yunus zuwa Surorin da suka
kai ayoyi 100 ko kusa da haka
*Almathani
*Almufassal su ne kananan surori daga 'Qaaf' ko 'Hujrat'
.
Surah mafi girma ita ce Suratu Fatiha
.
Aya mafi girma ita ce Ayatul Kursiyyu
.
Shugaban masu Tafsirin Qur'ani shi ne Imamud Dabariy
.
Annabin da aka fi ambaton sunan sa a Qur'ani shi ne
Annabi Musa (s.a.w) sau 136
.
Sura ta karshen sauka cikin Qur'ani ita ce suratun Nasr
(Iza ja'a)
.
Aya ta karshen sauka a Qur'ani ita ce aya ta 281 a cikin
Bakara (Wattaquu yauman) a magana mafi inganci
.
Surorin da aka ambace su da sunan dabbobi;
*Baqara-Saniya
*Namli-Tururuwa
*Ankabut-Gizo Gizo
*Nahli-Qudan Zuma
*Fiyl-Giwa
.
Surorin da aka ambace su da sunayen Annabawa;
*Suratu Yusuf
*Suratu Hud
*Suratu Ibrahim
*Suratu Muhammad
*Suratu Nuh
*Suratu Yunus
.
Surorin da aka ambace su da sunayen su taurari;
*Suratut Najm
*Suratul Qamar
*Suratud Dariq
*Suratush Shams
*Suratul Buruj
.
Surorin da aka ambace su da sunayen lokuta;
*Suratul Fajr
*Suratul Laili
*Suratud Dhuha
*Suratul Asr
.
Dabbobin da aka ambace su cikin Qur'ani;
*Baqara Saniya
*Ba'ubha Kwarkwata
*Zubaab Quda
*Namli Tururuwa
*Hudhuda tsuntsu
*Naaqah Raquma
*Khail Doki
*Bighaal Alfadari
*Himar Jaki
*Qusuurah Zaki
*Jaraad Fari
*Zi'b Kerkeci
*Kalb Kare
*Guraab Hankaka
*Fiyl Giwa
*Ankabuut Gizo Gizo
*Nahl Zuma
*Su'ban
*Ibil Rakumi
.
Sunayen Mala'iku da ya zo cikin Qur'ani;
*Jibril
*Miika'iil
*Maalik
*Haruut
*Maarut
.
Daular da aka ambace ta cikin Qur'ani ita ce daular
Rumawa-Ruum
.
Qabilar da aka ambace ta a cikin Qur'ani ita ce qabilar
Quraishawa-Quraish
.
Littattafan Tafsiri da suka fi shahara
*Tafsirud Dabari
*Tafsiru Ibn Katheer
*Tafsiru Ruhul Ma'ani-Aluusiy
*Tafsirul Qurdabi
*Tafsiru Mafaatihul Gaib
.
Gurare 4 sunan Annabin mu Muhammad (SAW) ya zo a cikin Qur'ani;
*Aali Imran aya ta 144
*Ahzab aya ta 40
*Muhammad aya ta 2
*Fathi aya ta 29.
.
Daga littafin
๏ปฃ๏บŽ๏บซ๏บ ๏บ—๏ปŒ๏บฎ๏ป‘ ๏ป‹๏ปฆ ๏บ๏ปŸ๏ป˜๏บฎ๏บ๏ปฅ ๏ปญ๏บ๏ปŸ๏ปจ๏บ’๏ปฒ

Yadda aka tsara taron gangamin harcen Hausa.Yau Alhamis 19-12-2018 da Misalin 9pm zuwa 10pm zamu kasance da kwararren marubucin Hausa daga garin Zaria Mallam Ibrahim Suleiman Mai Bazazzagiya wanda zai bamu ka'idodin daya kamata mu kula dasu wajen yin rubutukanmu Inda zasu karbu a duniya da dai sauran bayanai Insha Allah zamu kasance tare dashi.

Ranar Juma'a 20-12-2018 Karfe 8pm zuwa 9pm Insha Allah zamu kasance da kwararriyar Lauya daga Jihar Borno Barrister Aisha Usman zamu kasance da ita zata kallar mana abubuwan da mukeyi a Social Media a bayani na doka me dokar 'kasa tace akai, iya wadanne abubuwa ne yakamata muyi wadanne abubuwane basu kamata muyi ba. Ina yakamata mu tsaya iya ina yakamata kada mu tsaya.

Ranar Juma'a 20-12-2018  9pm zuwa 10pm Insha Allah zamu kasance da jami'in tsaro daga sashin dake kula da lefuka na Yanar Gizo daga head quartersu dake Jihar Kano. amma bamu samu approving daga wajensu amma idan basu samu damar gabatarwa ba zamu sake sanya wata ranar domin gabatar da shirin.

Ranar Asabar 21-12-2018 Insha Allah zamu fara zamu bude Blog kuma zamuyi posting aciki

Ranar Lahadi 22-12-2018 Zamu siyi Domain Name da sauran duk abubuwan da suka kamata muyi ranar kowa zai tanadi N1000 wacce mukace a ajiye zamu siyi Domain da ita ta hanyar Transfer za'a siya don haka kowa ya tanadi N1000 a account dinsa.

Ranar Litinin 23-12-2018 Zamu bude Email na kowane site Misali kamar Info@sharfadi.com da dai sunan site dinka sannan a ranar zamuyi posting na Monetizing shine yadda ake samun kudi da blogging.

Akwai mutum biyu da muke sanya rai Insha Allah zasu sakaa ido akan duk yadda zaman zasu kasance na farko Shine: Bashir Yahuza Malumfashi Editor na Jaridar Aminiya Na biyu shine Doctor Sarari wanda ba boyayye bane kuma mutum ne da yake kishin harshen Hausa sosai don a yanzu haka akwai yuwuwar zuwa January zai bude gidan radio da television babba mai karfi irin na Arewa24 don bunkasa harshen Hausa anan Birnin Kano. Insha Allah wadannan mutanen biyu zasu saka ido akan duk abubuwan da za'a gabatar a karshe su tattara zasu bamu shawara Insha Allah. Yanada kyau kowa ya Da Karfe 8:45pm zan gabatarda abinda za'a gabatar Kafin Karfe 9pm lokacinda bakonmu zai fara dora.

Kada a manta abubuwan da kowa yakamata ya tanada sune
Blog Name, Title, Discreption, da sauran rubututtuka masu kayatarwa.

Muh'd M. Umar

[Karanta Yanxo] Kaji Motions A Majalisar Dinkin Duniya da Lahirah.Majalisar Annabi Muhammad  (SAW)

   Wata rana Manzon Allah (SAW) yana zaune tare da Sahabbansa, sai ya fara tambayar su daya bayan daya, sai ya fara da Sayyidina Abubakar 'yantaccen wuta

Yace: "Yaa Abubakar! Me kake so a duniya?

Sai Sayyidina Abubakar yace: abinda na fi so a duniya_
1: zama a gaban ka,
2: kallon ka,
3: ciyar da dukiya ta gare ka.

Sannan Manzon Allah ya koma wajen Sayyidna Umar dan Khaddabi mai abin mamaki
Manzon Allah (Saw) yace: yaa Umar! Me ka fi so a duniya?

Sai Sayyidna Umar yace : abinda na fi so_
1: a mini umurni da kyakkyawan aiki ko da a boye ne,
2: a mini hani da mummunan aiki ko da a bayyane ne,
3: da kuma fadin gaskiya ko da tana da daci.

_Sannan manzon Allah ya koma wajen Uthman dan Affan, yace masa: "yaa Uthman! Me kafi so a duniya?_

_Sai Uthman dan Affan yace: abinda na fi so a duniya_
1: ciyar da abinci ga mabukaci,
2: yada sallama,
3: yin sallah cikin dare a lokacin mutane suna bacci.

_Sannan Manzon Allah (Saw) ya koma ta wajen Aliyyu dan Abi Daalib, yace masa: "yaa Aliyyu! Me ka fi so a duniya?_

_Sai Sayyidna Aliyyu yace: abinda na fi so a duniya_
1: Azumi a lokacin rani,
2: Karrama bako,
3: yakar abokan gaba da takobbi.

_Sannan Manzon Allah (Saw) ya koma wajen Abaa zarril Gifaari, ya ce masa: "yaa Abaa Zarri? Me ka fi so a duniya?_

_Sai Abaa Zarri yace: abinda na fi so a duniya_
1: yunwa,
2: jinya,
3: mutuwa.

_Sai manzon Allah (Saw) yace: "sabida me yasa kake son su?_
Sai Aba zarri yace:

*ina son yunwa ne don zuciya ta tayi laushi,
*ina son jinya ne don zunubi na yayi sauqi,
*ina son mutuwa ne sabida saduwa da ubangiji na

_A wannan lokacinne Mala'ika Jibrili ya sauqo zuwa majalisar Manzon Allah (domin hirar ta su ta birge shi ), sai yace: ni kuma ina son abubuwa uku a duniyar ku_
1: isar da sako,
2: bayar da amana,
3: son nakasassu.

_Daga fadin haka kuma sai ya tashi zuwa sama Sannan ya sauko a karo na daban sannan yace Allah madaukakin sarki yana karanta muku sallama Hirar manzon Allah da sahabbai tayi dadi, harma Allah yana gaishe su sannan Allah yace yana son abubuwa uku a duniyar ku_
1: harshe mai ambatonSa,
2: zuciya mai tsoronSa,
3: jikin da aka jarrabce shi da balaa'i kuma yayi hakuri.

_Tsarki da godiya sun tabbata ga Allah Girma da tsarki sun tabbata Allah_ Adu'o'i guda uku kada ku manta su acikin sujjadarku..
"Ya Allah ina rokonka kyawawan halaye".
"Allah ka azurta ni da tuba zuwa gareka tabbatace"
"Ya ALLAH mamallakin zuciyata ka tabbatar da ita akan addininka"

Lalle wannan ya cancanta ku tura zuwa ga waninku domin ya amfana.

Dauki darasin ka a cikin wannan hadith, ka aikata shi, za ka yi nasara.

Majalisar Manzon Allah makarantar mai imani ne, yi kokari ka fita a sahun farko na daliban makarantar.

{Darajarki abincinki} Dake ake.Assalamu alaikum wa Rahmatullah wa Barakatuh.

๐ŸฅRaisin roll๐Ÿฅ

Kayan hadi :
Flour gwangwani 4
Yeast teaspoon 1
Baking powder 1tea
Butter 2 tablespoon
Madara 4talbespoo
Kwai 1
Raisin gwangwani 1
Sugar 4 tablespoon

Yadda zaayi
Kisami flour ki tannkade kizuba yeast,bakinpowder,sugar, madara butter ki juya sosai kumai yahade sannan kisa kwai ki juya sannan kisa ruwa ki kwaba ki buga shi sosai kwabin kamar na meat pie sai kisa Leda ki rufe.ki ajiye a waje mai dumi dan ya tashi

Idan kwabin ya tashi sai ki murzashi yayi fadi,sai kiyi circle shape,saiki dauko butter ki shafa akan wannan kwabin saiki barbada madara sannan ki kawo inibi shima ki Barbada Ko ina sannan kinannade kamar tabarma sai ki yanka .

Sannan ki jera shi a farantin gashi,ki juya shi tsaye saiki sami kwai ko madara ki dauko brush ki dangwala  ki shafa saman  saiki gasa idan yayi golding Brown saiki cire asha da lemo๐Ÿท

     Safiya ...

[AURE] BA TA HANA MAKARANTA KO KUN SAN DALILI?Shannan, Aure tafi makaranta a lokacin ta.
 Daga Shehun Mallami *Imamul Juwaini Asshafi ee,*  yana cewa:

 Ku samawa kanku lafiya da mafita, bincike ya tabbatar da cewa; "Hanyoyin warkewa daga cutar hauka itace ; Yin Aure. Kamar kuma yadda bincike ya tabbatar cewa; Hanyoyin kamuwa da hauka shine; Rashin aure (Gwauranta da Tuzuranta).

Ku duba littafinsa mai suna (NIHAYATUL MADLAB 12/43).

Da yawa zakaga saurayi ko budurwa a hargitse kamar masu hauka, daga anyi aure sai ka rantse da Allah basu bane, niimar aure ta mayar dasu mutane. Sannan da yawa 'yammata masu aljanu kana auraddasu wallahi da yawa sai aljanun su tafi.

*KIRA GA IYAYE:
* Wallahi aure baya hana makaranta, kuma makaranta batafi aure ba, musamman a wannan zamanin da muke ciki, akwai matsaloli da yawa.

Allah ka gyara mana al'ummar mu, Allah Ka azurta gwagware da tuzurai mazansu da matansu su samu na gari, masu rufin asiri da kwanciyar hankali.

ู†ุฏุงุก ู„ู„ุนุฒุงุจ.. ุฃุฏุฑูƒูˆุง ุฃู†ูุณูƒู… !!!
ู‚ุงู„ ุงู„ุฌูˆูŠู†ูŠ ุงู„ุดุงูุนูŠ :
( ูˆุงู„ู†ูƒุงุญ ู…ู† ุฃุณุจุงุจ ุฒูˆุงู„ ุงู„ุฌู†ูˆู† ، ูƒู…ุง ุฃู† ุงู„ุนุฒุจุฉ ู…ู† ุฃุณุจุงุจ ุงู„ุฌู†ูˆู† )
[ ู†ู‡ุงูŠุฉ ุงู„ู…ุทู„ุจ 12/ 43]
ู…ู†ู‚ูˆู„

*DR UMAR GARBA IBRAHIM DOKAJI*

DOKOKIN YANAR GIZO (SOCOAL MEDIA) TAREDA KWARARRIYAR LAWYA, BARISTA A. A. USMAN.     Tambayuyi da Amsoshi.

1-  Mene ne copyright?

Copyright hakkin mallakan abinda ka rubuta ko wani Abinka wanda kaine ka mallakeshi.


2- Shin menene privacy?

Privacy: wani abu da ya shafeka ba zaka so wani ya sani ba. (Sirrinka).

Ko kuma abinka da baka Kai ga bayyanashi ga jama'a ba.

- Masali laifin privacy kamar dauka photon mutun bai Dani ba.

3- Kafafen Yada Labarai na Rediyo da tv ana yawan sanya Ido tare da taka mu su Birki akan wasu abubuwa da suka sabawa Dokoki. Amma a Yana gizo sai ka ga su na ci gaba da Baje-kolinsu ba tare da Hukunci ba.
Laifin Mahukunta ne ko Kuma Alkalai ne?

* A' a, ai sabon ci gaba ne Internet din, she ya sa dokokin ma yanzu ake kirkiransu a Nigeria.


4- Tambayata ga Barr.

Shin wai mene a Nijeriya a ke ci gaba da samun Sabgar nan ta Kwafin Rubutu Copyright Ma'ana a na ci gaba da samun bazuwarsa a Kafafen Yada Labarai na Yanar Gizo-Gizo

Shin rashin aiki da Dokokin ne ko Kuma rashin fadakar da jama'a ne?

Shin rashin Ilimi ne ko Kuma Rashin ladabtar da masu aikata wannan Sabgar ta kalaman Batanci  ?

* Dukka biyun bamu da cikkaken ilimi akan copyright dayawa bash san is actionable a kotu ba kuma ko sun sani basu damu da Kare ayyukansuba sam.


5- Ina wa Barista Barka da zuwa ina da tambaya kamar haka shin laifine idan mutun ya yi copy daga radio?

* Zai Iya zama laifi in baka sanar cewa ga inda na dauko bayanan.6- Ina ma Barr. Barka da zuwa shin laifine mutum yaje google yayi bincike yayi forming articles yayi posting a site dinsa.

* Kwarai kuwa laifi ne.

7- Tambaya
Barrister shin wadannan dokoki da kika zayyana, idan mutun ya karya su akwai wasu kotuna ne na musamman da akayi tanadi don yin hukunci?

* Sosai Yushe'u, akwai Federal high court in acikin kasa ne.


8- Inai wa Barr fatan Alkairi da godiya bisa namijin kokari da tayi na kasancewa damu cikin wannan shiri mai Albarka, Tambaya ta shine zan iya shiga *YouTube* in nasamu wani *Video Shots* da wani Yayi ni kuma sai na dawo na mayar dashi cikin rubutu.

Sannan zan iya daukan rubutun wani Wanda Yayi ba da yaren *Hausa* ba sai na maida shi *Hausa*

*Duk satar fasaha ce yana buqatar izini kafin ayi.

9- Tambaya
Mutum zai iya dauko labari na turanci daga wata kafa, ya fassara da Hausa a tashi kafar?

* A'a sai da izini.


10- Tambaya ta itace zan iya yin post akan wani mutum da ake zarginsa ko tuhumar sa da aikata laifi.

* Abba baza ka Iya rubutun batanci akan mutum  bisa zarghi har sai ka tabbatar da abun da ake zarginsan.

11- Ina neman karin ba yani akan harassment Laws.


* Harassment Laws: suna nufin dokokin akan cin zarafi ko akan mutum ko a kasuwancinsa.


12- Tambayata itace shin mutum zai iya zuwa cikin google ko cikin website Wanda ba nashi ba yayi copy and paste zuwa website dinshi?

* Abdul-Azeez Wannan Shima laifi ne ka copy abun wani ba izininsa musamman in har ya rubutu cewa a nemi izininsa Kafin amfani da shi.

13- Ana samun wadanda zasu yaudari mutane musamman mata su karbi hotonsu.
Daga baya suce sai ya biya kudi in ba haka ba su yada shi.

* Wannan criminal offence ne and is actionable a kotu in har an Kama shi dole a maza hukuncin.

 ~cheating it's there in our penal code.

Muh'd M. Umar

HUKUNCIN YAWAN ZUWA ZANCE TA WAYA A SHARI'ANCE.```Tambaya:```
      Dan Allah ina tambaya, Namiji ne yakeso ya qara aure to shine bayan ya dawo gida da dare sai budurwar ta riqa kiran shi ko kuma ta riqa turo txt, shikuma idan matarshi tana kusa sai ya riqa avoiding amma da ta dan daga sai shima ya fara responding ko ya kira ta, kuma idan asuba tayi sai ta kirashi. To shine matar ba taso, dan Allah a Shari'ance yana da laifi ko ba shi da? sannan matar zata iya neman ya dena ko kuwa ta shiga rayuwarsa ne a shari'ance?_


```Amsa:```

 To dan'uwa yana da kyau ka san cewa matar da kake nema aure ba muharramarka ba ce, don haka bai halatta ka dinga hira da ita ba, sai gwargwadon bukata.

 Yawan hira da budurwa da jin dadin zancenta, yana daga cikin abubuwan da suke kaiwa zuwa ga fitina, mai AHLARI ya kirga jin dadin zancen wacce ba muharrama ba daga cikin ayyukan da Allah ya hana.


 Duk wanda yake yawan hira da matar da ba muharramarsa ba, yana jin dadin zancenta, Allah zai iya haramta masa jin dadin zancen matarsa ta halal.


 Ya wajaba hirarka da buduwarka ta zama gwargwadon bukata, saboda jin dadin zancenta, zai iya kai ku, ku aikata katon sabo, yana daga cikin ka'idojin shari'a toshe duk hanyar da take kaiwa zuwa barna. Zunubi shi ne abin da ya sosu a ranka kuma ka ji tsoron kar mutane su yi tsinkayo, kamar yadda hakan ya tabbata a hadisin Muslim mai lamba ta: 2553.

Allah ne mafi sani.

Muh'd M. Umar

GANIN ALLAH A LAHIRAAl-Imamu Muslim da wasunsa sun ruwaito hadisi daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “An tambayi Manzon Allah (SAW) cewa ko za mu ga Ubangijinmu a ranar tashin alqiyama? Sai ya ce: Shin kuna yin turereniya wajen kallon rana da rana tsaka sanda ba girgije? Sai suka ce: A’ah. Sai ya ce: Ko kuna turereniya wajen kallon farin wata a daren haskensa sanda babu girgije?. Sai suka ce: A’ah.
Sai ya ce: “Na rantse da Allah wanda raina ke hannunsa ba za ku yi turereniya ba a wajen ganin Allah ba sai gwargwadon turereniyar da kuke yi wajen kallon wata ko rana. Sannan ya ce: [Ranar alqiyama] Allah zai gana da bawa, sai ya ce masa:
Kai wane! Ashe ban girmama ka ba? Ashe ban ba ka shugabanci ba? Ashe ban ba iyali ba? Ashe ban ba ka damar sarrafa dawaki da raquma ba? Ashe ban ba ka damar zama jagora ba? Ashe ba kai ne ka ke dauke daya bisa hudun ganima ba? Sai [bawa] ya amsa da cewa: An yi haka. Sai [Allah] ya ce masa: To dama kana tsammanin gamuwa da ni? Sai [bawa] ya ce: A’ah! Sai [Allah] ya ce masa: ba ruwana da kai kamar yadda ka yi halin ko-in-kula da ni.

Sannan sai Allah ya gana da [mutum] na biyu, sai ya ce masa: Kai wane! Ashe ban girmama ka ba? Ashe ban ba ka shugabanci ba? Ashe ban ba iyali ba? Ashe ban ba ka damar sarrafa dawaki da raquma ba? Ashe ban ba ka damar zama jagora ba? Ashe ba kai ne ka ke dauke daya bisa hudun ganima ba? Sai [bawa] ya amsa da cewa: An yi haka. Sai [Allah] ya ce masa: To dama kana tsammanin gamuwa da ni? Sai [bawa] ya ce: A’ah. Sai [Allah] ya ce masa: ba ruwana da kai kamar yadda ka yi halin ko-in-kula da ni.

Sannan kuma sai Allah ya gana da [mutum] na uku, sai yai masa tambayoyi irin wadanda suka gabata.  Sai ya ce: Ya Ubangiji! Na yi imani da kai, na yi imani da littafinka, na yi imani da manzanninka, na yi Sallah da Azumi da Sadaka. [haka] zai ta bayyana alherinsa gwargwadon iyawarsa. Sai [Allah] y ace: Anan ma karyar za ka yi?.
 [Sai Manzon Allah (SAW)] ya ce: Sa’annan sai a ce da shi: yanzun za a kawo shaidan da zai yi bayani akan ayyukanka. Sai [mutumin] ya fara tunani a zuciyarsa yana cewa: Oh! Ko waye zai zo ya ba shaida kaina? Daga nan sai a rufe bakinsa, kuma a ce da cinyarsa da namansa da qasusuwansa ku yi magana. Sai cinyarsa da namansa da qasusuwansa su yi magana su bayyana ayyukansa, [an yi hakan ne] don a kafa masa hujja. Wannan shine munafiki, wancan kuwa shine wanda Allah yai fushi da shi”.

ABU'BUWA 40 DA SUKE JAWO SAKIN AURE.1- Rashin ilimin zamantakewar aure.
2- Al'adu
3- Bidi'o'i (kamar lefe,gara d.s)
4- Rashin binciken halin miji kafin aure
5- Rashin binciken halin mace kafin aure
6- Matsalar iyayen miji
7- Matsalar iyayen mace
8- Matsalar dangin miji
9- Matsalar dangin mace
10- Rashin tsafta
11- Rashin iya kwalliya
12- Rashin iya magana
13- Rashin iya ciyarwa
14- Rashin iya kwanciyar aure
15- Rashin adalci
16- Goyon kaka ('yar shagwaba)
17- Auren kisan wuta
18- Zaman gidan haya
19- Ruwan ido wajen neman aure
20- Cin amanar aure
21- Auren bariki
22- Auren mace dan kudinta
23-Auren dole
24- Talauci
25- Qawaye
26- Zafin kishi
27- Rashin haihuwa
28- Rashin ladabi
29- Shaye-shayen kayan maye
30- Qannen miji
31- Abokan miji
32- Sata
33- Gulma
34- Tsananin damuwa
35- Waya(phone)
36- Rashin lafiyan miji wajen gamsar da mace
37- Rashin lafiyan mace wajen gamsar da miji
38- Sharrin boka
39- Rashin shawara tsakanin miji da mata
40- Aikin mace (kasancewar ta 'yar kasuwa, ma'aikaciyar gwamnati da sauransu.

#Daga Malam Aminu Ibrahim Daurawa.

ABUBUWA BAKWAI (7) DAKE SA MALA'IKU SUYIMA ADDU'A.

 
   
   
1. Lokacin da kake jiran sallah a masallaci.
    2. Lokacin da kake sallah a sahun farko.
    3. Fadin ameen bayan karatun fatiha a cikin sallah.
    4. Sallar subhi acikin Jam'i.
    5.  Yin addu'a ga dan uwanka musulmi abayan idonsa.
    6. Ciyarwa fisabilillah.
    7. Koyar da mutane al-khairi.
   
          Allah yasa Mudace.

HUKUNCIN HUDA HANCI SABODA KWALLIYA.

_Assalamu'alaikum, Malam dan Allah wata ce mijin ta yace hujin hanci na burge shi. So tana so ta huda sai aka ce mata babu kyau a musulunci. Shin malam ya abun yake? Haramun ne, ko kuwa tana iya hudawa tasa dankunne tayi kwalliya da shi?


```Amsa:```
_Wa alaikum assalam, An tambayi sheikh Ibnu Uthaimin akan Wannan mas'alar ta huda Hancฤฑ sai yake cewa: Huda Hanci zai iya zama Canza halittar Allah, amma Idan Garin da matar da ta huda hancin take ana yฤฑn ado a hanci, ta yadda hakan ya zama al'ada, to babu laifi ayi hakan. *Duba: Majmu'u Fatawaa Ibnu Uthaimin 11/137.*_

_Hakanan an tambayi *Sheikh Abdul Muhsin Al'abbad* akan haka a darasinsa da yake gabatarwa a Haram, sai ya ce babu laifi akan haka. Bisa Abin da ya gabata ya halatta matar BAHAUSHE ta huda hancinta saboda ta sanya abin kwalliya tun_da al'adarsu ce, saboda ya tabbata sahaban Annabi s.a.w mata suna huda kunnansu suna sanya 'yan kunnaye Kamar yadda hadisin Bukhari mai lamba: 98 yake nuni zuwa hakan._

    Allah ne mafi sani

[Cigaba] Yadda Zakayi Amfani Da Application (kamar WhatsApp & Instagram d.s) Sama Da Guda Daya A Wayarka'Yan uwa Assalamu alaikum yau za muyi magana akan yadda mutum zaiyi amfani da Applications na wayarsa sama da guda daya a waya guda daya.

Wato dai irin salon nan da 'yan gayu keyi a yanzu Baby ta gansu Online a wancan sim din sannan suyi magana da wani Sim din. 

In kun fahimta tsarin zai baiwa mutum damar bude account a facebook sama da guda daya kuma ya lura dasu ba tare da yayi log out ba, Haka su Twitter, WhatsApp, Insta d.s.

Dukkan apps dake wayarka zaka iya sakasu sama da sau daya a wayar. 

Yadda Ake Yi Shine:
Kaje Play store ka nemi application na "Morchat".
Sai kayi installing shikenan kamar yadda kuke gani a hoton dake kasa. 

Idan Allah ya kaimu Gobe zamuyi magana akan Yadda Mutum Zai Nemi Scholarships ta Wayarsa. 

Basheer Sharfadi 
Social Media Strategist. 
12-12-2018.
https://play.google.com/store/apps/details?id=info.cloneapp.mochat.arm64

[Karanta Yanzu] Yadda Zakayi Idan WAEC Original Result Dinka Ya Bata.Jama'a Assalamu alaikum a yau zamuyi magana akan yadda mutum zaiyi idan WAEC Original Result dinsa ya bata, sai a biyomu.

Idan ka duba jikin WAEC Original result zaka ga an rubuta cewa idan har ya bata to WAEC ba zata kara baka wani irin wannan result dinba.

Haka kuwa abin yake indai ka batar dashi to WAEC din zata shafawa idonta  toka tayi halin ba sani ba sabo domin kuwa ba zata baka wani irin wannan sakamakon ba.

Duk sanda wani abu ya taso maka da wani organisations ko hukumomi ke bukatar wannan result din to sai dai su rubuta takardar nema ga Hukumar WAEC, bayan wani lokaci hukumar WAEC zata aikawa da wannan organisation ko hukuma cewa Wane-wane tabbas yayi wannan jarrabawar da kuma karin bayani a rubuce, duk sanda mutum yake bukata sai yayi wannan tsarin.

A shekarar 2015 Hukumar WAEC ta canja sabon tsari cewa idan takardar ka ta bata.
Sabon tsarin 2015 shine mutum zai tafi hukumar WAEC ka sana musu cewa WAEC dinka fa ta bata.
Zaka tafi da hoton passport guda biyu.
Zaka cike form sannan ka biya N20, 000, WAEC zata buga maka sabon result irin wanda ya bata, ana kiran wannan result din da "Attestation" zaka ga an rubuta a jikinsa da jan biro, banbancin su kenan da na asalin.

Wannan itace hanyar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari yabi aka dawo masa da sakamakon jarabarwar sa da ya bata, sai dai shi Baba Buhari har Office aka kai masa, kai kuma babu wanda zai kawo maka har gida.
Zaka jira har WAEC ta gama sannan ta aiko da ita jiharka sai kaje ka karba shikenan.

Shawarata ga wanda jarrabawarsa ta bata:
1. Mutum yaje yayi police report.
2. Sannan yayi court affidavit.

Allah ya kiyaye batan jarabarwarmu Amin.

Basheer Sharfadi
Social Media Strategist

YADDA MUSULMI ZAI YI TA'AMULI DA BUKIN KIRSIMETI:


Da yake a Nigeria ana zaman cakuda ne tsakanin al'ummar Kirista da al'ummar Musulmi. Sannan da yake shi Musulunci addini ne da ya bayyanar da hukuncin dukkan wani lamari da ya shafi rayuwar dan Adam, ko dai ta hanyar nassi, ko ta hanyar zahiri, ko ta hanyar ishaarah da iimaai. Sannan da yake akwai karkatattu  da dama da suke halatta abin da Shari'ah ba ta halatta ba, ko haramta abin da Shari'ah ba ta haramta ba, lalle ya dace a yi wa al'ummar Musulmi bayanin hukuncin abin da ya shafi wannan Idi na Kirsimeti ta bangarorinsa da ke iya shafar wasu al'ummar Musulmi.

To amma kafin mu shiga bayanin wadannan hukunce-hukunce ya kamata Musulmi su san abubuwa kamar haka:-
1. Shi dai bukin kirsimeti wata bidi'ah ce da bata da Kiristoci suka kirkira sannan suka maida ita wata ibada da ake samun lada ta hanyar yin ta kamar dai yadda wasu Musulmi suka kirkiri bidi'ar idin Maulidi, Kiristoci sun kirkiri wannan bidi'ar ce kuwa a shekarar Miladiyyah ta 360, watau a cikin karni na hudu bayan haifuwar Annabi Isa alaihis salam.

2. Ya kamata kowa ya san cewa ba ya halatta Musulmi ya yi tarayya da wadanda ba musulmi ba cikin bukukuwansu na idi, watau ta hanyar halartan wasu tarurruka da za su kira, ko ta hanyar ba su wani taimako domin karfafa idodin nasu, wannan dai shi ne hanyar Salafus Salih: Sahabbai, da Taabi'ai, da Taabi'uttaabi'in; dalili kuwa shi ne:-
Imamul Baihaqiy ya ruwaito cikin As-Sunanul Kubraa hadithi na 19,334 cewa Sayyidina Umar Dan Khattab Allah Ya kara masa yarda ya ce: ((ุงุฌุชู†ุจูˆุง ุงุนุฏุงุก ุงู„ู„ู‡ ููŠ ุนูŠุฏู‡ู…)). Ma'ana: ((Ku nisanci makiya Allah cikin idinsu)).
Sannan Shaikhul Islam Ibnu Tamiyyah ya ce -kamar yadda ya zo cikin Al-Mustadrak Alaa Fataawaa Ibnu Tamiyyah 1/108, da Mukhtasarul Fataawaa Misriyyah1/517 :-
((ูˆู„ูŠุณ ู„ู„ู…ุณู„ู…ูŠู† ุงู† ูŠุนูŠู†ูˆู‡ู… ุนู„ู‰ ุฃุนูŠุงุฏู‡ู… ู„ุง ุจุจูŠุน ู…ุง ูŠุณุชุนูŠู†ูˆู† ุจู‡ ุนู„ู‰ ุนูŠุฏู‡ู… ูˆู„ุง ุจุงุฌุงุฑุฉ ุฏูˆุงุจู‡ู… ู„ูŠุฑูƒุจูˆู‡ุง ููŠ ุนูŠุฏู‡ู… ู„ุงู† ุฃุนูŠุงุฏู‡ู… ู…ู…ุง ุญุฑู…ู‡ ุงู„ู„ู‡ ุชุนุงู„ู‰ ูˆุฑุณูˆู„ู‡ ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู… ู„ู…ุง ููŠู‡ุง ู…ู† ุงู„ูƒูุฑ ูˆุงู„ูุณูˆู‚ ูˆุงู„ุนุตูŠุงู†)). ุงู†ุชู‡ู‰.
Ma'ana: ((Musulmi ba su da damar su taimaka musu cikin idodinsu, ko  dai ta hanyar sayar musu da abin da za su karfafu da shi, ko ta hanyar ba da hayar dabbobinsu domin su hau su cikin idinsu, saboda idodinsu na daga cikin abin da Allah Madaukakin Sarki da kuma manzonSa mai tsira da amincin Allah suka haramta, saboda abin da yake cikinsu na kafirci da fasikanci da kuma sabo)).

3. Babu wani wanda ya isa ya bugi kirji a duniyan nan ya ce: ga tabbatacciyar wata da rana da aka haifi Annabi Isa alaihis salam a cikinta, sai dai kowa ya fadi abin da yake zato kawai, wannan shi ya sa ma Kiristoci masu yin bukin ranar Kirsimeti watau ranar haifuwar Annabi Isa alaihis salam suka yi sabani dangane da ranar da za a yi wannan bukin zuwa mazhabobi biyu:-

Mazhabar farko: Za a yi bukin Kirsimeti ne a ran 25 ga watan December, wannan ita ce mazhabar da Catholic, da Protestant, da kuma mafi yawan bangarorin Kiristoci ke bi.

Mazhaba ta biyu: Za a yi bukin Kirsimeti ne a ran 7 ga watan January, wannan ita ce mazhabar da bangarorin Orthodox ke bi.

4. Kiristoci kafurai ne kamar yadda Yahudawa da Majusawa da sauran masu bautar gumaka suke kafurai, babu sabani cikin wannan mas'ala cikin  shari'ar Musulunci.

5. Ya kamata a san cewa akwai wasu kafuran da Musulunci ya kebanta su da wasu hukunce-hukunce saboda tabbatar wa Musulmi wata maslaha, wadannan kuwa su ne: Yahudawa da Kiristoci, su wannan nau'i na kafurai Musulunci ya halatta wa Musulmi cin yankansu, da auren matansu, sabanin mabiya addinin majusu, ko mabiya addinin Hindu, ko mabiya addinin Budha, ko mabiya sauran addinai na bautan gumaka.
Idan masu karatu sun fahimci wannan to sai mu shiga bayanin mas'alarmu da muke son yi wa jama'a bayaninta.

HUKUNCIN KARBAN KYAUTUTTUKAN KAFURAI A RANAR IDINSU:

Su kyaututtukan da kafurai -Ahlul kitabi ko wasun Ahlul kitabi- ke ba wa Musulmi a ranakun idinsu na kafurci da bidi'ah sun kasu kashi biyu ne:-

1. Kyaututtukan da suke ba nama ba ne da ake bukatar yankawa, watau kamar irinsu: halawa, da tufafi, da kayan marmari da sauransu.

2. Kyaututtukan da suke nama ne da ke bukatar a yi masa yanka irin ta Shari'ah.

To shi na farkon, watau kyaututtukan da suke ba nama ba ne da ke bukatar yanka irin ta Shari'ah, babu sabani tsakanin Salafus Salih -a dai iya saninmu- cikin halaccin karbarsu, saboda dalilai kamar haka:-

1- Imamul Baihaqii ya ruwaito athari na 18,644 daga Muhammad Dan Siiriin cewa:-
((ุฃุชูŠ ุนู„ูŠ ุฑุถูŠ ุงู„ู„ู‡ ุจู‡ุฏูŠุฉ ุงู„ู†ูŠุฑูˆุฒ، ูู‚ุงู„: ู…ุง ู‡ุฐู‡؟ ู‚ุงู„ูˆุง: ูŠุง ุงู…ูŠุฑ ุงู„ู…ุคู…ู†ูŠู† ู‡ุฐุง ูŠูˆู… ุงู„ู†ูŠุฑูˆุฒ. ู‚ุงู„: ูุงุตู†ุนูˆุง ูƒู„ ูŠูˆู… ููŠุฑูˆุฒ)) .
Ma'ana: ((An zo wa Sayyidina Aliyyu Dan Abii Taa'lib Allah Ya kara masa yarda da kyautar (idin) Nairuuz, sai ya ce: mene ne wannan? Sai suka ce: Ya Amirar Muu'miniin! Wannan ranar Nairuuz ce. Sai ya ce: (in haka abin yake) ku rika yin Fairuuz a ko wace rana)).

2- Imam Ibnu Abii Shaibah ya ruwaito cikin Musannaf athari na 24,371, da Imam Ishaq Ibnu Raa'huyyah cikin Musnad athari na 1,606 daga Qaa'bus Dan Zibyaan daga shi mahaifin nasa cewa wata mace ta tambayi Nana A'isha Allah Ya kara mata yarda ta ce:-
((ุงู† ู„ู†ุง ุงูƒุงุฑุง ู…ู† ุงู„ู…ุฌูˆุณ ูˆุงู†ู‡ ูŠูƒูˆู† ู„ู‡ู… ุงู„ุนูŠุฏ ููŠู‡ุฏูˆู† ู„ู†ุง، ูู‚ุงู„ุช: ุงู…ุง ู…ุง ุฐุจุญ ู„ุฐู„ูƒ ุงู„ูŠูˆู… ูู„ุง ุชุฃูƒู„ูˆุง ูˆู„ูƒู† ูƒู„ูˆุง ู…ู† ุฃุดุฌุงุฑู‡ู…))
Ma'ana: ((Muna da 'yan kodago daga cikin Majusawa, sannan kuma suna da ranar idin da suke aika mana da kyaututtuka. Sai ta ce: Amma abin da aka yanka saboda wannan ranar to kada ku ci, to amma ku ci daga 'ya'yan itatuwansu)).

3- Imam Ibnu Abii Shaibah ya ruwaito a cikin Musannaf athari na 24,372 daga Abuu Barzah cewa:-
((ูƒุงู† ู„ู‡ ุณูƒุงู† ู…ุฌูˆุณ ููƒุงู†ูˆุง ูŠู‡ุฏูˆู† ู„ู‡ ููŠ ุงู„ู†ูŠุฑูˆุฒ ูˆุงู„ู…ู‡ุฑุฌุงู† ููƒุงู† ูŠู‚ูˆู„ ู„ุฃู‡ู„ู‡: ู…ุง ูƒุงู† ู…ู† ูุงูƒู‡ุฉ ููƒู„ูˆุง ูˆู…ุง ูƒุงู† ู…ู† ุบูŠุฑ ุฐู„ูƒ ูุฑุฏูˆู‡)).
Ma'ana: ((Yana da wasu mazauna Majusawa, kuma sun kasance suna aika masa da kyautuka a lokacin Nairuuz da Mihrajan, sannan ya kasance yana gaya wa iyalansa cewa: Kyautar da ta kasance ta kayan marmari ne to ku ci, wacce kuma ta kasance ba hakan ba, to ku mayar da ita)).

Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya yi taliki a kan wadannan hujjojin a cikin littafinsa mai suna Iqtidhaa'us Siraa'til Mustaqiim 2/554-555 ya ce:-
((ูู‡ุฐุง ูŠุฏู„ ุนู„ู‰ ุงู†ู‡ ู„ุง ุชุฃุซูŠุฑ ู„ู„ุนูŠุฏ ููŠ ุงู„ู…ู†ุน ู…ู† ู‚ุจูˆู„ ู‡ุฏูŠุชู‡ู…، ุจู„ ุญูƒู…ู‡ุง ููŠ ุงู„ุนูŠุฏ ูˆุบูŠุฑู‡ ุณูˆุงุก؛ ู„ุงู†ู‡ ู„ูŠุณ ููŠ ุฐู„ูƒ ุฅุนุงู†ุฉ ู„ู‡ู… ุนู„ู‰ ุดุนุงุฆุฑ ูƒูุฑู‡ู…)).
Ma'ana: ((Wannan duka yana nuni ne a kan cewa: Idi ba yi da wani tasiri a kan hana karban kyautarsu, a'a hukuncin karban kyautarsu ba yi da wani bambanci tsakanin lokacin Idi da kuma lokacin da ba na Idi ba, saboda babu wani abu na taimakon addininsu a cikin karban kyautarsu)).

TALIKI:
Da wannan ne za mu fahimci cewa: Maluman Musulunci sun hana cin yankan da Majusawa suka yi domin bukukuwan idinsu, to amma fa ba wai  sun hana cin yankan ba ne saboda kasancewarsa yankan da aka yi domin bukin idin kafurai ba, a'a an hana cin yankan ne saboda kasancewarsa yankan Majusawan da ba sa cikin mutanen nan ne da ake kira Yahudawa ko ake kira Kiristoci, dukkan kuma kafurin da ba ya cikin abin da ake kira Yahudawa ko ake kira Kiristoci to ba a cin yankansa.

HUKUNCIN CIN NAMAN DABBAR DA YAHUDAWA KO KIRISTOCI SUKA YANKA DA HANNAYENSU SABODA YIN BUKUKUWAN IDINSU:

Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya yi bayani game da cin abin da Yahudawa ko Kiristoci suka yanka saboda bukukuwan idinsu, a cikin littafinsa mai suna Iqtidhaa'us Siraa'til Mustaqim 2/555,558 ya ce:-
((ูˆุงู†ู…ุง ูŠุฌูˆุฒ ุงู† ูŠุคูƒู„ ู…ู† ุทุนุงู… ุงู‡ู„ ุงู„ูƒุชุงุจ ููŠ ุนูŠุฏู‡ู… ุจุงุจุชูŠุงุน ุงูˆ ู‡ุฏูŠุฉ ุงูˆ ุบูŠุฑ ุฐู„ูƒ ู…ู…ุง ู„ู… ูŠุฐุจุญูˆู‡ ู„ู„ุนูŠุฏ. ูุฃู…ุง ุฐุจุญ ุงู„ู…ุฌูˆุณ ูุงู„ุญูƒู… ููŠู‡ุง ู…ุนู„ูˆู… ูุฅู†ู‡ุง ุญุฑุงู… ุนู†ุฏ ุงู„ุนุงู…ุฉ. ูˆุฃู…ุง ู…ุง ุฐุจุญู‡ ุงู‡ู„ ุงู„ูƒุชุงุจ ู„ุงุนูŠุงุฏู‡ู… ูˆู…ุง ูŠุชู‚ุฑุจูˆู† ุจุฐุจุญู‡ ุงู„ู‰ ุบูŠุฑ ุงู„ู„ู‡ ู†ุธูŠุฑ ู…ุง ูŠุฐุจุญ ุงู„ู…ุณู„ู…ูˆู† ู…ู† ู‡ุฏุงูŠุงู‡ู… ูˆุถุญุงูŠุงู‡ู… ู…ุชู‚ุฑุจูŠู† ุจู‡ุง ุงู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุชุนุงู„ู‰، ูˆุฐู„ูƒ ู…ุซู„ ู…ุง ูŠุฐุจุญูˆู† ู„ู„ู…ุณูŠุญ ูˆุงู„ุฒู‡ุฑุฉ، ูุนู† ุงุญู…ุฏ ุฑูˆุงูŠุชุงู†: ุงุดู‡ุฑู‡ู…ุง ููŠ ู†ุตูˆุตู‡: ุงู†ู‡ ู„ุง ูŠุจุงุญ ุงูƒู„ู‡ ูˆุงู† ู„ู… ูŠุณู… ุบูŠุฑ ุงู„ู„ู‡ ุชุนุงู„ู‰. ูˆู†ู‚ู„ ุงู„ู†ู‡ูŠ ุนู† ุฐู„ูƒ ุนู† ุนุงุฆุดุฉ ูˆุนุจุฏ ุงู„ู„ู‡ ุจู† ุนู…ุฑ.....ูˆุงู„ุฑูˆุงูŠุฉ ุงู„ุซุงู†ูŠุฉ ุงู† ุฐู„ูƒ ู…ูƒุฑูˆู‡ ุบูŠุฑ ู…ุญุฑู…))ุงู†ุชู‡ู‰
Ma'ana: (Cin abincin Ahlul Kitabi a lokacin idinsu ga abin da dama ba su yanka shi saboda Idi ba, yana halatta ne ta hanyar saye da kudi, ko kuwa kyauta, ko wanin haka. Amma abin da Majusawa suka yanka hukuncinsa sananne ne, watau haramun ne a wurin dukkan malamai, to amma abin da Ahlul Kitabi suka yanka saboda idinsu, da kuma abin da suke yin ibada ta hanyar yanka shi ga wanin Allah' kamar abin da suke yankawa saboda Almasihu, da Zahrah, irin dai abin da Musulmi suke yankawa na Hadaya, da Layya, domin neman kusantar Allah da shi, to, Imam Ahmad yana da fatawowi biyu game da hakan, fatawar farko wacce ita ce ta fi shahara: Wannan ba ya halatta a ci shi koda kuwa ba a ambaci sunan wanin Allah a kansa ba. An nakalto hana cin wannan yankan ma daga Nana A'isha, da Abdullahi Dan Umar.. Fatawa ta biyu ita ce: Cin wannan yankan makruuhi ne ba haramun ba. Wannan ita ce mazhabar Malikiyyah, Imam Malik ya kyamaci cin abin da Ahlul Kitabi suka yanka saboda Coci-Cocinsu, ko saboda idinsu amma ba tare da ya haramta hakan ba)).

Sannan har yanzu Sahikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya ce a cikin Iqtidhaa'us Siraa'til Mustaqim 2/559 :-
((ูˆู†ู‚ู„ุช ุงู„ุฑุฎุตุฉ ููŠ ุฐุจุงุฆุญ ุงู„ุฃุนูŠุงุฏ ูˆู†ุญูˆู‡ุง ุนู† ุทุงุฆูุฉ ู…ู† ุงู„ุตุญุงุจุฉ ุฑุถูŠ ุงู„ู„ู‡ ุนู†ู‡ู…، ูˆู‡ุฐุง ููŠู…ุง ุงุฐุง ู„ู… ูŠุณู…ูˆุง ุบูŠุฑ ุงู„ู„ู‡، ูุงู† ุณู…ูˆุง ุบูŠุฑ ุงู„ู„ู‡ ููŠ ุนูŠุฏู‡ู… ุงูˆ ุบูŠุฑ ุนูŠุฏู‡ู… ุญุฑู… ููŠ ุงุดู‡ุฑ ุงู„ุฑูˆุงูŠุชูŠู†، ูˆู‡ูˆ ู…ุฐู‡ุจ ุงู„ุฌู…ู‡ูˆุฑ، ูˆู‡ูˆ ู…ุฐู‡ุจ ุงู„ูู‚ู‡ุงุก ุงู„ุซู„ุงุซุฉ ููŠู…ุง ู†ู‚ู„ู‡ ุบูŠุฑ ูˆุงุญุฏ، ูˆู‡ูˆ ู‚ูˆู„ ุนู„ูŠ ุจู† ุงุจูŠ ุทุงู„ุจ ูˆุบูŠุฑู‡ ู…ู† ุงู„ุตุญุงุจุฉ، ูˆู‡ูˆ ู‚ูˆู„ ุงูƒุซุฑ ูู‚ู‡ุงุก ุงู„ุดุงู… ูˆุบูŠุฑู‡ู…. ูˆุงู„ุซุงู†ูŠุฉ: ู„ุง ูŠุญุฑู… ูˆุงู† ุณู…ูˆุง ุบูŠุฑ ุงู„ู„ู‡، ูˆู‡ุฐุง ู‚ูˆู„ ุนุทุงุก ูˆู…ุฌุงู‡ุฏ ูˆู…ูƒุญูˆู„ ูˆุงู„ุงูˆุฒุงุนูŠ ูˆุงู„ู„ูŠุซ)).
Ma'ana: ((An ciro yin sauki a kan cin yanke-yanken idodin (Yahudawa da Kiristoci) da makamantansu (su yanke-yanken) daga wani sashi na Sahabbai Allah Ya kara musu yarda amma fa wannan sai idan ba su ambaci wanin Allah a lokacin yankan ba, in kuma har sun ambaci wanin Allah a lokacin yankan to cin sa ya haramta a cikin fatawa mafi shahara daga cikin fatawowi biyu da Imam Ahmada yake da su a cikin mas'alar, wannan kuwa shi ne mazhabar jumhur, kuma shi ne mazhabar Fuqaha'un nan guda uku, kamar yadda mutane da yawa suka ruwaito, kuma shi ne maganar Aliyyu Dan zabii Taa'lib da waninsa a cikin Sahabbai, daga cikinsu ma akwai Abud Dardaa, da Abu Umamah, da Irbadh Dan Saa'riyah, da Ubaa'dah Dan Saa'mit, kuma shi ne maganar maluman Sham da wasunsu. Fatawar Imam Ahmad ta biyu ita ce: Cin wannan yankan ba haramun ba ne koda kuwa sun ambaci sunan wanin Allah a lokacin yankan, wannan kuwa shi ne maganar Ataa'u, da Mujaa'hid, da Makhuul, da Auzaa'ii, da kuma Laith)).

Taliki na farko:-
Za mu fahimta daga maganganun malaman da suka gabata cewa: Abin da Yahudawa da Kiristoci suke yankawa saboda bukukuwan idinsu yana kasuwa ne zuwa kashi biyu:-

Na farko: Abin da suka ambaci sunan Allah yayin yanka shi.
Na biyu: Abin da suka ambaci sunan wanin Allah yayin yanka shi.

To ita tabbar da aka ambaci sunan Allah lokacin yanka ta, Malamai sun kasu kashi biyu game da hukuncin cinta.

Mazhabar farko: Sahabbai da yawa sun ba da damar cin wannan nama. Maluman Malikiyyah, da Imam Ahmad cikin ruwayah sun halattar da cinsa amma tare da nuna kyama.

Mazhaba ta biyu: Nana A'isha, da Abdullahi Dan Umar, da kuma Maluman Hanaa'bilah sun ce cin wannan nama haramun ne.

Sannan ita kuma dabbar da aka ambaci sunan wanin Allah lokacin yanka ta, watau kamar wacce aka ambaci sunan Yesu Almasihu lokacin yanka ta, wannan ma Malamai sun kasu kashi biyu game da hukuncin cin wannan dabbar:-

Mazhabar farko: Cin wannan dabba bai halatta ba, wannan shi ne abin da Aliyyu Dan Abii Taa'lib, da Abud Dardaa'u, da Abuu Umamah, da Irbadh Da Saa'riyah, da Ubaa'dah Dan Saa'mit, da Hanafiyyah, da Malikiyyah, da Shafi'iyyah, da Hanaa'bilah, da mafi yawan maluman kasar Sham, suk fada.

mazhaba ta biyu: Cin wannan dabba halal ne, wannan shi ne abin da Ataa'u, da Mhjaa'hid, da Makhul, da Auzaa'ii, da Laithu Dan Sa'ad, da kuma Imam Ahmad cikin ruwaya suka fada.

Taliki na biyu:-
Za mu iya fahimta daga maganganun da suka gabata cewa: Naman kasuwa da Musulmi ke yankawa da hannayensu idan Kiristoci suka saya suka dafa a matsayin abincin Kirsimeti, to wannan abincin halal yake ga dukkan wanda suka ba da shi gare shi. Wallahu A'alam.

HUKUNCIN CIN YANKAN KIRISTOCI DA YAHUDAWA A MAZHABAR MALIKIYYAH:
A karshen wannan makala tamu za mu yi bayanin mene ne mash'hurin mazhabar Malikiyyah game cin yankan Kiristoci da Yahudawa, saboda Musulmin wannan kasa tamu Nigeria su kara fahimtar irin banbancin da yake tsakanin abin da ke rubuce cikin littattafan Mazhabar Malkiyyah, da kuma abin da wasu jahilan 'yan bidi'ah da suke ikirarin cewa su masu bin Mazhabar Malikiyyah ne, alhali kuwa hayaniyarsu kawai suke yi, son zuciyarsu ne kawai suke bi, duk abin da jahilan shaihunansu suka ce to shi ne addini a wurinsu. Allah ya tsare mu da sharrin Shaidan.
Babban malamin Malikyyah Imamul Qurtubii ya ce cikin littafinsa Aljaami'u Li Ahkaamil Qur'an 6/53:-
((ูˆู‚ุงู„ ุฌู…ู‡ูˆุฑ ุงู„ุงู…ุฉ ุงู† ุฐุจูŠุญุฉ ูƒู„ ู†ุตุฑุงู†ูŠ ุญู„ุงู„ ุณูˆุงุก ู…ู† ุจู†ูŠ ุชุบู„ุจ ุงูˆ ุบูŠุฑู‡ู…، ูˆูƒุฐู„ูƒ ุงู„ูŠู‡ูˆุฏ)).
Ma'ana: ((Jumhuurin Al'ummah sun ce: Lalle yankan ko wane kirista halal ne, babu banbanci daga kabilar Taglib ne ko daga wasunsu, haka nan su ma Yahudawa)). Intaha.
Khalil Dan Ishaq ya ce cikin Mukhtasar Khalil shafi na 90
((ูˆุงู† ุณุงู…ุฑูŠุง ุงูˆ ู…ุฌูˆุณูŠุง ุชู†ุตุฑ ูˆุฐุจุญ ู„ู†ูุณู‡ ู…ุณุชุญู„ู‡، ูˆุงู† ุงูƒู„ ุงู„ู…ูŠุชุฉ ุงู† ู„ู… ูŠุบุจ))
Ma'an: ((koda ya kasance wani basaamire ne, ko bamajuse ne da yazama kirista ya yanka abin da yake halal a gare shi saboda kuma kan shi, koda kuwa yana halatta cin mushe ne, matukar dai musulmi na sane da cewa shi din ne ya yi yankan)).
Sannan ya zo cikin littafin Adhalulu Madaarik 2/92:-
((ูŠุฌูˆุฒ ู„ู„ู…ุณู„ู… ู†ูƒุงุญ ุญุฑุงุฆุฑ ุงู‡ู„ ุงู„ูƒุชุงุจ .. ูˆูƒุงู† ุงู„ุตุญุงุจุฉ ุจุชุฒูˆุฌูˆู† ู…ู† ุงู„ูŠู‡ูˆุฏ ูˆุงู„ู†ุตุงุฑู‰ ูƒุซูŠุฑุง ุฒู…ู† ุงู„ูุชุญ .. ูˆู†ูƒุญ ุนุซู…ุงู† ู†ุตุฑุงู†ูŠุฉ، ูˆู†ูƒุญ ุทู„ุญุฉ ูŠู‡ูˆุฏูŠุฉ)).
Ma'ana: ((yana halatta ga musulmi auren 'yantattun matan Ahlul Kitaabi.. Sahabbai sun kasance da yawa suna auren matan Yahudawa da Kiristoci a lokacin da ake cin kasashe da yaki.. Sayyidina Uthman ya auri wata kirista, Sayyidina Talhah ya auri wata bayahudiya)). Allah muke roko da Ya taimake mu. Ameen.

MAI BAZAZZGIYYA TAREDA KA'IDOJIN HARCEN HAUSA.1- Tambaya
Shin kalmar DABO ma'anoni nawa take dashi, sannan akoi wani  alaka ne da kalmar DABA?

 * Amsa.
A fahimtata. Dabo wani abu ne da wasu kan yi kamar surkulle ko tsafi. Domin a yaudari mutum.

Sannan ana amfani da ita idan wani abin mamaki ya faru. Misali ka wata tana zuwa. Ka dan waiga kadan, sai ka juyo in da take. Sai ba ka gan ta ba. Sai ka ce ta yi mani dabo.

Sannan idan karamin yaro ya fara tsayawa, sai a ce ya fara dabo. Ko dabo-dabo.

Kalmar DABA: Abin da na fahimta wani wurin taruwa ne na mutane. Amma an fi alakanta ta da wurin taruwar 'Yan iska.

Ban san ko akwai alaka tsakanin Dabo da Daba ba. DABO aikatau ne. DABA kuma suna ne.


2- Tambaya
Wurin nikanje na lokaci sabau, mutum bazaisa nakan jeba kenan?

 * Amsa
Mutum zai iya cewa haka, nakan je.

 3- Tambaya
 Shin wurin amfani da wakilin suna da aikatau, shin tilas ne a fara rubuta wakilin suna da Babban baki?

* Amsa
Idan a farkon rubutu ne dole ne.

 4- Tambaya
Menene wakilin suna?

 * Amsa
Wakilin suna wata kalma ce mai wakiltar suna. Misali. Ni, ke, kai, Ku, su, mu da sauransu. Wato ana amfani da su a maimakon suna.

5- Tambaya
Karin bayani akan
Daidaitacciuar Hausa.

 * Amsa
Daidaitacciyar Hausa ita ce Hausar da masana suka amince a rika amfani da ita a gidajen rediyo da jaridu da buga litattafai.

 Na yi bayani akwai Zazzaganci, Kananci, Sakkwatanci, Dauranci, Katsinanci, Bausanci, Hadejiyanci.

To duk ba a yarda a yi amfani da su ba a rubutun littafi ko jarida.


Muh'd M. Umar

MACE MAI KAIFIN HARCE

r

SUFFOFIN DA SUKE HANA A AURI MACE.
๐Ÿ Mace mabarnaciya
๐Ÿ Mace mai yawan son ado idan zata fita
๐Ÿ Mace mai yawan fara'a ga kowa
๐Ÿ Mace mai kaifin harshe

ABUBUWAN DA SUKE JAWO LALACEWAR JIKI
๐Ÿ Karanta cin abinci
๐Ÿ Yawaita yin jima'i
๐Ÿ Yawan shiga bandaki
๐Ÿ Bacci bayan magrib

ABUBUWAN DA SUKE JAWO TALAUCHI
๐Ÿ Share daki da sutura
๐Ÿ Cin abinci akan tafin hannu
๐Ÿ Fyace hanci lokacin da ake kashi
๐Ÿ Cire farce da hakori
๐Ÿ Susa da itace

ABUBUWAN DA SUKE JAWO MANTUWAR ZUCIYA
๐Ÿ Yawan maganganu
๐Ÿ Yawan dariya
๐Ÿ Yawan cin abinci
๐Ÿ Cin haramun

LOKUTAN DA AKA FI KARBAR ADDU'OI
๐Ÿ Lokacin kiran sallah
๐Ÿ Lokacin ikama
๐Ÿ Bayan shiga masallaci
๐Ÿ Daren juma'a da yininta
๐Ÿ Lokacin sahur
๐Ÿ kashi uku na karshen dare
๐Ÿ Tsakanin magrib da isha'i

DALILAI DA SUKE HANA KARBAR ADDU'A
๐Ÿ Barin sunnar annabi
๐Ÿ Rashin godiya da ni'imar Allah
๐Ÿ Rashin bada hakkokin ubangiji
๐Ÿ Shagaltuwa da laifukan mutane dss.

HADARIN SON DUNIYA

       

Ibn Kayyim Allah madaukakin sarki yayi masa rahama yana cewa:

๏ปฃ๏บค๏บ ๏บ๏ปŸ๏บช๏ปง๏ปด๏บŽ ๏ปป ๏ปณ๏ปจ๏ป”๏ปš ๏ปฃ๏ปฆ ๏บ›๏ปผ๏บ™ : ๏ปซ๏ปขٍّ ๏ปป๏บฏ๏ปก ، ๏ปญ๏บ—๏ปŒ๏บ ๏บฉ๏บ๏บ‹๏ปข ، ๏ปญ๏บฃ๏บด๏บฎ๏บ“ ๏ปป ๏บ—๏ปจ๏ป˜๏ป€๏ปฒ

Mai son duniya baya rabuwa da abu uku:
1- Damuwa kullum
 2- Gajiya koda yaushe
  3- Nadama wacce bata Qarewa

Wani acikin magabata yana cewa:
๏ป—๏บŽ๏ป ๏บ‘๏ปŒ๏บพ ๏บ๏ปŸ๏บด๏ป ๏ป’ : ๏ปฃ๏ปฆ ๏บƒ๏บฃ๏บ ๏บ๏ปŸ๏บช๏ปง๏ปด๏บŽ ๏ป“๏ป ๏ปด๏ปฎ๏ปƒ๏ปฆ ๏ปง๏ป”๏บด๏ปช ๏ป‹๏ป ๏ปฐ ๏บ—๏บค๏ปค๏ปž ๏บ๏ปŸ๏ปค๏บผ๏บŽ๏บ‹๏บ
Wanda yaso duniya ya suma kansa wurin daukan masifu kala kala.

KA`IDOJIN RUBUTUN HAUSA DA RABEWA DA HADEWANSU


* TASHI DA MANYAN BAKAKE
1. SUNAYEN YANKA MISALI
- Abubakar  ba  abubakar  ba
- Dauda  ba dauda ba.
2. SUNAN ALLAH
- Allah  ba allah ba
- Arrahman ba arrahman ba.

3. SUNAYEN GARURUWA
- Zariya ba zariya
- Bauchi ba bauchi ba.
4. SUNAYEN RANEKU
- Alhamis ba alhamis ba
- Juma'a ba juma'a ba.
5. SUNAYEN MALA'IKU
- Jibril ba jibril ba
- Ridwan ba ridwan ba.
6. SUNAYEN SARAUTU
- Sarki  ba sarki ba
- Galadimi  ba  galadima ba.
7. SUNAYEN WATANNI
- Janairu ba janairu ba
- Febrairu ba febrairu ba.
* AMFANI DA WAKILIN SUNA DA DIRKA.
- AKWAI DIRKA IRI BIYU:
A) NE
B) CE
MISALI:
Ni ne ba nine ba
Ni ce  ba nice ba
Kai ne ba kaine ba
Shi ne ba shine ba
Ita ce ba itace ba
Mu ne ba mune ba
Ku ne ba kune ba
Su ne ba sune ba.
* AMFANI DA WAKILIN SUNA DA AIKATAU
MISALI
Na ci  ba naci ba
Ka ci, ba kaci ba
Kin ci, ba kinci ba
Ya ci, ba yaci ba
Ta ci, ba taci ba.
Mun sha, ba munsha ba
Kun sha, ba kunsha ba
Sun sha, ba sunsha ba.
* AMFANI DA WAKILIN SUNA DA AIKATAU
MISALI
Na yi, ba nayi ba
Ka yi, ba kayi ba
Kin yi, ba kinyi ba
Ta yi, ba tayi ba.
Na je, ba naje ba
Kin je, ba kinje ba
Kun je, ba kunje ba
Sun je, ba sunje ba.
* WAKILIN SUNA DA LAMIRIN LOKACI
MISALI
Ina wasa, ba I na wasa ba
Kana ba ka na
Kina, ba ki na ba
Suna, ba su na na
Tana, ba ta na ba.
* LOKACI SABAU DA WAKILIN SUNA
Nikan je, ba ni kan je ba
Kakan je, ba ka kan je ba
Yakan je, ba ya kan je ba
Takan je, ba ta kan je ba
Kukan je ba Ku kan je ba.
* HARDADDUN KALMOMI
MISALI
- A-Kori-kura ba, akorikura ba
- Babba-da-jaka
- Ba-ji-ba-gani
- Ci-rani
- 'Yan-ba-ni-na-iya
- Fadi-ka-mutu
- Ci-ma-zaune
- Gaya-wa-jini-na-wuce.

HUKUNCIN KYAUTAR BIKIN CHRISTMAS: HALAL KO HARAM?Da yawa Musulmi suna tambayar shin ko yahalatta su karbi kyautar kiristoci a ranar
kirsimeti,
musamman wandanda suke zaune lafiya tare da
su, ko suke aiki a guri daya. Ga bayanin da Malamai suka yi dangane da haka:
1. Baya halatta ga Musulmi ya nuna farincikinsa da wannan ranar, ta hanyar aikawa da gaisuwa ko kyauta ko furanni, ko makamantan su.
2. Ba ya halatta gare shi ya ci abin da aka yanka da sunan wannan rana.
3. Ya halatta ya karbi kyautar da za su bashi a wannan ranar. Kamar yadda ya halatta gare shi ya ci abin da za su ba shi wadanda ba yankawa ake yi ba. Kamar kayan marmari.
* Dalili kuwa shi ne:
A) Baihaqi ya ruwaito a cikin littafinsa As-Sunanul Kubra 9/234 cewa, Muhammad Bn Sirin ya ce: an kawo wa Ali, Allah ya kara yarda a gare shi, kautar idin majusawa Nairuz. Sai ya ce:
  menene wannan kuma? Sai suka ce masa, ya Sarkin
Muminai yau ranar idin Nairuz ce. Sai yace, to kullum ma su yi 'Fairuz'. Wato ya karba, tare da nuna ya ji dadin kyautar.
B) Ibn Abi Shaibah a cikin littafinsa Al-Musannaf
5/126 daga Sahabin nan Abu Barzata Al-Aslamy
cewa: yana da makwabta majusawa, kuma a duk ranar bukukuwansu suna aiko masa da kyaututtuka gidansa, sai yakan cewa iyalinsa, yaya abin yake?; idan kayan marmari ne to ku ci, wanda kuma ba kayan maramari bane, to kumayar musu kayansu.
C) Haka kuma ya ruwaito 5/126 cewa: wata mata ta tambayi Nana A'isha ta ce, muna tare da mata majusawa masu sana'ar shayar da jarirai, to duk ranar idinsu suna aiko mana da kyauta.
       Sai A'isha, Allah ya kara yarda a gareta, ta ce mata, abin da aka yanka domin wannan ranar kada kuci. Ku ci kayan marmari na itatuwa.
* Ibn Taimiyya ya ce, wannan ya nuna idinsu bashi da wani tasiri wajen ya hana a karbi kyautarsu. Karbar kyautarsu a ranar idinsu da ranar da ba idin ba duk hukunci daya ne, domin wannan ba shi ne taimaka musu ba akan aikinsu na kafirci.
    Duba Littafinsa Iqtidha' Siratil Mustaqim 2/52.
* Sannan a karshe Ba ya halatta musulmi ya taimaka da yi musu yanka a wannan ranar. Kuma koda musulmi ne ya yanka musu ba za a ci ba. Allah ka shiryar da mu tafarkinka madaidaici.
Dr. Muhammad Sani Umar R/Lemo
Hey, we've just launched a new custom color Blogger template. You'll like it - https://t.co/quGl87I2PZ
Join Our Newsletter