001-234-567-8910

5th Avenue Madson, NY758, USA

Get Update on our recent Gadgets & Tabs

Add this

Add this

Web Design Agency Nigeria https://www.ads54.com/ad/a/10595_4daf76b52369930

Add this

Website Value Calculator - Domain Worth Estimator - Buy Website For Sales

Add This

Cikekken bayani akan Microsoft wordsDuniyar words part 1

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga ALLAH wanda yace shine wanda ya halitta
muku abinda yake bayan kasa gaba daya.

 Tsira da amincin ALLAH su kara tabbata ga manzon tsira Annabi Muhammadu
S.A.W. wanda yace ku nemi ilimi koda daga Sinne (China) wato Chana.
Bayan haka yauma kamar kullum mun kara zuwa mannan maktabar tamu ta
Shababul Uzzab a karkashin makarantar A'Isha ta haddan Alkur'ani da darussan
musulunci kuma a bangaren cibiyan koyan Komfiuta wato Shawakat Computer
Institute karo na na uku inda muke so muci gaba da silsilolinmu na koyar da ilimin
komfiuta inba a mantaba a karo na farko wato a littafinmu na farko mai taken
Duniyar komfiuta mun yi bayani akan samuwar komfiuta da ire-irenta da kuma
ayyukan kowanne daga cinkinsu sannan kuma muka takaita maudu'inmu akan PC
Computer sannan kuma a littafin mu na biyu mukayi bayani akan Madannai wato
Keyboard sannan kuma muka yi alkawarin cewa zamu yi magana akan abinda ya
shafi manhajar rubutu ta wod wato Microsoft Word kenan a littafinmu na gaba ta
yadda zamu fadi wasu daga cikin muhimman abubuwa na Word sai gashi yau
Allah ya kawo mu wannan lokacin don mu ci gaba a abinda muka yi alkawari
kamar haka:-

Ku kasance tareda mu a rubutun gaba

#Bintubetv

[KUNYA] KONA-GARI SUNA FUSKANTAR HADARI.Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda
yace yaku bayina wadanda sukayi barna ada kada ku
cere tsammani daga rahaman Allah domin Allah ‘yana
gafarta zunubi gaba daya.
 Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga manzon
tsira wanda yace dukkan al’ummata Allah ‘yana
gafarta musu zunubbansu saidai masu futo-na-futo da
Allah.


Bayan haka yauma kamar kullum na shigo wannan
maktabar tamu wanda muka sake mata suna da
shawakat li nashriddiniyyat domin in tunatar da
‘’yan uwa ‘’yan mata kona-gari akan wani abu mai
muhimmanci wanda yake da hadari a rayuwansu wato
shine bakin mutanne don haka ya ku ‘’yan mata ku
matso kusa ku bani aron kunnuwan ku.

 Ya ku ‘yan mata kona-gari ina so in tunatar daku da
wani hadisi guda daya wanda annabi s.a.w. yake cewa
dukkan al’ummata Allah ‘yana musu rangome amma
banda wadanda suke wa Allah da manzonsa da sauran
muminai barambaran.


 Wato sanin cewa babu wanda baya kuskure
a Duniya indai dan Adam ne shi har ni mai
maganan ma wallahi ba mamaki ina da laifinda
gwara wanda nakeyiwa nasiha dinma to amma abinda
Allah yake so shine in kayi laifi ka yarda cewa kayi
laifi sannan kuma kayi istigfari ka koma ga Allah.

sannan kuma ka daina nuna laifinka a zahiri ta yadda
baka jin kunya kowa domin hakan futo-na-fitone da
Allah da manzonsa.
 Don hakanema annabi s.a.w. yace dukkan wanda
yake laifi amma kuma yana jin kunya yana boyewa to
a daina fallasa asirinsa amma kuma dukkan wanda
yake laifi sannan kuma yana fitowa fili baya jin
kunyan kowa annabi s.a.w. yace wannan bashi da wata
alfarma don an fadi laifinsa ko an zagesa.

 A wani
hadisinma annabi s.a.w. yake cewa kunya tana daga
cikin imani a wani hadisin kuma yake cewa indai baka
d a k u n y a t o k a y i a b i n d a k a g a d a m a .

To hadisinda muka kawo da farko cewa annabi yace
dukkan al;ummata ana musu rangome amma banda
masu nuna laifinsu a zahiri sai malamai sukace to me
annabi yake nufi da wannan Magana sai suka bada
amsa kamar haka:-
Da farko sukace saboda dukkan wanda yake nuna
sabon allansa a zahiri to kamar yana fito-na-fito ne da
Allah don haka Allah yake fushi da shi sosai .

Na biyu kuma sukace duk wanda yake nuna sabon
Allansa a zahiri to wasu zasu iya koyan wannan sabon
a wajensa ta yadda koda shi ya tuba ya bari ko ya
mutu duk lokacinda wanda ya koya a wajensa yayi
wani abu sai an rubuta masa zunubi sabod a
s a n a d i y y a n s a a k a k o y a .
Na uku dukkan mai sabon Allah a zahiri zai iya tuba
ko ya manyanta ya bar wannan sabon amma kuma har
yanzu mutane suna kallonsa da hoton abinda ya aikata
a d a d o n y a b a y y a n a a b i n a z a h i r i .

Na hudu, mai sabon Allah a zahiri kamar yana yada
barnace a cikin al’ummar annabi s.a.w. kuma yana
kiran mutane da suzo su aikata wanna abin alhali.
kuma Allah ya fada acikin Alkur’ani cewa dukkkan
wadanda suke so su dinga yada barna a cikin mutane
to suna da azaba mai tsanani a lahira.
Abu na biyar dukkan wanda yake yin sabon Allah a
zahiri to yana haduwa da hadarin bakin mutane da
kambun baka da sauransu saboda bakin mutane yana
da hadari annabi s.a.w. kuma ya tabbatar da hakana
cikin hadisi inda annabi yake cewa bakin mutane da
idon mutane yana kai mutum kabari sannan kuma
yana kai dabba zuwa tukunya.


 Ma’anan hakan shine duk wanda yake nuna wani
abinda yake yi a zahiri musamman ma kuma sabon
Allah a zahiri kowa yana magana akansa sannan ana
kushe masa ana saka masa ido to zai iya rasa
rayuwarsa tun yana kuruciya don haka nema zamuga
hatta annabawa suna gugun bakin mutane da idon
mutane inda zaka fahimci hakan kuma shine annabi
Yakub baban annabi Yusuf lokacinda ya aiki ‘ya’yansa
guda goma sha daya zuwa kasar misra yake ce musu
yaku ‘ya’yana kada ku shiga garin ta hanya daya ku


#Nasiha #Bintunetv
16/03/2019

YADDA ZAKA GANO INDA WAYAN YAKE IN TABATA KO BAYAN SACETA.Assalamu alaikum, once again...
Yau insha Allahu zamuci gaba da darasin mu kaman yadda muka fara a baya, amma bisaga laakari da waauabubuwa mun yanke shawari akan zamu faro daga farkon insha Allahu, darasin namu zai kasance ne akan "Yaad zaka tracking wayanka".

Na'am ba taree da cikaku da dogon surutai ba bari nadanyi bayani gameda darasin namu.

Da farko de zamu irgo amfanin wannan darasin ga al'umma, sa'annan sai mu shiga cikin darasin, sa'annan bayan haka kuma zamu bada lokaci ga masu tambaya insha Allahu.

Yadda ake tracking waya:
wannan darasin namu na kunshe da ilimi kaman haka;

Yadda zaka gano inda aka yi amfani da wayanka na karshe/inda take(in an kunna a lokacin).

Yanda zakagoge wayanka(remotely) in an sacwta sabida tsoro kar a tabama abunda baka so.

Yanda zaka gano IME naka ko da ada baka sani ba koh kwalin wayam ya bata, don kakai ga SSS su bincikama inda takee, don wannan darasin da zamuyi in wayan a kashe takee bazaka gani inda take ba saide inda akayi amfani da jta na karshe kafin a kashe ta.

Da farko de zamu hau browser namu, anan nafi bada shawarin ayi amfani da Chrome, UC browser, FireFox.
Banda Opera Mini(don bazai ma yadda akaeso ba).

Saika danna kan "address bar" ka rubuta wannan link din..

Shiga nan 


1. : Assalamu alaikun

Shin akoi hanyan da mutum zai yi c wayan ne idan ya kasa samu ta wannan tsarin? Godiya muke.


: eh inka danna "Erase Device" zai goge komai na wayan, amma amam ba condemning nata zaiyiba, iyakade ua gogema du wasu anuniwanka daka ajiye a wayan.

2. Q

Shin Meyasa Muke Ganin Wayar Da Muke Amfani Da Ita Alokacin Mafarin Muga Waccce Muke Nema.A: Wa'alaikumus salam, dalili anan shine email(gmail) dakayi login dashi nakan wayan da kake amfani da itane, in yanakan dayan wayan zaka ganshi shima(dayan wayan), kaman haka;

3. : Assalamu Alaikum Oga Ni Abinda Bangane Ba Anan Shine Misali Wayar Da Aka Sace Nakeson Gano Inda Take Amma Kuma Idan Muka Hau Ina Ganin Wacce Muke Amfani Da Ita A Lokacin Itace Dai Ake Nuno Location Da Bayyanan Nata

: Eh wannan, na faruwa ne in an cire email(gmail) naka akan wayan lokacin da aka saceta...

In kuma baa jima da saceta ba, har yakaiga a goge email din, zaka iya bin amsan da muka bawa mai tambaya na sama(kafin kai)

4. Q : Tambaya

Shin idan Wayan da zan Nemo wayana Akwai Gmail na mutumin Aka ya zanyi kenan.


A: Na'am wannan tambayan ban fahimce inda ta dosa ba, don amsoshi biyu nake bama kaina inna tambaye kaina tambayan... Bari na kawosu kaman haka;

- in wayan da aka sace an cire gmail naka, ba halin ka ganota anan.

- in wayan da aka sace gmail na wanine a kanta kuma kuna tare da wannan din, sai kahau Google Find din(kaman yanda muka bada link a sama) saika hau da gmail din wannan din saika bi yadda mukayi bayani a sama.

5. Q: Tambayata

 anan shine idan wanda yasace min wayar yayi mata plashing...dinta sannan yasanya tasa shin xan iya tracking din ta ko shi kenan.A: idan anyi flashing nata, gmail ya sauka kenan..
Ba za'a iya ganota ta wannan hanyan ba, amma inkasan IMEI naka zaka iya kaima SS.

#Bintubetv #Tracking #Email #find

SHIN SU WAYENE MASOYAN ANNABI?
1. Wai su wayene

Masoyan annabi ?

A

Munasabar hafla na ukuNa

Abu Ibrahim baba gana abubakar Muhammad

(Sibawai)

مَكْتَبَــــــةُ شَوَكَتْ لِنَشْرِ الدِّينِيَّاتِ

G.s.m: 08027789545

G.s.m: 07066627321

E mail: sibawai2@gmail.com

Facebook: idris abubakar muhammad

Wazob (whats app)  08027789545BUGAWA: 26-4-1440 hijiriyya

Daidai da 2-1-2019بلغوا عني ولو ءاية2

بسم الله الرحمن الرحيم

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda yace ya kai annabi kace musu indai da gaske kuke son Allah da manzonsa to ku bini (ni annabi s.a.w.) sai Allah ya souk kuma ya gafarta muku zunubbanku.       

     Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga manzon tsira wanda yace dayanku bazai yi cikekken imaniba har sai abinda cuciyansa take so yayi daidai da abinda nazo dashi (na Alkur’ani da Hadisi).                   

                           

 Bayan haka yauma kamar kullum na shigo wannan maktabar tamu wanda muka sake mata suna da shawakat li nashriddiniyyat domin in tunatar da ’yan uwa musulmai game da wani abu mai muhimmanci wato shine matsalan son annabi domin wanda kowa yake ikirarin cewa yana son annabi s.a.w. wanda kowa yake da’wa amma alal hakika in anga aikinmu kuma ba na annabiba kawaidai wani abu mukeyi amma kuma kowa yana cewa shine na annabi dan izala a wajen wa’azinsa ko hafla ko koyarwa sai ya dinga cewa ai mune na annabi wadannan ‘yan darikan su baza su sha ruwan alkausaraba haka kuma shima dan darika sai ya tara mutane a wajen Maulidi ko zikiri yana cewa ai mune na annabi wadancan ‘yan izalan makiya annabine mabiya yahudawane shima dan shi’a sai ya tara mutane a ranar Ashura ko lokacin muzahara sai ya dinga cewa mune masoya annabi da iyalan gidansa sauran mutanenda basa shi’anci duka makiya manzon Allahne kowa yana cewa shine na annabi amma kuma annabi bai tabbatar musu da wannan ikirarinba har sai sunyi aiki kamar yadda wani mawaki yake cewa:-                                                                 

                         

وكُلٌّ يَدَّعِي وَصْلًا بِلَيْلَى ... ولَيْلَى لَا تُقِرُّ لهم بِذَاكَا                                                                                                 

ma’ana: kowa yana cewa shine masoyin Laila amma kuma laila batace tana sonsuba.                                   

     To kamar haka sai kaga kowa yana cewa shine masoyin annabi s.a.w. amma kuma kowa baya son yin aiki irin na annabi s.a.w. din su ‘yan shi’a kam da suka fi kowa baki cewama sukayi ‘yan shi’a sunema kadai ahlussunnah masoyan annabi banda wasu kamar yadda wani kuikuyonsu ya rubuta.                         

                          Don hakanema annabi s.a.w. yace dukkan wanda yake laifi amma kuma yana jin kunya yana boyewa to a daina fallasa asirinsa amma kuma dukkan wanda yake laifi sannan kuma yana fitowa fili baya jin kunyan kowa annabi s.a.w. yace wannan bashi da wata alfarma don an fadi laifinsa ko an zagesa a wani hadisinma annabi s.a.w. yake cewa kunya tana daga cikin imani a wani hadisin kuma yake cewa indai baka da kunya to kayi abinda kaga dama.                             

3

Su kuma mutanen duniya wadanda basu yi karatuba kullum su suna amfanine da abinda yawancin mutane sukeyi koda ba daidaiba don haka sai kaga kullum suna duba yawan mutane da taruwansu misali in anga wasu mutane suna wani abu kuma suna da jama’a shikenan sai ace shine daidai wannan kuma ba hujja bace don hakanema Allah yake cewa:-                           ”وَإِنْ تُطِعْ أَكْثَرَ مَنْ فِي الْأَرْضِ يُضِلُّوكَ عَنْ سَبِيلِ اللَّهِ إِنْ يَتَّبِعُونَ إِلَّا الظَّنَّ وَإِنْ هُمْ إِلَّا يَخْرُصُون“

ma’ana: indai zaka bi yawancin mutanen duniya zasu batar dakai daga barin hanyar Allah saboda babu abinda suke bi sai zato sannan kuma suna kame-kamene kawai (ba bin hanyar Allah sukeba).                  A wata ayarma Allah cewa ya yi:-                             

”وَمَا أَكْثَرُ النَّاسِ وَلَوْ حَرَصْتَ بِمُؤْمِنِينَ“

ma’ana: yawancin mutane basa zama masu imani koda kana kwadayin su zama.     Kunga ashe yawa bashine yake nuna son annabi s.a.w. ko kuma yin daidaiba ya zama dai akwai aiki a wajen masu magana da fada wai ba girin-girinba tayi mai don haka koda kun yaudaru da yawanku da yawan mabiya indai ba aiki to aikin banzane domin wannan matsalan har daluban ilimima suna fadawa a ciki misali irin yadda muke yin hafla a makarantunmu in kace ba daidai bane sai ace yanzu kowa yanayin haka dukkan makarntu suna yi amma kai kace ba daiaiba to kunga su hujjansu shine yawa.                                 

                                               

Wasu kuma sai kaga a baki sunfi kowa son annabi amma kuma inkaga aikinsu suda Benyeme-tanyaho banbancinsu shine musulunci wannanma aikin banzane domin duk lokacinda kace kana son wani amma kuma baka yin abinda yake so to karya kake baka sonsi don hakane wani mawaki yake cewa:-          تَعْصِي الألَه وَأَنْتَ تُظْهِرُ حُبَّهُ ...هَذَا محَالٌ في الْقِيَاسِ بَدِيعُ

لَوْ كانَ حُبُّكَ صَادِقاً لأَطَعْتَهُ ...إنَّ الْمُحِبَّ لِمَنْ يُحِبُّ مُطِيعُ

ma’ana: Kana sabon Allah da manzonsa sannan kuma kace kana sonsu ai wannan abune wanda ba’a taba yin irinsaba indai da gaske kake son Allah da manzonsa da kayi musu biyayya domin duk wanda yake son wani to dole yayi masa biyayya.4

To don haka indai har mutim yace yana son annabi s.a.w. to dole aikinsa yayi daidai da irin na annabi s.a.w. kuma aga yana koyi da masoyinshi misali kamar yadda dayawa daga cikin samari suke zaka ga in yana son wani dan kollon kafa kamar ace Ronaldo ko Mesi ko waninsa sai kaga har rigan jikinsama yafi so ya saka irin na wadancan yahudawan saboda yana sonsu wanima sunansama zai canza daga Muhammadu ko Musa ko Isa ya koma Mesi saboda yana sonsu wani askin kansama sai ya dinga yin irin na wannan dan kollon wannan shine soyayya na gaske.                       

     Haka kuma yadda mata suke yi in suna son wata daga cikin ‘yan shirin hausa sai kaga suna dinki irin nasu kolliya irin nasu saka sutura irin nasu watama har har hotunansu zaka ga suna mannawa a jikin wayansu ko ajikin kwanukansu na talla ko a jikin kobet na daki da sauransu saboda suna sonsu daga baki harzuciya sannan kuma sai kaga dukkan labaran wadannan masoyan nasu sun sanshi kakab zaka ga saurayi yana baka labarin wani dan bol kamar sun zauna agida daya kaji yana cewa an saye shi dala kaza ko yiro kaza sannan yana daukan kaza a kowane wata sannan yana da mata da ‘ya’ya kaza sannan kuma shekarunsa kaza duk wani abinda ya shafesa ya riga ya haddace in kuma matane suma sun haddace dukkan abinda ya shafi masoyansu na shirin hausa sai kaji suna cewa sunanta wance sunan babanta kuma wane amma anfi saninta da wance sannan ita asalinta ‘yar gari kazane ta taba yin aure tana da yara kaza duk ta haddace saboda tana sonta to haka ake so mutum ya san masoyinsa kuma ya zama yana koyi dashi a cikin komai kuma yana son dukkan abinda yake da alaka dashi na suturane ko magana ko wata mu’amala.            To amma sai kaga ana son a saka kayan Ronaldo ko Mesi amma ba’a son na annabi asalima abinda annabi baya so shi mukeyi sai kaga mutum yana sauraron wake-wake da kade-kade sannan ga yawan gulma da karairare ga zalumci ga zamba cikin aminci ga cutan mutane da fada da makobta ga cin bashi ko danne kudin mutane ga algussu a cikin kasuwanci ko tauye mudu da sauranssu amma kuma in aka zo maganar son annabi sai yace ai shima masoyin annabine.                 5

In dan darikane sai kaga yana ta tabka wadannan abubuwanda muka fada dinnan amma in shekarar haifuwar annabi ta zagayo sai yazo yana ta salati yana kuka yana cewa shi masoyin annabi wai annabi zai ceceshi bayan kuma dukkan abinda masoyin nashi ya hana shi din ba bi yake yiba kai abin haushi ko takaicima sai kaga har Maulidinma ba irin yadda magabata daga cikin iyaye da kakanni suke yi sukebiba sai kaga wani abinsu daban sukeyi sai kaga yanzu har anko ake yi akawo DJ ko manyan sifiku a zuba a jikin mota ko amalanke ahada mata da maza waje daya ayi ta cashewa shikenan sai ace wannan shine son annabi daga an gama kuma sai a koma aci gabada sabon Allah ba ji ba gani.                               

                               

     Amma da ace Maulidinma irin yadda iyayenmu da kakanninmu suke yi haka sukeyi da sai ya zama dama-dama wai dan sarki akan jaki domin su mutanen da ba rawa da waka da kida da hayaniya da manna hotuna sukeyiba sudai salatin annabine da da karanta tarihin annabi da mu’ujizozinsa da waken yaba annabi da sauransu sukeyi amma na yanzufa wallahi wani abinsu daban suke yi da sunan son annabi in mutum yana so yaga Maulidi na gaske to shine irin wanda ake yi a gidan shehu kamar yadda kowa yana gani a TV  wannan shine Maulidi na gaske amma irin wanda samari da ‘yan mata ko malaman islamiyya suke a cikin anguwanninnan wallahi ba Maulidi bane ballema ya zama son annabi asalima rusa Maulidin gasken sukeyi amma kuma yawancin malamansu basa fada musu gaskiya sai mutane guda biyune kacal a cikin garinnan wanda suke fadan kura-kuran muridansu sune Sheikh Sheriff Ibrahim Sale wanda na karanta lakcanda yayi akan irin wadannan kura-kuranda muridai suke yi wandama yana cutarda darikarma da kanta sannan sai Sheikh Tijjani Umara shima yana iya kokarinsa in yana wa’azi yaga ya fada musu gaskiya amma kuma basa ji wasuma har zaginsu zaka ji suna yi wai suna goyan bayan ‘yan Izala alhali kuma gaskiya suke fada musu domin Shehu Tijjani da kansama cewa yayi: idan kuka ji ance nace abu kaza to ku godata da Kur’ani da Hadisi in tayi daidai sai kuyi aiki da shi in kuma ta saba sai ku bari karya akayi min to amma ina masu bin maganan shihi din?.                 6

Sannan kuma muma ‘yan izalan wataran muna yin abinda za’ace gwarama dan darikanma saboda zaka ga mutum yana da’awar son annabi da sunnah amma aurensa da sunansa da jana’izansa da mu’amalansa da kasuwancinsa duka ba irin na annabiba iri daya da na ‘yan bidi’an amma kuma sai yace mune masoyan annabi don haka irin wadannan sunema suke bata sunan sunnar annabi dinma ko sunan ‘yan izala alhali kuma su sunyi hannun riga da sunnan da izalan duka  saboda in suka yi barna sai ace ai ‘yan izalanma suna yi ko ace ahlussunnama suna yi saboda su mutane kullum in sunga mutum ya daga wando ya bar gemu yana ashiwaki sai su dauka kawai shine ahlussunnah ko dan izala don haka da zaran yayi laifi sai ace ahlussunnah suni ko yan izala sunyi kuma idan malamai na kwarai masu son sunnan sukayi magana sai su dinga cewa ai shi malan wanenma ai yanzu ya juyawa gaskiya baya ya koma izalan bangare kaza kuma yana magana akan abinda bai saniba kumafa mai fadan hakan shi ba malami bane kawai de gama garin musulmine amma ya dan iya tada baki kuma ya dauki siffar malamai sai kaji yana sakin harce akan malamai kawai don an taba laifinsa wani malamin kuma in ya fada musu gaskiya sai su dinga cewa ai shi malan wanennan dama bashi da fuska yana takurawa mutane yana takurawa dalubai da sauransu to wallahi kuma in dagaske annabin kuke so kuma izalan kuke yi to sai kun yarda da abinda ake fada muku kunyi aiki  domin son annabi aikine ba surutuba kuma bazai yiwu kace kana son annabi sannan kuma baka da banbanci da sauran mutanen gariba kuma ka koma gefe kace wai kaine masoyin annabi su kuma‘yan bidi’a ko ‘yan wuta wallahi wannan ba adalci bane to kowa ya sani cewa son annabi aikine ba cacan bakiba sannan kuma son annabi bai tsaya akan salla da azumi da yin Maulidi da sauransuba dole sai ka bawa annabi s.a.w rayuwarka gaba daya don hakanema                            قُلْ إِنَّ صَلَاتِي وَنُسُكِي وَمَحْيَايَ وَمَمَاتِي لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ Allah yace:

ma’ana sallata da sauran ibaduna da dukkan abinda nakeyi a rayuwata da abinda zan mutu akai duk na Allah ne.to duk wanda yayi haka sine masoyin annabi dan izalane shi ko dan darika ko zauna-gari-banza to anan zan dakata sai Allah ya hadamu a wani karo.                                     

               Wassalamu alaikum                           

 #Bintubetv #History

[AHLUS SUNNAH] SHIN WAYENE AHLUS-SUNNAH?


Wai wayene
Ahlussunnah ?
 A
Munasabar hafla na uku

Na
Abu Ibrahim Baba gana Abubakar Muhammad
(Sibawai)


مكتبة شوكت لنشر الدينيات
G.S.M:- 08027789545
G.S.M:- 07066627321
Email:sibawai2@gmail.com

Bugawa:
25-4-1340
1-1-2019

بلغوا عني ولو ءاية2
بسم الله الرحمن الرحيم
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda yace kuyi aiki domin Allah yana ganin aikinda kuke yi sannan mazansa zai gani da kuma sauran muminai.     
Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga fiyayyen halitta wanda yace duk wanda aikinsa ya jinkirtar dashi shiga aljannah to dangantakansa bazai shigar dashi aljannaba.                             
                                                             
 Bayan haka ina kara yi muku sallama a wannan maktabar tamu wanda muka sake mata suna da maktabatu shawakat li nashriddiniyyat domin gabatar muku da wata ‘yar makala mai taken wai wayene ahlussunnah domin mu rabata a wajen haflanmu na saukan Alkur’ani kuma na zabi wannan maudu’inne saboda irin yadda naga dayawa daga cikin ahlussunnah sun dauka cewa sunnah itace kadai a yanke wando zuwa kwauri a bar gemu a daura hannu akan kirji a cikin sallah a dinga goge baki da ashiwaki a dinga zuwa wajen wa’azi da karatu da sauransu mata kuma sun dauka cewa sunna itace kawai a saka hijabi da nikabi da safa sannan a dinga zuwa makarantun mata Alhamis da Juma’a ko a Asabar da Lahadi shikenan ya isar don haka sai kaga yawancin wadanda suke aikata abubuwanda na lissafa dinnan shikenan sun dauka sune kadai ahlussunnah sauran mutane kuma ‘yan bidi’ane to shine naga ya dace a fadakarda mutane cewa menenema ma’anar sunnan sannan kuma su waye ahlussunnah.                                       
                                                     
     Domin rashin fahimtar ma’anar sunna ta sa sai ka tara ahlussunnah guda dari amma da wuya ka cire ahlussunnah guda goma a cikinsu wannan matsalan kuma ba ta tsaya bane akan mutanenda basu da ilimiba harma ta zarce kan wadanda suke da’awar suna da ilimi ko kuma su daluban ilimine sannan harma da wasu daga cikim malaman islamiyya wadanda babu wanda ya dace yabi sunnan annabi s.a.w. daidai kamarsu amma kuma sai kaga su sunfi kowa nisantar sunna amma kuma sunfi kowa ikirarin sunnantaka aso dayawa zakaga dalubin ilimi yana cewa shi ahlussunnane amma kuma aikinsa sunyi hannun riga a irin aikin ahlussunnah nesa ba kusaba misali
   


3
Zaka ga daluban ilimi masu koyarda mutane a makarantu amma sai kaga sun zauna a majalisa basu da aiki sai gulma da kire da kazafi da sauransu duk inda kaga su biyu zuwa uku sun kebe sai kaga suna magana akan wani ko kuma kaga sun kakkasu kamar gumba biyu anan uku a can hudu a gefe amma kuma kowane bangare maganan daya bangaren sukeyi suna zagin junansu sannan kuma ga karya da yiwa mutane kazafi saboda cimma wata manufarsu sannan kuma ga son yin magana da matan mutane da sunan cewa ai dalubanmune suna karatu a wajenmu ko kuma suce ai mun sansu ko kuma ai matar abokinane da sauransu. 
     Kai akwai wani abin haushi da takaicima wanda naga wasu daga cikin malaman islamiyya wadanda suke kiran kansu da suna ahlussunnah sukeyi shine sai kaga mutum yana yawan maganganu da matan mutane da yawan gaisuwa da kallo mara misali in kayi magana sai yace ai da ni zan aureta tukun Allah baiyiba kuma har yanzu tana sona don itacema take fara yi min magana da sauransu kai wanima jagolgolon nasa yakai harma yana cewa  har yanzu ni ban cire tsammani akan wanceba komi daren dadewa inaga zan aureta saboda mun shaku to amma abinda zai baka mamaki wannan yarinyarfa yanzu haka tana gidan mijinta shi kuma yake fadan haka.                     
     To ni kuma in naji irin wadannan maganganun sai zuciyata ta kusan fashewa don haushi har sai naga cewa na fadi wani abu akan wannan abinda sukeyi  a rubuce ko da baki cikin abinda Allah ya sanar dani da kuma abinda muka ji daga bakin malmanmu kuma da zaran ka fadi wani abu sai suce damu yake yana zaginmu to amma sun manta annabi s.a.w. yace dukkan al’ummarsa masu wa’azine indai har mutum ya kalli abinda bakyau to kodai ya hana karfi da yaji kodai yayi magana da baki kodai yaki abin a zuciyansa to sai ni naga zan iya magana da baki sannan kuma in rubuta da alkalamina to amma da yake su ba sunnanr suke so subiba sai kaga suna cewa ai muma mun san abubuwanda yake fada dinnan duka yau shekara nawa mun karantasu sai abin ya kara bani haushi saboda yace ya karanta amma baya aiki da ita don hakan ni nakan yawan yin gugan zana harma ince musu ai yanzu in ance ka nemo ahlussunna ai dakayar  zakaashawa sukayi wa annabi s.a.w. cewa tunda yanzu 
                                                                         

4
 Ai yanzu in akace ka nemo ahlussunnah zaka sha wahala domin ahlussunnah sunyi karanci sai masu surutu kawai kowa sai cacan baki ba aiki to sai kaga wadannan marasa gaskiyan sai su fara cewa to yanzu ya fara cewa babu ahlussunnah a duniya don haka bari muyi masa wani sharri sai su shiga mitin su fara irin abinda Kuraishawa sukayi wa annabi s.a.w. lokacinda ya damesu da yawan wa’azi suma sai suke gwadawa akaina wani sai yace muce yana zagin gomnati wani yace a’a muce baya son alluran polio wani yace muce yana zagin malamai wani kuma sai yace yana ga hanya mafi sauki tunda yace ba ahlussunnah sai muce to shi meye akidansa wani sai yace ai koko haramne kawai.                                                                   
To ni kuma sai ince:             
                       وَيَمْكُرُونَ وَيَمْكُرُ اللَّهُ وَاللَّهُ خَيْرُ الْمَاكِرِينَ
To don haka yaku ‘yan uwa daluban ilimi wannan abinda kukeyi dinnan bashine mafitaba kawai tunda kuna ikirarin ku ahlussunnane kawai kuyi aikida abinda sunnah ta fada ku daina kwana-kwana sannan kuma ni sai yanzuma nasan kaina waye ni saboda dama annabi s.a.w. yace duk lokacinda kace zaka bi gaskiya sannan ka fadawa mutane gaskiya yace sai ka zama bako a cikinsu sannan kuma sai duniya tayi maka kunci.                         
                                                                   
Don haka kowa ya sani cewa ita sunnah ba suaa bace aikine don haka dole sai da aiki ake zama ahlussunnah ba da sunaba sannan kuma kusani cewa ita kalmar ahlussunnah malamai sukace tana nufin dukkan musulmin duniya izalane shi ko dan darika indai musulmin gaskene sunansa ahlussunnah amma ahlussunnah na gaske wadanda annabi yace sune wadanda zasu kubuta a lahira sune masu bin Alkur’ani da hadisi da maganganun malamai magabata na kwarai don hakane malamai sukace ahlussunnah na gaske yana da wasu abubuwanda kamar haka wadanda suka banbantashi da sauran tarukucen ahlussunnah gasu kamar haka:-                                                       
1-bakonta:
ma’ana indai mutum yace zai bi sunnar annabi sau da kafa sai ya zama bako a cikin mutane domin duk abinda yayi sai aga ya sabawa mutane domin yawancin mane ba sunnar annabi na gasken suke biba. 


5
2- suna tsyawa akan Alkur’ani da hadisi kadai da kuma maganganun sahabbai da malamai magabata na kwarai amma basa aiki da al’ada da kuma mun gani ana yi ko an dade anayi ko malan wane yace ba tare da hujjaba ingacecceba.                                 
                                                                         
3- su mutanene ‘yan tsaka-tsakiya cikin komai abin ibadane ko mu’ama kamar akida da sauran ibadu da kuma aure ko suna da sauransu.                 
                                   
4- basu da wani shehi ko jagora wanda suke daukan dukkan abinda ya fada ba tare da daliliba saidai in maganar annabine sannan kuma ingacacce.                   
5- su suna girmama magabata kamar sahabbai da tabi’ai da sauran malamai magabata kamar malaman fikihu da sauransu indai maganarsu bata ci karau da na annabi s.a.w. ba.                                   
                                                           
6- su kullum suna cikin yin umarni da kyakkawa da kuma hani ga barin mummuna kuma suna tsoratar da mutane game da dukkan abinda zai cutar dasu duniya da lahira.                                                                       

7-su abin koyine ga dukkan mutumin kirki mai son gaskiya hakan kuma suna nunawane a aikinsu don mutane su dauki halaye na gari kamar kyan hali da kyauta da taimakon juna da takaita rayuwa da gudun duniya da sauransu a aikace ba da baki ko wa’aziba.                                                               
8- su suna kwadaitar da musulmai akan hadinkai akan bin gaskiya ba raba kan mutane ana cewa wannan izalan bangare kazane wannan kuma na kazaba.           
9- su basa kafirta mutane don kawai su fuce fushin zuciyarsu saidai da hujja da kuma kafa hujja akan wanda za’a kafirtar dashi.                           
                                       
10- su mutanene masu son dukkan wani ahlussunnah dan uwansu basa munafurtan junansu ko suyi musu kazafi saboda wasu manufarsu na duniya kuma soyayyansu da kiyayyansu duk sunayine don Allah ba don duniyaba ko don burge wani ko samu matsayi ko kusanciba.                               
                                                               
                                         

6
11- suna isar da abinda suka sani ga al’ummar annabi duk karancinsa ta dukkan hanyar da ta dace na wa’zine ko rubutu.                       
                                                           
12- suna yin abinda Allah da manzonsa suka yi umarni matukar zasu iya basa daukan wani su bar wani.         
13- su kuma basa roko saidai bayarwa rokon kuma kowane irine na dabarane ko na zahiri saboda annabi s.a.w. baya son roko kuma ya toratar akan roko sosai. 
14- su suna karatu sannan kuma suna aiki da ilimin ba wai zama suke yi suce munyi karatuba amma kuma ba aiki da karatun.                                           
                                                             
15-su basa maganganun ance-sunce da gulma da kire da kazafi da sakawa mutane ido ana cewa wane yana da kudi amma baya taimako wane kuma baya sadaka  da sauransu su kullum abinda zai amfanesu a lahira ko a duniya sukeyi.                         
16- su ba ‘yan duniya bane basa guduwa a bayan duniya sannan kuma basa auranta saidai su rike duniya  da hannun hagu sai su rike lahiransu da hannun dama ta yadda dukkan abinda zai iya kawo musu cikas a lahiransu zasu iya rabuwa dashi koda kuwa ransune.   
17- su suna hada neman duniya da lahira duka amma suna neman duniyane don gina lahira misali suna neman kudi don su gina addini dashi sannan su gina masallaci makaranta taimakon al’ummar da sauransu sannan suna neman kudi don suyi karatu su taimakawa addini amma basa yin karatu don su samu kudi su gina duniya sannan kuma basa yin karatu don ace musu wane ko a basu wani matsayi da sairansu.                   
To a takaice malamai sukace dukkan ahlussunnanda baya kotanta ire-iren wadannan abubuwan to ba’a ce masa ahlussunnah na kwarai saidai ahlussunnah da ma’anarsa mai fadi.                                                     
To zan takaita anan dukkan wanda yake so ya samu bayanai mai yawa sai ya karanta littafinmu mai taken: إفحام الثرثارين العواطل في خصائص أهل السنة العوامل
Wassalamu alaikum


Contacts us with

Info@bintubetv.com.ng 
                 or
whats..  08165999194
www.bintubetv.com.ng

BLOGGER AN DANNE HAKKIN SHI WAJEN #34.7M A NIGERIA.

Barkan ku da zuwa shafin wayedda kan al-Umma wanda akafi sanida da

                 www.bintubetv.com.ng

Wani blogger yayi aikin kudi na naira miliyan na goga miliyan har na miliyan #34,700,000 aka ki kulashi, balle ma batun biya.

Bazan cika ku da surutu ba zan gabatar da AUDIO  dan ku tabbatar da kan ku.

Malam ba Haushe ya ce waka a bakin mai ita tafi dadi, sabida haka zaku iya latsan link din da dake kasa don saurarun sakon muryan ko saukewa.

Click the following link


http://kiwi6.com/file/7zrohsqx3v


Domin karin bayani ko shawara zaku iya tuttubam mu  a waje kamar haka:
Info@bintubetv.com.ng
www.bintubetv.com.ng

ZOTON DA AKE WA PRESIDENT MUHAMMADU BUHARI YA FARA TABBATA.Hausawa sukace rikicin duniya da mai rai ake yi, yau gashi jirgin a kwana a tashi ya kawo mu zamanin da mutum zai tabbatar abu kamar tatsuniya agaban Ido ko hankali.

Cewa kekkewan fata da zoton al-heri zai fara tabbata lalle hakuri magani ne jama'a. Kar na cika ku da surutu. Mai karatu zai iya leko

Link din nan don saurara ko saukewa

http://k007.kiwi6.com/hotlink/onxfpgc2h2/Zoton_alheri


Ambi dare an kashe wani minister mp3


Barka da zuwa wannan shafimmu mai suna.

 www.bintubetv.com.ng

Domin audio latsa link dake kasa

http://kiwi6.com/file/7zrohsqx3vDUNIYAR COMPUTER (DIGITAL WORLD) PART. 1Shawakat Computer institute بوساحلل تكوش دهعم

Gabatarwa.
ميحرلا نمحرلا الله مسب

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga ALLAH wanda yace shine wanda ya halitta muku abinda yake bayan kasa gaba daya.Tsira da amincin ALLAH su kara tabbata ga manzon tsira Annabi Muhammadu s.a.w. wanda yace ku nemi ilimi koda daga sinne (China) wato Chana.

Bayan haka yauma kamar kullum Allah ya kara dawo dani wannan maktabar tamu mai suna Shababul uzzab a karkashin makarantar A'isha ta haddar Alkur'ani da darussan musulunci domin gabatar da wata 'yar takaitacciyar waraka wanda ta shafi ilimin na'ura mai kwakwalwa (Computer) wato komfiuta don ya zama madogara ga daluban makarantar A'isha saboda muhimmancinda komfiuta (Computer) take dashi a wannan zamanin don haka sai naga ya dace mu dan haskaka musu hanya ta yadda idan suka tafi makarantar gaba baza su sha wahalar fahimtar Computer ba.

To kamar yadda na fada wannan dan takaitaccen littafin zan rubutashine saboda daluban makarantarmu don haka zan takaita abubuwanda zan fada saidai kuma hakan bazai hana indan yi bayani akan wasu abubuwanda zai amfani maso karatun litattafanmuba saboda a baya mun saba muna gabatarda wasu takardu ga 'yan uwa musulmai game da abubuwanda ya shafi addininmu na musulunci da kuma wasu abubuwan fadakarwa wadanda zasu amfani samari da kuma iyaye mata saidai kuma a wannan karo zamu yi sabon salo wai shafa kolli da tabarya don haka kar mai karatu ya fahimci cewa zamu takaitane akan dalubanmu kadai A'a hakan bazai hana mu fadi abinda zai shafi sauran masoya sanin ilimin komfiutaba (Computer) amma a takaice saboda lura da shekarun dalubai Allah yayi mana jagora amin.
Kuma zan rubuta wannan littafinne da harshen hausa amma kuma saidai zan fassara sunan wasu abubuwa da yaren larabci da turanci amma dai zan farane da hausa sannan sai Larabci sai kuma turanci saboda ina so dalubanda nayi wannan littafin dominsu su fahimci komfiuta (Computer) da harcen larabci da kuma hausa saboda shi turanci duk inda kaje za kayi karatun komfiuta (Computer) dashi ake amfani don haka ni zan so in baiwa larabci da hausa muhimmanci anan haka kuma zan kasa wannan littafin nana kashi daban-daban saboda sawwakawa.

Muhadu a zongo na biyu.

#Fasahar Zamani. 

BAMBANCIN DESKTOP, LAPTOP & NOTEBOOK.

Duniyar computer (digital world) part. 7

Sannan kuma abaya munyi magana akan bambanci tsakanin Laptop da Notebook yanzu kuma zamu fadi bambanci guda daya wanda ya rage tsakanin Laptop da Desktop da Notebook domin akansune maudu'inmu zai takaita ga bambancin kamar haka:-

Shi Laptop yana aiki da batir don haka ba'a saka shi a wuta kai tsaye saidai ayi amfani da Chaja (Charger) sai ayi masa cahji kamar yadda akeyiwa wayar hannu in ya cika sai a cire in kuma baya rike chaji saboda raunin batir sai a canza masa sabon batir ko kuma a dinga yin amfani da chajan nasa kai tsaye amma da zaran an ciresa daga wuta shikenan sai ya mutu ga kuma yadda

Chajan   nashi yake kamar haka:-
Chaja (Charger).Sannan kuma ana iya yi masa cahji da External Battery

(Batir din waje) ko kuma Power Bank (Bankin wuta) kamar haka:-Laptop External Battery Laptop Power Banksannan shi kuma Notebook baya zuwa da CD Drive saidai ayi amfani da External CD Drive (ma'ana gidan CD na gefe) a yayinda ake so ayi masa Formatting wato (kwaskorima) ko kuma a kofi wani abu zuwa kan faifan CD ko ayi kallo akan CD da sauransu ga kuma yadda External CD Drive din yake kamar haka:-External CD Drive


Amma shi Desktop yana aiki da wutane kai tsaye ba tare da an saka masa Chajaba sannan kuma shi baya yin chaji kawai ana dauke wuta zai mutu saidai kuma shima yana da wani abu wanda ake kira da suna UPS wanda yake yin aikinda batir yake yi amma saidai baya dadewa kamar yadda batir din Laptop yake dadewa saboda rashin karfinsa domin anyisane kadai don ya baiwa mai amfani da komfiuta daman adana abinda yake yi ko rubutunsa sannan ya kashe Komfiuta cikin natsuwa don hakane da zaran an dauke wuta sai kaji wannan abin wato UPS ya fara kara don ya nuna maka cewa an dauke wuta ko kuma an taba wutan sai kayi gaggawa ka kashe Komfiuta ga abin kuma kamar haka:-UPSBambanci na karshe shine shi Laptop dukkan kayakinsa ma'ana Input da Output da Storage divices da CPU duka a hade yake a waje daya sabanin Desktop wanda komansa a rabe yake kai zaka hadasu ka jona kamar yadda za ka

gani a wannan hoton na kasa:-
Tarkacen Desktop


LaptopTo a karshe kuma ga yadda rabe-raben Komfiuta take kamar yadda muka bayyana a sama:-


Computer ta bangaren aikinta

ta kasu kahi ukuDigital Computer.

Analoge  Computer.

Hybrid Computer.
Computer

ta bangaren manufar da akayi ta don shi ta kasu kashi biyu


1) General  Purpose.

2) Special Purpose.
ta bangaren girmanta ta kasu kashi biyar1. Super Computer.

2. Main Computer.

3. Control Computer.

4. Mini Computer.

5. Micro Computer.Frames Computerkuma ta kasu kamar haka:* Desktop Computer.

* Laptop Computer.

* Notebook Computer.

* Palmtop Computer.

* Tablet Computer.

 
  Sai mun hadu a wata gaban


#fasaharzamani #Duniyarcomputer #bintubetv

CPU, YADDA COMPUTER TAKE AMFANIDA QWAQWALWARTA.

Duniyar computer (digital era) part 18.

4) Na hudu Qwaqwalwar komfiuta

Kwakwalwar Komfiuta wato CPU (Central Processing Unit) itace wannan akwatin da ake ajiyeta a gefen Allon talbijin din Komfiuta indai Towaer ce In kuma Desktop ce ana ajiyetane a karkashin Allon talbiji saidai kuma shi wannan sunan asali an arawa wannan akwatinne amma alal hakika ba sunansa bane sunan wata na'urace 'yar karama daga cikin wannan akwatin akan Mother Board (wato Allon asali) ita wannan na'uran ita ake kira da suna froseso (processor) wanda kuma dukkan ayyukanda Komfiuta take yi tana dogarane akan wannan dan na'uran saidai kuma itama girma-girmace akwai mai sauri sosai akwai kuma mara sauri gorgodon tsadan Komfiutar da ka saya sannan kuma ana gane karfin wannan na'uran da saurinsane da ma'aunin Mhz (Mega Hartz) sannan kuma tana aiki da memorin Kech wato (Cache Momery) wanda take taimaka mata wajen yin aiki in su biyunnan suka yi karfi sai Komfiuta ma tayi sauri.


Ga kuma hoton shi CPU da wannan Na'uran da muka fada wato (Processor) suke kamar haka:-
CPUiwannan shine akwatinda yake dauke da CPU a cikinsa don haka ake kiransa

da  sunan  mafi  girman  abinda  yake  cikinsa  shine  CPU  wato  (processor).


Sannan kuma ga yadda hoton  Processor yake:-Processor

to ina ga cewa anan ya kamata in dakata saboda abinda muka fada a farko cewa zamu rubuta littafinne saboda koyarda yara a makarantar islamiyya don haka baza mu fadadaba sannan kuma munce zamu lura da irin shekarunsu don haka zamu katse annan sai Allah ya hadamu a littafinmu na gaba wanda zamu yi muku bayani a akan abinda ya shafi madannai wato keyboard kafin mu shiga yin bayani akan manhajar Microsoft Office wato manhajar koyan rubutu a Komfiuta domin babu yadda za'ayi mutum ya iya yin rubutu a Komfiuta alhali bai san yadda ake amfani da maballanda suke jikin madanni ba sannan kuma yawancin madannanda muke amfani dasu babu Larabci a jiki sai Turanci don haka zanso in fadi dukkan abinda ya shafi yin amfani da madanni don a rubuta Larabci amma hakan bazai hana muyi bayanin na Turancinba don haka sai ku jiramu a littafinmu na gaba inda za muyi muku bayani akan abinda ya shafi madanni da kuma yadda za kayi rubutu da Larabci da Turanci duka koda kuwa babu Larabci a jikin madannan Komfiutarda kake amfani da ita sannan kuma a fada maka amfanin dukkan maballanda suke jikin madanni in sha Allahu haka kuma a fada maka yadda zaka dauki gajerar hanya wato (Short-Cut) a yayinda kake rubutu domin a saukaka maka bin doguwar hanya.


sannan kuma ina tawassali da wannan aikinda nayi indai don amfanar Al'ummar annabi s.a.w. nayi Allah ya karamin ilimi mai albarka wanda zanci gaba da dubbunnan irin wannan aikin sannan kuma Allah ya bani tsawon rai da lafiyan jiki da abinda lafiyan zataci don in dade inayi sannan kuma Allah ya gafartawa mahaifina da kuma dukkan wanda ya koyar dani wata kalma mai amfani sannan kuma ina tawassali da wannan aikin Allah ya biyawa dukkan wanda ya nemi addu'a ta alkhairi a wajena bukatunsa na alkhairi amin.na fara rubuta wannan littafin a ranar goma ga watan safar sannan 10-2-1438 kuma na gama a ranar 22-2-1438 na hijiriyya.Wassalamu alaikum

Sai mun hadula a tafinmumumuu na gaba.

#Bintubetv #Duniyarcomputer #Fasaharzamani .

YADDA AKE AMFANIDA CARD READER (KAD-RIDA)
Duniyar computer digital era part 17

http://kiwi6.com/file/otn8020495

Card-Reader (kad-rida)

To ganin cewa muna da Memori-kad din waya iri daban-daban dolene mai son tura abu daga cikin Komfiuta zuwa memori ko kuma daga memori zuwa cikin Komfiuta ya zama yana da Kad-rida mai daukan dukkan nau'ukan memori inba hakaba watarana zai iya gamuwa da memorinda bazai iya shiga jikin irin kad-ridanda yawancin masu Komfiuta suke amfani dashiba don haka yana da kyau ya zama ka mallaki molti in wan memori kad rida (Multi in One Memory Card Reader) kamar yadda muka nuna hotonsa a sama don kusanto da nesa.

Jan hankali

Ya kai mai karatu ko mai koyan Komfiuta ka ji tsoron Allah kar kayi amfani da wannan damar na koyan tura abu daga Komfiuta zuwa memori ko kuma daga memori zuwa Komfiuta kaje ka tura waka ko Fina-finan batsa domin wannnan hanyar ba karamin hadari bane a gareka da ka dauki wannan hanyar a matsayin sana'a wallahi gwara ka zauna babu sana'a domin duk wanda ka tura masa waka ko fina-finan batsa ko dukkan wani abinda zai taba addinin mutum koda ka bar duniya wato ka mutu wannan abinda ka tura din zunubinsa yana binka haka kuma duk wanda ya saurari wannan wakar ko fimdin koda sunkai dubu sai an baka naka rabon na zunubi kamar yadda suma suka samu inji annabi S.A.W. don haka indai annabi kake bi to karka dauki wannan hanyar.

A karshe kuma akwai hanyar tura bayanai ko kuma daukar bayana ta hanyar Internet wato yanar gizo-gizo ta yadda mutum zai yi amfani da modem wanda yake da memori a jikinsa bayan ya jonata a jikin Komfiuta zai dinga ajiye dukkan bayananda ya samo akan Internet a cikin memorin don yayi amfani da ita a wani lokaci haka kuma zai iya tura abinda yake cikin memorin modem din zuwa kan Internet in yana son yin hakan to amma ganin cewa wannan ba maudu'inmu bane zan bar wannan bayanin sai lokacinda Allah ya kaimu yin bayani akan Internet a wani littafin daban sai mu fadada in sha Allahu ta'ala ga.


kuma yadda hoton modem yake  kamar haka:-#Bintubetv #fasaharzamani #Duniyarcomputer ?

Amfnin flash memori (Flash Memory)

Duniyar computer (digital era) part 16

Amfnin flash memori (Flash Memory)

Shi flash memori kuma ana amfani da shine a jona a jikin Komfiuta don a tura wasu bayanai daga cikin Komfiuta zuwa cikinsa don a ajiye koda watarana za'a nemi wadannan bayanan ko kuma ana amfani dashi don a kofi wani abu daga cikin wata Komfiuta zuwa wata itama tana da amfani matuka saidai kuma tana iya daukan cutan Komfiuta daga Komfiuta mara lafiya zuwa mai lafiya kuma duk lokacinta kwayar cutan bairos ya shiga cikin flash yana iya bata abubuwanda yake ciki.

Sannan kuma shi Flash Memory yana baciwa idan har ba'a bin ka'idar amfani da ita misali idan aka sakata a jikin Komfiuta aka tura wasu abubuwa ko kuma aka kofa daga cikinta ba'a yarda a cireta daga jikin Komfiutaba har sai Komfiuta ta bada daman cirewa yadda Komfiuta zata bada daman cirewan kuma shine kamar j:-

Zaka je kan Task bar (sandan ayyuka) 

Sannan sai ka dannan wannan alamar 

Sai ya nuna maka haka 

Daga nan sai ka dannan

Ko kuma zai nuna maka sunayen ma'aiyoyi masu yawa sai ka dannan wanda kake so daga ciki sai ya fitar daga jikin komfiutar sannan sai ka zare kayanka.Ko kuma ga hanya ta biyu kamar haka:Shi kuma zaka tafi mai Komfiuta (My Computer) sai kaje kan ma'jiyar da kake so ka zare sai ka danna maballin gefen daman (Rigth Click) a dan bera sai ya nuna maka wani Allon bada zabi sai ka danna fitarwa (Eject) sai ya fitar maka amma shi wannan hotonda kuke gani a sama na Komfuitar Larabcine saidai babu bambanci da na Turanci duka saidai yare kawai sannan kuma na daukone a Windowss Xp.Fadakkarwa

Akwai lokacinda zaki bi wadannan hanyoyin duka amma kuma Komfiuta taki bada dama a cire ma'ajiyar da take jikinta to a wannan yanayin dole a kashe Komfiuta ta hanyar dannan maballin kashewa kai tsaye saboda a cire wannan ma'ajiyar inba haka ba za'a iya samun matsalar lalacewar ma'ajiya matukar Komfiuta bata bada dammar cirewaba abinda yake kawo rashin amincewar Komfiuta a cire ma'ajiya a jikinta kuma shine samuwar bairos a cikin ma'ajiyar ko kuma a jikin Komfiuta kokuma rashin yin saurin Komfiuta ta yadda bazai bada umrani da wuri a cireba.Sannan itama ma'ajiyar Flash Memori tanada girma gorgodon kudinta da tsadanta domin ana samun mai Gig um m----------har zuwa 256 sabanin ma'ajiyar Floppy Disk wanda baya wuce mega byte uku kachal.
A karshe kuma akwai hanyar da mutum zai dauki bayanai a cikin Komfiuta.

ko ya tura zuwa cikin Komfiuta ta hanyar yin amfani da memorin wayar Salula amma ita wannan hi.


#Bintubetv  #Duniyarcomputer #fasaharzamani 

[Computer] Yaya ake amfani da External CD-ROM.

Duniyar computer (digital wold) part.15

Na uku itace ma'ajiyar Blu-Ray:-

Ita wannan ma'jiyar tafi kowace ma'ajiya daga cikin ma'ajiyoyi guda ukunda muka fada a sama daukan kayaki mai yawa da karfi da inganci da kuma sauri da dadewa amma saidai ba akasaifai ake samuntaba saboda itace sabuwar fita wato na zamani don haka ba a ko ina ake samuntaba sannan kuma tana da tsada haka kuma bata kunnuwa a cikin Komfiutocin da sai na yayi kamar yadda ma'ajiyar DVD bata kunnuwa a cikin wasu Komfiutocin don haka mai karatu bazai iya mu'amala da wannan ma'ajiyarba har sai ya shirya amma da za'a samu wannan majiyar da tafi kowane daga cikin ukun da yafi saboda ita wannan ma'jiyar tana iya daukan kayanda nauyinsu yakai gig dari (100) don haka zai taimaka wajen ajiya matuka indai ana da daman samu.

To wadannan sune abinda ake nufi da ma'ajiya Curarriya kamar yadda muka sa mata suna da hausa wanda kuma ake kira da suna CD-ROM da DVD-ROM da Blu-Ray da ire-irensu kamar yadda kuka kalli hotunansu a sama da kuma amfaninsu don haka anan zamu dakata don mu wuce wani bangaren daban.Fadakarwa

Mai karatu ka san cewa idan Komfiuta bata da makunnin DVD to babu yadda za ayi kayi amfani da ma'jiyar DVD haka kuma idan Komfiuta bata da makunnin Blu-Ray ba yadda za'ayi kayi amfani da ma'ajiyar Blu-Ray haka kuma koda Komfiuta tana da ma'jiyar DVD ko Blu-ray to ba yadda za'ayi ka iya kofan bayanai daga cikin Komfiuta ka daura akan ma'ajiyoyinnan guda uku har sai makunnin naka ya kasance yana iya karantawa sannan kuma ya rubuta saboda a ilimin Komfiuta akwai abinda ake cewa karantawa da kuma rubutawa to dole sai Komfiuta ta kasance tana iya yin biyun duka kafin ka ajiye kayanka a wadannan ma'ajiyoyin in kuma Komfiuta bata dashi sai ka samu makunnin waje wato External-Drive kenan a turance wanda aka fi sani da suna External CD/DVD ROM don tayi maka wannan aiki ita kuma ana jonatane a jikin Komfiuta sai a saka ma'ajiyar a ciki ga hotonta kamar haka:-                         External CD-ROM

#Fasaharzamani #Bintubetv #Duniyarcomputer

[Computer] Amfanin ma'ajiya curarriya (CD ROM & DVD ROM).


Duniyar computer (digital wold) part. 15

Amfanin ma'ajiya curarriya

Ita ma'ajiya Curarriya ta kasu kashi uku:-
CD ROM.

DVD ROM. 

Blu-Ray.

Na farko ita ma'ajiyar ajiya ta CD-ROM  ko CD-R itama ta kasu kashi biyu:-

1-Akwai CD-R.

2-Akwai CD-RW.

Bambancinda yake tsakanin wadannan nau'ukan guda biyu kuma shine shi CD-R zaka tsaye shine babu koma a cikinsa sai ka tura dukkan abubuwanda kakeso daga Komfiuta zuwa gareshi don ka ajiye zuwa watarana idan na Komfiutarka ta samu matsala sai ka dauko na CD-R dinka ka saka mata ko kuma zaka kofi wani abu daka Komfiutarka don ka baiwa wani da sauransu amma bayan an saka mata abu ba'a iya gogeta ko a kara da zaran ka gama ka cireta a Komfiuta shikenan ba yadda za'ayi a sake saka mata wani abu ko a goge abinda ke cikinta.

Na biyu wato CD-RW shi ana iya saka mata abu sannan kuma ana iya goge abinda yake cikinta don a saka wani wannan shine bambancinda yake tsakaninsu to amma kudinsu dabanne saboda amfaninsu ya bambanta shi na biyun yafi tsada.

Sannan kuma ita ma'ajiyar CD-ROM ko CD-R iri biyu duka suna iya daukan kaya wanda yawansu zai kai mega byte700 wato kusan Gig daya kenan.

Haka kuma ita ma'ajiyar DVD-ROM itama ta kasu kashi biyar:-

1- DVD-R

 2- DVD+R

3- DVD-WR

4- DVD+WR

5- DVD RAM

Bambancinda ke tsakaninsu kuma sune kamar haka:-

Shi Ma'jiyar DVD-ROM ko DVD-R ana iya sayansa haka babu komai a cikinsa don a zuba masa bayanai daga cikin Komfiuta a ajiye ko a saka a wata Komfiuta amma da zaran an saka mata abu ba'a iya gogeta ko a kara wata ana amfani da itane ta wajen tura abu sau daya kawai.


Itama ma'jiyar DVD+R haka take kamar na farkon amma bambancinsu shine shi wannan ma'ajiyar ta DVD+R tafi ta DVD-R kyau da inganci ta wajen tura abu ko kofan abu.
Sannan kuma ita ma'ajiyar DVD-RW ita tana iya daukan abu ta ajiye haka kuma ana iya goge abinda yake cikinta don a sake saka wani kamar yadda ake wa memori.
Haka itama m'ajiyar DVD+RW itam aikinta daya da na DVD-RW amma saidai wannan tafi ta saman sauri da kuma wasu 'yan bambance-bambance ammadai bambancin bashi da wani muhimmanci mai yawa.


Na akrshe daga cikin nau'ukan ma'jiyar DVD shine DVD-RAM shi kuma yafi kowanne daga cikin ma'ajiyoyin DVD inganci saboda shi yana da sauri sosai sannan kuma aikinsa ya sha bamban da sauran nau'ukan sannan kuma

ana iya saka masa abubuwa sannan a goge har sau 100,000 dubu dari sabanin sauran DVD wanda in aka gegesu sau 1000 dubu ko sama da haka kadan shikenan zasu daina aiki amma kuma shi wannan na karshen yafi kowanne tsada da kuma wahalan samu.To amma mai karatu ya san cewa dukkannin nau'ukan ma'ajiyar DVD guda biyar da muka fada suna da kayu ta wajen ajiye abu saboda suna iya ajiye maka abinda yake cikinsu tsawon shekara talatin 30 ba tareda sun samu matsalaba haka kuma suna iya ajiye maka kaya wajen kusan gig biyar akwaima wanda yake iya daukan gig takos ko tara sannan kuma cutan bairos baya iya yi musu komai balle ya bata maka abinda yake ciki.
Fadakarwa

Saidai kuma su ma'ajiyoyin CD ko DVD basa son a taba fuskarsu da abu mai kaushi ko a ajiyesu a inda ruwa zai taba ko zafi mara misali ko goguwa da juna don haka indai kana so kayanda ka ajiye a ciki ya dade har tsawon wannan shekarun dole sai ka bi wadannan ka'idojin da kamfani ya fada.

#Duniyarcomputer #Fasaharzamani #Bintubetv.

[Computer] Ma'ajiyar Flash حيضييىنا جشكازنا Flash Memory.


Duniyar computer (digital wold) part. 14

Ma'ajiya ta biyu

Ma'ajiya ta biyu kuma sune ma'ajiyoyin Komfiuta wadanda ake iya sakawa a jikin Komfiuta ko kuma a cire sannan ana iya goge abubuwanda yake cikinsu in anga daman hakan su kuma sune kamar haka:-Hausa Larabci Turanci:


Ma'ajiya mai karfi حثهصنا نيزختنا جذحو      Hard Dick


Ma'ajiya mara karfi حنشًنا نيزختنا جذحو    Floppy Disk.


Ma'ajiya Curarriya حديذًنا نيزختنا جذحو       CD ROM.

Ma'ajiyar Flash حيضييىنا جشكازنا      Flash MemoryTo wadannan sune abubuwanda ake kira da suna ma'ajiya ta biyu kamar yadda kuka ga hotunansu a sama yanzu kuma sai muji yadda ake amfani dasu kamar haka:-Amfanin ma'ajiya mai karfi

Ita ma'ajiya mai karfi itace babban abinda Komfiuta take dogaro dashi wajen ajiye dukkan abubuwanda aka saka a cikin Komfiuta gorgodon girmanta gorgodon yadda Komfiuta zata dauki abubuwa masu yawa saidai kuma a sani cewa koda wannan ma'ajiyar tana da girma indai RAM bata da girma to akwai abubuwanda baza a iya sakasu a cikin Komfiutaba kamar wasu daga cikin Softwere amma indai ajiyane kake so kayi a cikin Komfiuta kamar ajiyan karatuttuka da wa'azi da kayan kallo da sauran bayanai masu amfani to dole ka bukaci wannan ma'ajiyar tayi girma.


Haka kuma girman wannan ma'ajiyar tana farawane daga GB (giga byte) 8-

har zuwa GB dubu biyu ana samun Komfiuta mai gig 8,20,40,80,120,160,250,320,500,640,750,1000,2000 wato Terabyte biyu kenan a ma'aunin ma'ajiyar Komfiuta.

Amma a sani cewa duk lokacinda girman wannan ma'ajiyar tayi yawa

dole kudin Komfiutama ta karu amma kuma ana iya cire wannan ma'ajiyar a saka wata wanda ta fita girma in aka bukaci hakan kamar yadda ake yi wa wayar hannu.
Amfanin ma'ajiya mara karfi wato (Floppy Disk)


Ita ma'ajiya mara karfi ana amfani da itane a da lokacinda ba' samu ci gaba kamar na yanzuba kuma ita amfi amfani da itane a Komfiutocin kan tebur da kuma wasu daga cikin Komfiutar tafi da gidanka kiran da amma yanzu an maye gurbinta da CD ko DVD ko Flash Memory ko Blu-ray saboda su wadannan ma'ajiyoyin suna dauka abubuwa masu yawa amma ma'ajiya mara karfi bata wuce wasu mega byte (Mega byte) 'yan kadan.#Fasaharzamani #Bintubetv #Duniyarcomputer.

[Computer] Bambanci tsakanin ma'ajiyar ROM da RAM.


Duniyar computer (digital wold) part. 14

To anan zan dakata game da abinda ya shafi na'urorin fitarwa sai mu wuce gaba domin jin bayani gameda na'urorin ajiya wato (storage devices) kamar haka:-
Na uku na'urorin ajiya

Abinda ake nufi da na'urorin ajiya kuma sune dukkan abubuwanda ake amfani a dasu don a ajiye bayanai ko murya ko kayan kallo da sauransu a cikin Komfiuta wadannan ma'ajiyan kuma akwai wadanda suke zuwa tare da Komfiuta akwai kuma wadanda ake jonawa a jikin Komfiuta daga baya gasu kamar haka:-

Wadannan ma'ajiyan kuma sun kasu kashi biyu:-


Hausa
larabci
Turanci

1.
Akwai ma'ajiyar ainihi.
حيسيئشنا جشكازنا
main memory

2.
Akwai ma'ajiya ta biyu.
حيىناثنا جشكازنا
Secondary memoryMa'ajiya na ainihi sune kamar haka:-

Hausa larabci turanci:


Ma'ajiyar dindindin.   حًئاذنا نيزختنا جذحو Rom


Ma'ajiyar lokaci kadan حيئاىشعنا نيزختنا جذحو Ram
To wadannan sune ake kira da suna ma'ajiyar ainihi abinda yasa ake kiransu da suna ma'ajiyar ainihi kuma shine su wadannan ma'ajiya guda biyu in babu su ba yadda za'ayi Komfiuta tayi aiki ko ta kunnu domin ita ROM a cikintane aka ajiye dukkan abubuwanda suke kunna Komfiuta wanda kuma kamfaninda ta kera Komfiuta ita take sakawa don haka ba yadda za'ayi ka goge wani abu a cikinta ko ka kara sannan kuma ita ba'a canzata.


Amma ita ma'ajiyar RAM ana iya canzata a saka babba ko karami ko a kara wata akan na ciki.

Bambanci tsakanin ma'ajiyar ROM da RAM


Ita ma'ajiyar ROM abubuwanda yake cikinta baya goguwa koda an kashe Komfiuta ko ta dauke sannan kuma tana amfanine da abinda kamfani ya saka mata don ta kunna Komfiuta ta fara aiki amma ita ma'ajiyar RAM abubuwanda suke cikinta suna goguwa da zaran an kashe Komfiuta ko ta dauke don hakanema ake kirantan da suna ma'ajiyar lokaci kadan sannan kuma ita RAM ita take saka Komfiuta yin sauri don haka gorgodon yadda ma'ajiyar RAM take da girma gorgodon yadda Komfiuta zata yi sauri ta wajen kunnuwa ko yin kowane aiki.

Fadakarwa

Saidai kuma akwai abinda ake cewa froseso (Processor) inhar wannan froseso bashi da sauri ko girma to koda ma'ajiyar RAM tana da girma to Komfiuta baza ta dinga yin aiki da sauri kamar yadda ake soba don haka koda ma'ajiyar RAM tayi girma to dole froseso ma yayi girma kafin Komfiuta tayi saurinda ake bukata.


#Bintubetv #Duniyarcomputer #Fasaharzamani

[Computer] Na biyu Na'urorin fitarwa (output devices).

Duniyar computer (digital wold) part. 13

Na biyu Na'urorin fitarwa

Su kuma na'urorin fitarwa kamar yadda muka fada a baya sune abubuwanda ake fitar da bayananda aka saka cikin Komfiuta ta hanyarsu su kuma sune kamar haka:-1. Allon talbijin   حشاشنا Monitor.2. Lasifika   خىصنا خاشثكي   loud-speaker.3. Mabugar takardu حعتاطنا      Printer.To wadannan sune na'urorin fitarwa da hotunansu wadanda ake amfani dasu wajen fitar da bayanai daga cikin Komfiuta yanzu kuma sai mu ji

yadda ake amfani dasu kamar haka:-
Amfanin allon talbijin.

Shi Allon talbijin wato (Monitor) da shine ake amfani don kallon dukkan abubuwanda aka shigar cikin Komfiuta ko kuma ake shigarwa ita amfaninta da tibi kusan dayane saboda ana iya kallon tibi ma da shi akwai maballai na rage murya da karawa a jikinsa da kuma yadda za'a rage launi ko a kara da kara haske ko duhu amma shi wannan Allon talbijindin yana da nau'uka biyu .


1-Akwai Allon talbijin mai suna CRT


2-  Akwai kuma Allon talbijin mai suna LCD
Bambancinda yake tsakanin wadannan nau'ukan kuma shine shi Allon talbijin na na CRT ya zama tsohon yayi saboda shi ana amfani da shine a da sannan kuma shi yana cin waje dayawa ga kuma nauyi ga kuma jan wuta sosai don yana iya cin watt 160 na wuta sannan kuma baya amfani da wutan DC sai AC wato in babu wutan lantarki bazai iya kunnuwaba sannan kuma shi yana daukan zafi kuma sannan bashi da kyan hoto sosai da sauransu.
Amma shi Allon talbijin na LCD yana  da kyan nuna  hoto gashi kuma baya daukan zafi sosai kuma yana iya kunnuwa da DC wato wutan batir sannan kuma baya cin waje sosai haka kuma baya jan wuta sosai domin duk jan wutansa baya wuce watta 40 na wuta sannan kuma yana da amfani dayawa sabanin CRT saidai kuma wannan Allon na LCD yafi na CRT tsada sosai.
Amma ta wajen amfani dukkansu biyu ana iya kallon tibi ko dish dasu sannan kuma ana iya hadasu da Komfiutar tafi da gidanka domin ayi amfani dasu a matsayin Allon Komfiutar tafi da gidanka to wannan shine abinda zan iya fada gameda Allon talbijin na CRT da kuma LCD.
Amfanin lasifika

Lasifika kuma amfaninta a jikin Komfiuta itace fitar da murya saboda yawancin Komfitocin da ake amfani dasu a da babu sifika a jikinsu don haka duk lokacinda mai amfani da Komfiuta yake so ya saurari karatun Alkur'ani ko ya ji wa'azi ko yayi kallo a cikin Komfiuta dole sai ya bukaci Lasifika don yaji murya.

Haka kuma ana amfani da Lasifika wajen kara murya ko ragewa saboda wasu daga cikin Komfitoci basu da murya sosai musammanma kamar Komfiutar tafi da gidanka wanda ake kira da suna NoteBook saboda ita bata da murya sosai domin tana amfanine da batir sannan kuma sifikunsa kananane sosai don haka in mai amfani dashi ya bukaci jin karatu ko kallo to dole zai ya bukaci Lasifika ya jona mata.Amfanin mabugar takardu

Ita kuma mabugar takardu wato (Printer) ana amfani da itane ta wajen fitarda dukkan abubuwanda aka rubuta a cikin Komfiuta ko aka zana ko kuma wani abinda aka samo daga kan yanar gizo-gizo ko kuma wani sakonda aka aikowa mutum a hanyar E-Mail da sauran abubuwanda ake so a fitar dashi a rubuce ko a zane saidai kuma ana saka fallen takarda a cikin mabugar takardu kafin ta cire rubutacciyar takardan sannan kuma wani nau'in mabugar takardun ana zuba mata tawadanta wato Ink na baki-da-fari ko kuma mai launi wani mabugar takardan.

kuma tana amfanine da gari wanda ake saka mata.

Sannan kuma wata tana iya buga takarda ta cire sannan kuma ta iya yin foto-kofi sannan kuma tana iya daukan hoto ko rubutaccen takarda don ta gyara

sannan ta sake cirewa.


Saidai kuma ita mabugar takardu ta kasu kashi biyu:-

Akwai mai baki-da-fari

Akwai mai launi.

Haka kuma suna da farshi daban-daban wanda ya danganci karfinsu da kyansu da kuma saurinda suke dashi da kuma ayyukanda suke yi da sauran bambance-bambancensu.

#Bintubetv #Duniyarcomputer #fasaharzamani

[Computer] Amfanin karan wasa, (pen/finger), modem, camera.
Duniyar computer (digital wold) part. 12

Amfanin karan wasa

Ita karan wasa ana amfani da itane a lokacinda mai amfani da Komfiuta yake so yayi was na shaya rai a cikin Komfiuta sai ya dauko wannan karan wasan ya saka sai yayi amfani dashi ta wajen yin wasa saboda ita Komfiuta tana da wasanni iri
daban-daban a cikinta wanda idan mai amfani da Komfiuta yaso yayi wasa sai ya budesu a cikin Komfiuta haka kuma mutum zai iya kara wasu wasannin daban

wadanda babu a cikin Komfiutarsa in yaga dama.


Amfanin web kemara

Ita kemaran web ana amfani da itane a yayinda mai amfani da Komfiuta yake so yayi hira da wani ta yanar gizo-gizo (internet) ko kuma yake so ya dauki hotonsa ya saka a cikin Komfiuta ko ya daura akan yanar gizo-gizo sai ya kawo kemaran web ya daura a kan Allon Komfiutarsa ko kuma ya ajiye a gefe sai yayi amfani da ita in kuma Komfiutar tafi da gidankane to yana da nasa kemaran a fuskar marfin Komfiutar sannan kuma ana iya makala mata wata daban a jikinta ko a gefe.

Amfranin makirufo

Shi kuma Makirufo ana amfani da shine a yayinda mai amfani da Komfiuta yake so ya dauki muryarsa ya sakata a cikin Komfiuta ko kuma yake so ya yi rekodin din wani abu da sauran abubuwanda ake so a shigar cikin Komfiuta indai

muryace to ana amfanida Makirufo don yinta.


Amfanin modem

Modem ana amfani da shine a yayinda ake so a hada Komfiuta da yanar gizo-gizo wato Internet don a samo bayanai ko kuma a aika bayanai zuwa kan Internet wanda inhar mai Komfiuta bashi da modem bazai iya shiga yanar gizo-gizoba saidai yayi amfanida wasu abubuwanda suke zama a maimakon modem.


Amfanin madaukin hoto

Shima madaukin hoto ana amfani dashine idan ana so a saka wani hoto ko zane ko bugeggen rubutu zuwa cikin Komfiuta saboda ita wannan na'urar tana daukan surar abu yadda take ta saka a cikin Komfiuta sannan kuma in anga dama sai asake gyarar wannan hoton ko rubutun ta yadda za'a canza masa tsari ko a sake cireta kamar yadda aka sakata ta hanyar mabugin takarda wato (Printer).

To wadannan sune na'urorin shigarwa da kuma amfninsu a jikin Komfiuta yanzu kuma sai mu wuce gaba muga bangare na biyu wato na'urorin fitarwa da kuma

yadda ake amfani dasu da kuma amfaninsu a jikin Komfiuta.


#Bintubetv #Duniyarcomputer #Fasaharzamani

[COMPUTER] AMFANIN DAN BERA (MOUSE).


Duniyar computer (digital wold) part. 11

AMFANIN DAN BERA

Shi kuma dan bera ana amfani da shine kamar yadda ake amfani da yatsa ma'ana shi kamar wata yatsace mai aiki da wutan lantarki da shine ake amfani wajen nuna abu acikin Komfiuta ko kuma jan abu ko kuma amincewa da wani abu ko ki a cikin Komfiuta.

Shi kuma dan bera yana da maballai guda biyu daya a hagu daya kuma a dama kuma a yawancin lokaci amfi yin amfani da maballin gefen hagu indai a babban Komfiutace amma indai a karamin Komfiutar tafi da gidan kane amfi yin amfani da maballi gefen dama saboda a Komfiutar tafi da gidanka ana amfani da tsakiyar Touch Pad wato waje mai tsantsinnan na kusada madannani domin ya yi maka aikinda maballin gefen hagu yakeyi amma a babban Komfiuta kuma babu wajen saidai ka dinga jan dan bera akan wani abu ko cinyarka.Don haka duk lokacinda akace ka dannan dan bera a babban Komfiuta to amfi danna na gefen hagu in kuma na gefen dama ake so ka danna sai ace maka ka danna na dama sabanin karamar Komfiuta.Kuma ana amfani da maballin gefen hagu don nuna abu a cikin Allon talbijin na Komfiuta saboda akwai wata kibiya wanda ake kira da suna Kuso (Cursor) wanda da ita ake nuna abu a jikin Allon talbijin din Komfiuta duk lokacinda ka taba dan bera itama zata dinga motsi don haka da ita ake nuna abu haka kuma ana amfanida maballin gefen hagu don jan wani abu kamar hoto ko rubutu sannan kuma da ita ake amfani wajen zaban abu da sauransu amma shi maballin gefen dama ana amfani da shine ta wajen neman karin bayani idan aka tsaya a gaban abinda ake so a nemi Karin bayani a game dashi aka danna ko kuma ana amfani dashine idan ana so a ofantar da wani abu ma'ana rashin amincewa ko yarda da wani abu.
#Bintubetv #fasaharzamani #Duniyarcomputer

[Computer] Amfani madannai (Keyboards).


Duniyarcomputer (digital world) part 10

Amfani madannai (Keyboard)

Madannai yanada amfani sosai a jikin Komfiuta saboda dashine mai amfani da Komfiuta zai shigar da bayanai cikin Komfiuta kamar rubutu saboda madannai yana daukeda haruffa daga A,B,C, har zuwa Z, wanda da sune mai amfani da Komfiuta zai shigar da dukkan abinda yake so ya rubuta a Komfiutarsa sannan kuma madannai yana daukeda lambobi daga 1, har zuwa 9, da 0 wadanda mai rubutu ko lissafi zai yi amfani dasu idan ya bukaci hakan hakannan kuma madannai yana da wasu alamomin tsara rubutu kamar alamar tambaya da alamar motsin-rai da karan dauri da karan-tsaye da aya da waqafi da alamar hadawa da rabawa da ragewa da bugawa da sauransu kamar yadda muke gani a jikin

kakuleto (Calculator).
Haka kuma madannai yana da wasu maballai wadanda ake amfani dasu ta wajen yin aiki na musamman kamar bawa Komfiuta umarni wadannan maballan kuma ana kiransu da suna (Function Keys) su kuma guda goma sha biyune suna farawa da F1-F12.Sannan kuma muna da wasu maballai a jikin madannai kamar maballin Ctrl da Alt da Delete da Back space da Shift da sauransu wanda zamuyi Maganaakansu in muga zo yin bayani akan amfanin madannai a manhajar rubutu wato Microsoft word in sha Allahu.

Wannan atakaice Kenan da yarda Allah zamu zo muko da cikekken bayanai gameda keyboards din nan.


#Bintubetv #Duniyarcomputer #fasaharzamani

Qwaqwalwar Computer. K. حيزكشًنا حدناعًنا جذحو. CPU


Duniyar computer (digital world) part 10

Sanin PC. Computer

Menene PC Computer (Na'ura mai kwakwalwa ta mutum daya)?

Na'ura mai kwakwalwa wato Komfiuta itace: wata na'ura da take amfani da wutan lantarki' wacce take karbar bayanan da aka shigar mata ta hanyar na'uran shigarwa ta ajiye, sannan kuma ta fitar da bayanan a duk lokacinda aka bukata ta hanyar sarrafawar mai amfani da ita da taimakon na'urar fitarwa.

Abinda ake nufi da na'urar shigarwa sune dukkan abubuwanda ake amfani dasu wajen shigar da bayanai cikin Komfiuta su kuma sun kasu kashi hudu kamar haka:-
Hausa
Larabci
Turanci

1- Na'urar shigarwa. لاخدلإا جزهخأ. Input devices.

2- Na'urar fitarwa. جاشخلإا جزهخأ. Output devices.

3- Na'urar ajiya. نيزختنا جزهخأ. Storage devices.

4- Kwakwalwa K. حيزكشًنا حدناعًنا جذحو. CPU.


Na farko na'urar shigarwa

To na'urar shigarwa kuma sune kamar haka:-


Cikin yaren, Hausa, Larabci, Turanci.

1. Madannai
حيتافًنا ححىن
Keyboard

2. Dan bera
جسأفنا
mouse

3. Karan wasa
ةعهنا اصع
Joy stick

4. Kemaran Web
ةيو جساىصّ   Web Cam.

5. Makirufo
خىصنا طللا
Microphone

6. Modem
فشاكنا/ ىيدىي
Modem

7. Madaukin hoto
يئىضنا حساًنا
Scanner
To a takaice wadannan su ake kira da suna na'urorin shigarwa wadanda ake amfani dasu domin shigarda bayanai cikin Komfiuta kamar yadda mai karatu ya kalli hotunansu a sama da kuma sunayensu a harcen Hausa da Larabci da kuma Turanci yanzu kuma sai mu dan yi bayanai akan kowanne daga cikinsu a takaice.

#Bintubetv #Fasaharzamani #Duniyarcomputer.
Hey, we've just launched a new custom color Blogger template. You'll like it - https://t.co/quGl87I2PZ
Join Our Newsletter